Covid-19: An shiga kullen Korona mai tsanani a Burtaniya

Firanministan Burtaniya Boris Johnson

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Firanministan Burtaniya Boris Johnson

Shirin sassaucin dokar kullen annobar Korona a lokacin bikin kirsimeti a Burtaniya ya gamu da cikas, bayan da hukumomi suka janye batun ɗaga ƙafa kwata-kwata.

Matakin wanda ya fara aiki daren Asabar ya biyo bayan gargadin da masana suka yi cewa yanzu haka nau'in annobar wanda yafi na baya haɗari na ci gaba da ɓarna musamman a London.

Baya ga London, sun ce za a dauki matakan kullen masu tsanani a yankunan Kent da Essex da Bedfordshire.

Akan haka ma Firanminista Boris Johnson ya sanar cewa yankunan da ke mataki na hudu na kullen kada su kuskura su yi cuɗanya da makwabtansu ko kuma duk wani da ba a zaune yake a cikin gidansu ba.

Ko a sauran yankunan da a baya aka aminta da ayi cuɗanya tsawon kwanaki biyar saboda bikin kirsimeti, a yanzu bikin ya takaita ga ranar kirsimetin kaɗai.

Bugu da ƙari dokar za ta shafi doka gundumomin London 32 da kuma ƙwaryar birnin, kuma za a hana zirga zirga daga wani yanki zuwa wani a duk fadin Burtaniya

A yankunan Scotland da Wales ma matakin iri daya ne, inda hukumomi suka sanar da cewa a ranar kirsimeti ne kawai za a sassauta dokar.

Za a hana zirga zirga daga wani yanki zuwa wani a duk fadin Burtaniya
Bayanan hoto, Za a hana zirga zirga daga wani yanki zuwa wani a duk fadin Burtaniya

A yanzu duk wata fita da ba ta zama ta dole ba an dakatar da ita daga nan zuwa mako biyu, lokacin da hukumomi za su sake nazarin kan sabbin matakai lura da yadda yanayin da ake ciki.

Firanminista Boris Johnson ya ce tuni an baiwa mutun 350,000 rigakafin annobar makonni biyu da fara shirin.

Ya kara da cewa dakunan shan magani za su ninka aikin da su ke yi na raba rigakafin don ganin an baiwa mutane da dama cikin ƙanƙanin lokaci.