Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran ƙasashen duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 2 ga watan Mayu, 2024.

Takaitacce

  • Zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa na ƙara bazuwa a Amurka
  • An kama jami'ar ƴansanda kan zargin safarar ƙananan yara a Sokoto
  • Dakarun Amurka na musamman sun fice daga Chadi
  • Ana ƙorafi kan yadda wayar Iphone ba ta tayar da masu ita daga barci
  • An kama masu zanga-zanga 17 a jami'ar Texas
  • Hukumar alhazai na taron masu ruwa da tsaki don inganta jigilar maniyyata
  • NLC ta bai wa gwamnati sabon wa'adi kan mafi ƙanƙantar albashi
  • Za a fara jigilar maniyyatan Najeriya daga ranar 15 ga watan Mayu – Nahcon

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba, Abdullahi Bello

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Yara takwas sun jikkata a harin da Rasha ta kai Ukraine

    Yara takwas ne suka jikkata sakamakon wani harin da Rasha ta kai a gabashin Ukraine.

    Yaran dai sun kasance a wata cibiyar wasanni ne a garin Derhachi a lokacin da rahotanni suka ce wani bam ya afka wa ginin.

    Wasu dai na zargin cewa hari ne na makami mai linzami.

    Derhachi na kusa da birnin Kharkiv, wanda aka zafafa kai wa hare-hare a cikin 'yan watannin nan.

  3. MDD ta ce ana buƙatar aƙalla dala biliyan 40 don sake gina Gaza

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana buƙatar aƙalla dala biliyan 40 wurin sake gina Gaza bayan yaƙin Isra’ila.

    Abdallah al-Dardari, wani mataimaki ga Sakatare Janar na MDD, ya shaida wa taron manema labarai cewa ɓarnar da aka yi yankin na da girma kuma ba a taɓa ganin irinsa ba.

    Ya ce, a matsayinmu na Majalisar Dinkin Duniya, abin da ya shafe a yanzu shi ne samar da muhallai, koda na wucin-gadi ne, ga dubban ɗaruruwan Falasɗinawa da kuma samar da muhimman abubuwan jin daɗin jama’a, kamar kiwon lafiya, da ilimi da ruwan sha da tsaftar muhalli da makamashin lantarki ga waɗannan mutane.

    Mista al-Dardari ya ce al'ummar duniya ba ta fuskanci irin wannan lamari ba tun bayan yaƙin duniya na biyu.

  4. 'Yan sandan Najeriya sun kama gomman masu aikata laifuka

    Makamai

    Asalin hoton, Nig Police

    Bayanan hoto, 'Yan sandan sun kuma ce sun gano bindigogi 16 da nau'ikan harsasai daban-daban

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'anta da ke aikin wanzar da tsaro a kan titin Abuja zuwa Kaduna sun samu nasarar kama gomman mutanen da take zargi da aikata miyagunj laifuka.

    Cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar mai ɗauke da sa hannun Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce jami'an rundunar da ke aiki a kan babban titin sun samu gagarumar nasara a aikin kakkaɓe ayyukan ɓata-gari a yankin.

    Sanarwar ta ce jami'an 'yan sandan sun kama mutum 81 da suke zargi da fashi da makami, da mutum 44 da suke zargi da yin garkuwa da mutane, sai mutum 73 da suke zargi da aikata laifin kisan kai, da mutum 36 da suke zargi da fyaɗe da mutum 22 da suke zargi da hannu a ayyukan da suka danganci tsafi ko asiri, da kuma wasu 28 da 'yan sandan suka zarga da aikata sauran laifuka.

    Harsasai

    Asalin hoton, Nig Police

    'Yan sandan sun kuma ce sun gano bindigogi 16 da nau'ikan harsasai daban-daban, da kuma wasu muggan makamai fiye da 200.

    Sanarwar 'yan sanda ta kuma ce jami'an sun gano ababen hawa 28 da ake zargin na sata ne, da buhunan takin zamani kimanin 600.

    Haka kuma 'yan sanda sun ce sun gano tsabar kuɗi naira miliyan 3,350,000 da suka yi zargin cewa an biya kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane.

    'Yan sandan sun kuma ce sun samu nasarar kuɓutar da mutum 158 da aka yi garkuwa da su, waɗanda tuni 'yan sanda suka ce an sada su da iyalansu.

  5. Ambaliya ruwa ta kashe mutum 24 a Brazil

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 24 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da ake ci gaba da neman wasu fiye da 20 a yankin kudancin Brazil, bayan mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliyar ruwa.

    Mutum 14,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon yanayin mai tsanani.

    Masana sun ce kashi daya bisa uku na matsakaicin ruwan sama na shekara guda ne ya sauka a jihar Rio Grande do Sul, tun ranar Asabar.

    Matsalar sauyin yanayi dai na addabar sassa daban daban na duniya musamman a shekarun baya-baya nan.

  6. Ƙungiyar MSF ta ce yaƙin Sudan na ƙara ta'azzara a yankin Darfur

    Ƙungiyar Likitoci ta 'Doctors Without Borders' ko 'MSF' ta ce mambobinta sun yi wa masu raunuka fiye da 100 magani, ciki har da ƙananan yara yayin da yaƙin da ake yi a yankin Darfur ke ci gaba da ta'azzara.

    Ƙasashen duniya na ta kiraye-kirayen tsagaita wuta, yayin da ake samun ƙaruwar fargabar mayaƙan RSF na shirya kai hari birnin Al-Fashir, mai ɗimbin fararen hula 'yan gudun hijira.

    Tuni dai ake ci gaba da yaƙi a kusa da Al-Fashir a yankin na Darfur, to sai dai ba cikakken yaƙin da ake fargabar ba ne.

    Ƙungiyar MSF ta ce dubban ƙananan yara da mata, da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam - da ke kudancin birnin - na fuskantar matsalar rashin abinci.

    MSF ta ce an shafe kusan shekara guda ba tare da kai abinci yankin a hukumance ba.

    Sojojin Ƙasar da dakarun RSF sun hana mafi yawan tallafin abinci zuwa yankin.

    A yayin da rayukan mutane da dama ke cikin hatsari, ƙungiyar likitocin ta ce abin da Majalisar Dinkin Duniya ke yi ba zai kare bala'in yunwa a yankin ba.

  7. Ba za mu ɗora wa gwamnatin da ta gabata alhakin gazawarmu ba - Shettima

    .

    Asalin hoton, x/Kashin Shettima

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatinsu ba za ta ɗora alhakin matsalolin - da riƙa fuskanta bayan karɓar mulki - kan tsohuwar gwamnatin da ta gababa ce su ba.

    Yayin da yake jawabi a wajen taron tattaunawa da jaridar '21st Century Chronicle' ta shirya, mataimakin shugaban ƙasar, ya ce wannan shi ne lokaci mafi wahala na riƙe muƙami a Najeriya, sakamakon matsalolin da ake fuskanta a ƙasar.

    Kashim Shettima ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu na ɗaukar matakai masu tsauri a ƙasar, don fitar da ita daga halin da take ciki.

    ''Shugaban ƙasa ya ɗauki matakan da za su kare rayukan mutane, a maimakon waɗanda za su ƙara jefa jama'a cikin wahala. Mu ba za mu ɗora alhakin wahalar da ake ciki kan gwamnatin da ta gabata ba, saboda shi shugabanci abu ne da ya jiɓanci ƙarfin gwiwa da ci gaba.''

    “Kafin mu karɓi mulki, babban abin da muka tarar shi ne batun cire tallafin man, abu ne da ya daɗe yana ci ya wa 'yan ƙasar tuwo ƙwarya na tsawon shekara 20 zuwa 30. Mun fahimci yadda gwamnatin da ta gabace mu ta yi yi tanadi cire tallafin, saboda ba ya cikin kasafin kuɗin shekarar''.

    “Shekara kafin mu karɓi mulki, bashin da ake bin NAjeriya ya ƙaru da kashi 111.18 cikin 100. Mataki ne da matsin tattalin arziki, abin da hakan ke nufin shi kamar a ce kana samun N100,000, to dole sai ka karɓo bashin ƙarin N11,800 don biyan wanda ke binka bashi. To ta yaya za mu rayu a wanna yanayi? Lamarin ya jima tun kan a fara sukar gwamnatinmu.''

    'Yan Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, lamarin da ya sa 'yan ƙasar da dama ke ɗora alhakin hakan kan tsare-tsare da manufofin gwamnatin ƙasar.

  8. Biden ya gabatar da jawabi kan zanga-zangar jami'o'in Amurka

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce dole ne a martaba 'yancin faɗar albarkacin baki da kuma dokar ƙasa.

    Yayin da yake jawabi kan zanga-zangar da ɗaliban jami'o'in Amurka ke gudanarwa kan yaƙin Gaza, shugaba Biden ya ce zanga-zangar lumana ba ta nufin barnatar da kadarori, da wuce gona da iri, da karya tagogi da rufe makarantu tare da tilasta soke ɗaukar darusa.

    “Haƙiƙa akwai 'yancin gudanar da zanga-zanga , amma babu 'yancin kawo ruɗani'', in ji Biden.

    Rashin dakatar da yaƙin Gaza ne ya sa ɗalibai a faɗin jami'o'in Amurka suka riƙa kafa tantuna tare da bazama kan wasu titunan ƙasar don gudanar da zanga-zangar.

    Sai dai a jawabin nasa, shugaba Biden bai yi ƙoƙarin yin bayani ko kare manufar gwamnatinsa kan yaƙin Isra'ila da Gaza ba.

    Shugaban na Amurka bai kuma bayyana wani dalilin da zai sa ɗaliban su janye daga zanga-zangar ba. Amma ya ce idan suka ƙetare iyaka a zanga-zangar tasu, to za a ɗauki mataki a kansu.

  9. Kotu ta ɗage shari'ar ma'aikatan Binance a Najeriya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata babbar kotu a Abuja, babban birnin Najeriya ta ɗage sauraron ƙarar halasta kuɗin haram da aka shigar kan ma'aikatan kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto - Binance zuwa ranar 17 ga watan Mayu.

    An tsara ci gaba da zaman shari'ar yau Alhamis sai dai a yanzu, an jinkirta.

    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati na zargin kamfanin na Binance da ma'aikatansa biyu, Tigran Gambarayan da Nadeem Anjarwalla da laifin halasta kuɗin haram da ya kai dala miliyan 35.4.

    Lauyan Gambarayan ya shaida wa kotu cewa ba a bai wa wanda yake karewa takardun kotu ba, don haka ya roƙi kotu ta jinkirta ƙarar.

    Ita ma hukumar tattara haraji ta Najeriya tana tuhumar Binance da ma'aikatan nasa da laifuka biyar da suka shafi kauce wa biyan haraji.

    Tigran Gambarayan, wanda ɗan Amurka ne, ya musanta zargin tuhume-tuhumen da ake yi masa yayin da har yanzu ake neman abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla ruwa a jallo bayan ya tsere daga gidan gyaran hali a watan Maris.

    Gambarayan, mai shekara 39 zai ci gaba da zama a tsare har sai ranar 17 ga watan Mayu da za a ci gaba da zaman shari'ar.

  10. Yadda ƴan sanda suka kama masu zanga zanga a jami'ar California

    Kamar yadda muka ba da rahoto a ɗazu, ƴansanda sun fara tsare mutane tare da cire abubuwan da masu zanga-zanga suka datse hanya a jami'ar California Los Angeles.

    Ƴansanda sun yi arangama da mazu zanga-zangar.

    Ga wasu ƙarin hotuna daga wurin zanga-zangar.

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Malaman jami'ar Abuja sun tsunduma yajin aiki

    ..

    Asalin hoton, UNIABUJA

    Mambobin ƙungiyar malaman jami'a ASUU, reshen jami'ar Abuja sun tafi yajin aikin sai baba ta gani saboda wasu matsaloli da ke daƙile ci gaban ƙungiyar.

    Ƙungiyar malaman ta sanar da hukuncin fara yajin aikin ne a ranar Alhamis bayan kammala taron da ta yi a harabar jami'ar.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa mambobin ƙungiyar ASUU reshen jami'ar ta Abuja ba sa ga maciji da shugaban jami'ar mai bari gado Farfesa Abdulrasheed Na’allah da kuma ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman kan zaɓen sabon shugaba da zai ja ragamar jami'ar.

    Wata sanarwa da aka buga a ɗaya daga cikin jaridun ƙasar a ranar 15 ga watan Maris ta buƙaci a sauya Na'Allah.

  12. An kammala bincike kan kisan da aka yi wa masu maulidi a Tudun Biri

    ..

    Asalin hoton, X/DEFENCE HQ

    Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ta kammala binciken da aka daɗe ana dako kan bam ɗin da aka jefa kan mutane a ƙauyen Tudun Biri a ƙaramar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

    Ta kuma ce sojojin da aka samu da laifi a kai harin za su gurfana a gaban kotun soji domin fuskantar hukunci.

    Daraktan yaɗa labarai na hedikwatar tsaron, Edward Buba ne ya bayyana haka a taron yaɗa labaran da aka gudanar a Abuja.

    A Disambar bara ne wani jirgin sojoji ya jefa bam kan mutanen da ke bikin maulidi lamarin da ya janyo asarar rayuka da jikkatar wasu da dama.

    Rundunar sojin Najeriya ta ɗauki alhakin kai harin inda ta ce lamarin ya faru bisa kuskure.

  13. An kama fiye da mutum 50 kan zargin tayar da zaune-tsaye a Legas

    ..

    Asalin hoton, @BenHundeyin/X

    Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Legas ta cafke mutum sama da 50 bayan hargitsin da ya kaure tsakanin wasu matasa da ɓatagari a yankin Ile-Epo da ke jihar Legas.

    A sanarwar da kakaknin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ya fitar ranar Alhamis, babban jami'in ɗansanda yankin ya tura jami'ansa zuwa wajen inda kuma tuni aka maido da zaman lafiya.

    Sanarwar ta ce an lalata rumfunan da suke zaune.

    Kwamihsinan ƴansanda CP Adegoke Fayoade ya bayar da umarnin a gurfanar da mutanen da aka kama inda kuma ya yi gargaɗi cewa rundunar za ta ɗauki mataki kan duk wanda aka samu da ta da zaune tsaye.

  14. Za a fara jigilar maniyyatan Najeriya daga ranar 15 ga watan Mayu – Nahcon

    ..

    Asalin hoton, Nahcon/Facebook

    Hukumar alhazai ta Najeriya Nahcon ta ce a ranar 15 ga watan Mayu ne za a fara jigilar maniyyatan bana zuwa Saudiyya domin sauke farali.

    Shugaban hukumar Malam Jalal Ahmad Arabi ne ya bayyana haka a jawabin buɗe taron masu ruwa da tsaki na farko da hukumar ta shirya a Abuja.

    Arabi ya ce kimanin maniyyata 51,000 ne za su gudanar da aikin hajjin bana inda ya ce jiragen da suka samu sahhalewa ne za su yi jigilarsu zuwa ƙasa mai tsarki.

    Shugaban hukumar ta Nahcon ya ce hukumar ta yanke cewa a bana, duka maniyyatan Najeriya za su yi aƙalla kwana huɗu a Madina kafin soma aikin hajji.

    Ya ce an shirya taron ne domin inganta ayyukan hukumar na gudanar da aikin hajji.

  15. NLC ta bai wa gwamnati sabon wa'adi kan mafi ƙanƙantar albashi

    ..

    Asalin hoton, JOE AJAERO/FACEBOOK

    Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta bai wa gwamnatin ƙasar nan da 31 ga watan Mayu don ƙara fito da sabon albashi mafi ƙaranci ga ma'aikatan ƙasar.

    Ƙungiyar ta sanar da haka ne yayin bikin murnar ranar ma'aikata ta ƙasa a filin taron Eagle Square da ke Abuja a ranar Laraba.

    Shugaban ƙungiyar NLC Joe Ajaero tare da takwaransa na ƙungiyar TUC Festus Osifo sun haɗu kan cewa mafi ƙaranci albashi na naira 30,000 ya yi wa ma'aikatan Najeriya kaɗan duba da yanayin matsi da kuma tsadar rayuwa da ya haɗa da tashin farashin abinci da kuɗin wuta da na sufuri da kuma sauransu.

    Sun dage kan naira 615,000 a matsayin albashi mafi ƙaranci da suke so gwamnatin shugaba Bola Tinubu t saka hannu kafin ƙarshen watan Mayu.

    Ajaero ya ce, "ƙungiyar NLC da ta TUC na jaddada cewa matsawar za a ci gaba da tattaunawa kan batun mafi ƙarancin albashi ba tare da mafita ba har zuwa ƙarshen Mayu ba za mu iya ci gaba da ba da haɗin kai ba a ƙasar nan".

    A ɓangaren Osifo kuma ya nemi hukumar kula da wutar lantarki tare da kamfanonin da suke rarraba wutar kan su janye ƙarin kuɗin da su ka yi wa mutane da ke rukunin A waɗanda suka fi samun wuta.

    Ƴan Najeriya sun tsinci kansu cikin raɗaɗin tsadar rayuwa da layi mara iyaka a gidajen mai bayan tashin farashi da rashin man fetur a fadin ƙasar.

    Duk da tabbacin da kamfanin mai na ƙasa ya bayar kan shawo kan matsalar, an ci gaba da samun layuka a gidajen siyar da mai fiye da tsawon sati ɗaya.

  16. Hukumar alhazai na taron masu ruwa da tsaki don inganta jigilar maniyyata

    ..

    Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta soma gudanar da taron masu ruwa da tsaki na ƙasa na farko kan aikin hajjin wannan shekara ta 2024 ga duka jami'an aikin Hajji da kuma masu kamfanonin sufurin jiragen sama.

    A taron za a mayar da hankali a kan sabbin tsare-tsaren da aka fito da su domin inganta aikin Hajjin bana.

    Daga cikin waɗanda suka halarci taron har da mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III, da mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shattima wanda ya samu wakilcin tsohon ministan birnin tarayya Abuja Aliyu Modibbo da kuma jakadan Saudiyya a Najeriya Faisal Ibrahim Al - Ghamidy da sauran manyan baƙi.

    Kimanin maniyyata 51,000 ake sa ran za su gudanar da aikin Hajjin wannan shekarar 2024 daga Najeriya.

    ..
    ..
  17. An kama masu zanga-zanga 17 a jami'ar Texas

    ..

    Asalin hoton, EPA

    An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon aka yi kamen a jami'ar Texas da ke Dallas.

    Wata sanarwa daga jami'ar ta ce ƴan sandan sun je makarantar bayan da masu zanga-zangar suka fara kafa sansani a babbar hanyar shiga makarantar.

    An ba su gargaɗi a rubuce kan cewa su bar wajen kafin ƴan sanda su kutsa kai tare da tarwatsa wajen.

    Ya zuwa ƙarfe 5:00 agogon ƙasar (22:00 GMT) na ranar Laraba ƴan sanda sun ce sun kama mutum 17 kan laifin ƙetare iyaka.

    Daga bisani kuma kafar yaɗa labarai ta CBS ta yi rahoton cewa mutum 21 aka kama inda ta ruwaito lauyoyin waɗanda aka tsare.

  18. Ana ƙorafi kan yadda wayar Iphone ba ta tayar da masu ita daga barci

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin Apple ya ce yana ƙoƙarin ganin ya shawo kan matsalar da ke hana wasu daga cikin wayoyinsa buga ƙararrawawar ta da masu amfani da wayar daga barci.

    Babu tabbacin mutane nawa lamarin ya shafa, wanda ke haifar da dogon barci ga masu amfani da wayoyin.

    Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun yi ta ƙorafi a shafukan sada zumunta.

    Apple ya tabbatar cewa ya san da matsalar amma bai kai ga gano abin da yake janyo haka ba ko kuma abin da masu amfani da wayoyin za su yi domin farkawa a makare.

    Akwai abin da mutum zai iya yi kafin a magance matsalar a hukumance.

    Na ɗaya shi ne a kaucewa yin kuskure ta hanyar tabbatar da cewa an seta ƙararrawar yadda ya kamata da kuma ƙara sautinsa.

    Apple ya ce yana fatan zai magance matsalar.

  19. Dakarun Amurka na musamman sun fice daga Chadi

    Amurka ta janye gaba ɗaya dakarunta 75 da aka kirge a sansanin sojojin sama na Adji Kossei da ke N'Djamena, babban birnin Chadi, kamar yadda jaridar Le Pays Tchad ta ruwaito.

    Ministan kula da dakarun ƙasar, Dago Yacouba ya ce hakan ba yana nufin ƙarshen ƙawancen sojoji da Amurka.

    "Babu wanda ya nemi Amurka ta fice daga Chadi. Ficewar ta ɗan lokaci ne kuma ta shafi sojojin da ke sansanin Adji Kossei," in ji shi.

    A ranar 19 ga watan Afrilu ne, Chadi ta umarci a dakatar da ayyukan sojojin Amurka a sansanin na Adji Kossei bayan da nemi dalilin kasancewar sojojin.

    Kwana biyu bayan nan, Amurka ta musanta cewa Chadi ta nemi wasu buƙatu game da janye sojojin, inda ya ce sun tattauna kan makomar alaƙarsu ta tsaro.

    Har yanzu Chadi ce ƙawa ta ƙarshe ga ƙasashen yamma a yankin Sahel inda ta karɓi baƙuncin Amurka da Faransa.

    Sojojin da ke mulki a Mali da Nijar da Burkina Faso sun kori dakarun Faransa daga ƙasashensu, abin da ya ƙara ƙarfafa alaƙarsu da Rasha.

  20. Hotunan masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a jami'ar California

    Waɗannan sabbin hotunan wurin da masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa suka yi sansani a kusa da ɗakin taron Royce na Jami'ar California Los Angeles.

    Masu zanga-zangar sun toshe hanyoyin zuwa wajen.

    An ga mambobin tsangayar UCLA tsaye a gaban dandazon jama'ar bayan ƴan sandan jami'ar sun nemi masu zanga-zangar da su watse.

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    ..

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    ..

    Asalin hoton, Reuters