Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, A'isha Babangida da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Sai da safe

    Mun kawo ƙarshen rahotonni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Gwamnoni ba su adawa da sabon mafi ƙarancin albashi - Abdullahi Sule

    Abdullahi Sule

    Gwamnan jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya ya ce shi da takwarorinsa ba su ƙyashin biyan ma'aikata mafi ƙarancin albashi da ake sa ran ƙarawa nan gaba kaɗan.

    Da yake yi wa manema labarai jawabi a fadar shugaban ƙasa, Abdullahi Sule ya ce jiharsa na biyan ma'aikata N30,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi tun daga 2019 "har ma da wasu alawus".

    "Mun damu da walwalar ma'aikata. Hasali ma, muna biyan wasu alawus-alawus da muke biyan ma'aikatan lafiya," in ji shi. Sai dai BBC ba ta tabbatar da iƙirarin nasa ba.

    "Saboda haka ba na jin gwamnoni na da wata matsala da biyan mafi ƙarancin albashi."

    Har yanzu gwamnatin tarayya na tattaunawa da gamayyar ƙungiyar ƙwadago don cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashin.Ƙungiyar NLC na neman sama da N600,000.

  3. Majalisar Najeriya za ta yi dokar kare haƙƙin 'yan aikin-gida

    Godswill Akpabio

    Majalisar dattijai a Najeriya na shirin samar da dokar da za ta kafa hukumar tattara bayanai na ‘yan aikin-gida da kuma iyayen gidansu.

    Majalsar ta ce za a samar da hukumar ne domin tabbatar da kare haƙƙin ‘yan aiki, waɗanda ke yawan fuskantar cinzarafi daga iyayen gidansu.

    Kazalika, ƙudirin dokar ya tsallake karatu na biyu ya nemi a kare iyayen gdan, waɗanda a wasu lokutan ke fuskantar hadari daga masu yi musu aikin.

    "Idan ƙudirin nan ya zama doka to wajibi ne a bai wa 'yan-aiki wurin kwana mai kyau kamar yadda mutum zai bai wa iyalinsa, ba za a ci mutuncinsu ba. Talauci ba zai zama hujjar da mutum zai mutuncin wani mutum ba," in ji Sanata Babangida Hussaini.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Buhari Muhammad Fagge:

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Buhari Muhammad Fagge:
  4. Wutar Olympic ta ƙarasa Faransa

    Wutar Olympic

    Wutar gasar Olympic ta ƙarasa birnin Marseille na Faransa cikin "tsattsauran tsaro" kwana 79 kafin bikin buɗe gasar a birnin Paris.

    Wani jirgin ruwa ne ya kai wutar birnin da ke gaɓar ruwan Baharrum daga birnin Olympia na Girka.

    Za a ƙarasa da wutar kan dandariyar ƙasa yayin wani fareti da za a yi da jiragen ruwa sama da 1,000 a gaban Shugaban Ƙasa Emmanuel Macron, inda ake sa ran 'yan kallo 150,000 za su halarta.

    Hukumomi sun ce an jibge jami'an tsaro 6,000, waɗanda suka haɗa da 'yansanda na musamman, da masu harbi daga nesa.

  5. Za mu ɗauki mataki kan Binance saboda zargin cinhanci - Majalisar Wakilan Najeriya

    Tajuddeen Abbas

    Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za ta ɗauki matakin da ya dace a kan kamfanin kuɗin intanet na Binance saboda zargin cinhanci da ya yi wa hukumomin ƙasar.

    Shugaban kamfanin na cryptocurrency, Richard Teng, ya yi zargi ranar Talata cewa kwamatin majalisar kan harkokin kuɗi ƙarƙashin jagorancin Ginger Onwusibe ya nemi cinhanci daga wajen wakilansa yayin wata ganawa a harabar majalisar a watan Janairu.

    "Daidai lokacin da ma'aikatanmu ke shirin barin wurin, sai wasu mutane da ba su san su ba suka matsa kusa da su kuma suka nuna musu cewa za su iya biyan kuɗin don sasanta zarge-zargen," a cewar Mista Teng.

    Sai dai kuma yayin zamanta na yau Laraba, ɗan majalisa Kama NkemKanma ya tayar da batun, yana mai cewa Teng ya yi kalaman ne don ɓata sunan majalisar.

  6. Gwamnatin Kano ta ɗauki nauyin yaran da ake zargi abokin mahaifinsu ya yi lalata da su

    Aisha Saji

    Kwamishinar Mata da Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Aisha Saji, ta shiga tsakani kan lamarin wasu yara maza biyu ‘yan kasa da shekara 10 da ake zargi abokin mahaifinsu ya yi lalata da su don tabbatar da adalci ga yaran.

    Cikin wata sanarwa, daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar Aishatu Haruna ta ce kwamashinar ta dauki nauyin lamarin ne bayan ɓullar labarin a wani shirin gidan rediyon ‘Yanchi da Rayuwa’.

    "Nan take kwamishinar ta umarci daraktoci biyu da wani ƙwararen ma’aikaci a ma’aikatar da su tuntuɓi waɗanda abin ya shafa tare da ba ta rahoto kan lamarin," in ji sanarwar.

    "Bisa la'akari da halin da mutanen da lamarin ya shafa suka shiga, kwamishinar ta yi alƙawarin bin diddigin lamarin har zuwa karshe, sannan kuma ta yi kokarin ganin an samar da wata kafa ta gwamnati da za ta samu nasara a shari'a."

    Haka nan, ta biya basukan da aka tara na tsawon watanni ana jinyar yaran biyu, waɗanda har yanzu ba su samu cikakkiyar lafiya daga raunukan da suka samu a duburarsu ba.

  7. Falasɗinawa kusan 200 ne ke barin Rafah duk awa ɗaya - UNRWA

    Rafah

    Mutum kusan 200 ne ke barin yankin Rafah duk awa ɗaya - a lisaffi na tsakatsaki - bayan Isra'ila ta umarce su da yin hakan, a cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira Falasɗinawa (UNRWA).

    "Ana ci gaba da raba mutane da muhallansu kuma mutane na tafiya zuwa Khan Younis da kuma tsakiyar Gaza," a cewar shugabar sashen yaɗa labarai ta UNRWA Juliette Touma.

    "Ba zai yiwu a faɗi adadin mutanen da aka raba da muhallansu ba a yanzu, ganin yadda yanayin yake a yanzu."

    Dubban mutane ne suka bar yankin tun daga ranar Litinin saboda fargabar hare-haren Isra'ila da ta fara kaiwa ta ƙasa.

    Rafah
  8. Kotu ta ɗaure masu damfara ta Intanet 41 a jihar Anambra

    ...

    Wata babbar kotun tarayya da ke zama a garin Onitsha a jihar Anambra, karkashin jagorancin mai shari’a S. M Shuaibu da Hauwa Inuwa ta yankewa wasu ƴan damfara ta intanet 41 hukuncin ɗaurin shekara daya a gidan yari.

    Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin sada zumunta na X na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC.

    An ɗaure waɗanda aka yanke wa hukuncin ne bayan sun amsa laifukansu da suka haɗa da samu ta hanyar karya da mallakar takardun damfara, da kuma taimakawa wajen aikata wani laifi bayan da hukumar ta EFCC ta gurfanar da su a kotu

    Dukkan wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu ne a lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhume daban-daban, kuma bisa la’akari da rokon da suka yi, lauyan Hukumar EFCC, Michael Ikechukwu Ani, ya roki kotu da ta yanke musu hukunci tare da yanke musu hukuncin da ya dace.

    Sai dai lauyoyin wadanda ake tuhuma sun roki kotun da ta yi musu sassauci da kuma tausaya musu wajen yanke musu hukunci, inda suka kara da cewa sun nuna nadamar abin da suka aikata.

    Alkalan sun kuma bayar da umarnin a rika shigar da wadanda aka yankewa hukuncin hidimtawa al'umma daurin bisa ga sashe na 462 na dokar shari’a tare da bayar da umarnin a yi gwanjon kayayyakin da aka kwato daga hannunsu da suka hada da wayoyin hannu da kwamfutaci ta hannun tare da tura kuɗaɗen a Asusun bai ɗaya.

    View more on twitter
  9. Masu safarar mutane sun bar ɗimbin ‘yan ƙasar Habasha a dazukan Kenya

    'Yan sanda a Kenya na tsare da 'yan kasar Habasha 24 da aka bari a wasu dazuka da ke lardin Isiolo a arewa maso gabashin kasar, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

    An ce sun nemi agaji ne a wani ofishin ‘yan sanda da ke yankin Merti bayan waɗada ake zarginsu da safarar su sun gudu sun bar su ranar Lahadi.

    An bayar da rahoton cewa, masu safarar mutane da ba a san ko su waye ba sun gudu ne da niyyar kaucewa shingen bincike a kan babbar hanyar Isiolo zuwa Nairobi.

    Bakin hauren sun shaida wa 'yan sanda cewa suna kan hanyar zuwa Afirka ta Kudu bayan sun tsallaka kan iyakar Kenya da Habasha.

    Ƴan Habashan dai na hannun ‘yan sanda suna jiran a gurfanar da su a gaban kuliya saboda kasancewarsu a kasar ba bisa ka’ida ba.

    ‘Yan sanda sun ce za su ci gaba da neman masu safarar mutanen.

    Kenya dai hanya ce ta gama-gari ga bakin hauren Habasha da ke yunkurin shiga Afirka ta Kudu.

  10. Za mu yi gagarumar zanga-zanga idan ba a soke harajin tsaron intanet ba - TUC

    ..

    Ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Najeriya ta yi barazanar gudanar da gagarumar zanga-zanga tare da dakatar da al'umura a faɗin ƙasar matuƙar gwamnatin tarayya ba ta soke sabon harajin tsaron intanet da Babban bankin ƙasar ya ɓullo da shi ba.

    Ƙungiyar ta yi barazanar ce a wata sanarwa da ta fitar yau Laraba, wadda ta samu sa hannun shugaban ƙungiyar, Festus Osifo.

    Hakan na zuwa ne bayan ita ma ƙungiyar ƙwadago ta TUC ta soki lamirin sabon harajin, wanda ta bayyana a matsayin wani gagarumin nauyi da gwamnati ke ɗora wa talaka.

    A ranar Talata ne Babban Bankin Najeriya ya fitar da wata sanarwa wadda ke neman a cire harajin kashi 0.5 cikin ɗari kan duk wata hada-hadar tura kuɗi da mutanen ƙasar suka yi ta intanet.

    Sanarwar TUC ta ci gaba da cewa "babu dabara wajen fito da irin wannan haraji daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa sanadiyyar faɗuwar darajar naira da ƙarin farashin man fetur da na lantarki.

  11. Ecowas za ta kafa dakarun ko-ta-kwana don yaƙi da ta'addanci a yammacin Afirka

    ..

    Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka Ecowas ta ce za ta kafa dakarun ko-ta-kwana domin tunkarar matsalar 'yan ta'adda masu iƙirarin jihadi da ke tayar da zaune tsaye a ƙasashe daban-daban, kamar yadda shafin intanet na The Nation mai zaman kansa a Najeriya ya rawaito.

    Kwamishinan Ecowas Abdel-Fatau Musah ya fadi hakan ne jiya a Abuja cewa ƙungiyar na bukatar tara dala biliyan 2.4 ga dakarun, inda ƙasashe mambobin kungiyar suka bayar da rabin adadin.

    "A yau, Burkina Faso ta zarce Afganistan a matsayin kasa mafi fama da ta'addanci a duniya kuma Afirka ta zama gida ga kungiyoyin ta'addanci," in ji Musah.

    Shugabannin sojojin Mali da Burkina Faso da Nijar dai sun janye daga kungiyar ta Ecowas a farkon wannan shekarar, bayan da suka zarge ta da rashin tallafa musu wajen tunkarar tashe-tashen hankula daga kungiyoyin al-Qaeda da IS a tsawon shekaru.

  12. Amurka ta dakatar da tura wa Isra'ila makamai

    ..

    Amurka a makon da ya gabata ta dakatar da aika wa Isra'ila bama-bamai kan fargabar kai munanen hare-hare a birnin Rafah da ke kudancin Gaza...a cewar wani babban jami'in gwamnatin Amurka.

    Jami'in ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS cewa kayan sun haɗa da bam mai nauyin tan 1,800 2,000lb da 1,700 500lb.

    Ya ƙara da cewa Isra'ila ba ta saurari koken Amurka kan buƙatun kayan agajin da suka kamata a kai wa mutanen Rafah ba.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ta IDF Daniel Hagari ya shaida wa manema labarai cewa Amurka ta riƙa bayar da taimakon tsaro tun farkon yaƙin, inda ya ƙara da cewa an yi wata tattaunawar sirri tsakanin ƙasashen biyu.

    Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare a tsakiyar dare a zirin Gaza sa'o'i bayan sojojin Isra'ila cikin motocin yaƙi sun ƙwace mashigar Rafah da ke ɓangaren Falasɗinawa a kan iyakar Masar.

    Yanzu haka dai Isra'ila ta tsananta kai hare-hare a kewayen Rafah. Wasu kafofin sun ce mutum bakwai aka kashe ƴan gida ɗaya a wani hari da aka kai.

    Rafah ta kasance muhimmiyar hanya ta shigar da kayan agaji kuma hanya ɗaya da mutane ke iya fita daga garin tun farkon fara yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas a Oktoban shekarar da ta gabata.

    An rufe mashigar tun safiyar ranar Laraba amma rundunar sojin ta ce za ta ƙara buɗe mashigar Kerem Shalom da ke kusa da wadda aka rufe tsawon kwanaki huɗu.

  13. Isra'ila ta kori ƴan malawi da suka bar gonakin da aka ɗauke su aiki

    ....

    Gwamnatin Malawi ta ce Isra'ila ta kori ma'aikata 12 'yan Malawi da suka bar gonakin da aka dauke su aiki.

    A wata sanarwa da ministan yaɗa labaran ƙasar Moses Kunkuyu ya fitar, ya ce ma'aikatan na da takardar biza mai inganci na yin aiki a wasu gonaki na musamman amma sun "keta kwantiraginsu" ta hanyar zuwa aiki a gidan burodi.

    'Yan Malawi 12 na daga cikin ma'aikatan kasashen waje sama da 40 da aka kama yayin da suke aiki a gidan burodi a Tel Aviv a makon jiya.

    Mista Kunkuyu ya ce laifi ne da saɓa doka a dokokin Isra'ila idan ma'aikacin waje ya canza aiki ba tare da bin hanyoyin da suka dace ba.

    Ya gargadi dukkan ma'aikatan bakin haure 'yan kasar Malawi a Isra'ila da su guji irin wannan hali da ke jefa kasar cikin rashin mutunci.

    "Irin wannan hali na iya rage aikin yi na mutanen da abin ya shafa," in ji shi.

    Daruruwan 'yan Malawi ne suka je Isra'ila a bara domin cike giɓin ma'aikata a gonakin Isra'ila, yayin da dubban ma'aikata suka fice bayan fara yaki da Hamas a watan Oktoba.

    Hakan ya zo ne a wani bangare na yarjejeniyar fitar da ma’aikata tsakanin ƙasashen biyu a shekarar 2022.

    A makon da ya gabata, wasu 'yan kasar Malawi sun shaida wa BBC cewa karancin albashi ne ya sa wasu daga cikinsu suka bar aikinsu a gonakin neman wani aiki a kasar.

  14. Najeriya ta musanta zargin neman cin hanci daga kamfanin Binance

    Bola Tinubu

    Gwamnatin Najeriya ta musanta iƙirarin da kamfanin hada-hadar kuɗi ta intanet, Binance ya yi kan cewa wani jami'in gwamnatin ƙasar ya nemi cin hanci daga jami'in kamfanin na kuɗin kirifto dala miliyan 150.

    A ranar Talata ne shugaban kamfanin na Binance, Richard Teng ya yi zargin, wanda aka wallafa a jaridar New York Times ta Amurka da ma wasu jaridun duniya a ci gaba da taƙaddamar da ake yi tsakanin kamfanin na kuɗin kirifto da Najeriya.

    Sai dai a wata takardar sanarwa da ta samu sa hannun Rabi'u Ibrahim, mai magana da yawun ministan yaɗa labari na Najeriya, ƙasar ta ce zargin na kamfanin Binance wani yunƙuri ne na "ɓata wa Najeriya suna domin ɓoye ayyukan da yake yi na saɓa ƙa'ida".

    Sanarwar ta ce "babu ko ƙwayar zarra ta gaskiya a zargin da kamfanin na Binance ya yi."

    Sanarwar ta ci gaba da cewa gaskiyar lamarin shi ne ana ci gaba da tuhumar Binance a Najeriya saboda barin da ya yi aka yi amfani da shafinsa wajen "halasta kuɗaɗen haram da taimaka wa ayyukan ta'addanci da kuma ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen ƙetare ba bisa ƙa'ida ba".

  15. Binance na zargin jami'an Najeriya da neman cin hancin dala miliyan 150

    ..

    Kamfanin Binance ya zargi wasu manyan jami'an gwamnatin Najeriya da neman cin hancin dala miliyan 150 a kuɗin kirifto domin a kawo ƙarshen tuhumar da ake masa.

    Shugaban kamfanin, Richard Teng ne ya bayyana haka a wani shafin intanet, kamar yadda jaridar New York Times ta wallafa.

    A cewar rahoton na jaridar ta New York Times, Tigran Gambaryan, jami'i a a kamfanin, ya yi iƙirarin cewa ya samu wani saƙo mai ɗaga hankali a wata tafiya da ya yi zuwa Najeriya a watan Janairu.

    Rahoton ya ce "a wata ziyara zuwa Najeriya a watan Janairu, Tigran Gambaryan, jami'i a kamfanin Binance mai hada-hadar kirifto, ya samu wani saƙo mai tayar da hankali. An bai wa kamfanin kwana huɗu su biya dala miliyan 150 a kuɗin kirifto,"

    Gambaryan, wanda tsohon jami'in tsaro ne a Amurka, ya fahimci saƙon a matsayin neman na goro daga wani a gwamnatin Najeriya, a cewar wasu mutum biyar da suka san da batun da kuma nazarin saƙon da jaridar New York Times ta yi.

    Shi da abokan aikinsa na Binance sun gana da ƴan majalisar dokokin Najeriya da suka zargi kamfanin da kauce wa biyan haraji da kuma barazanar kama ma'aikatan kamfanin."

    Bayanai sun nuna cewa lamarin ya faru ne kafin a kama Gambaryan da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla bisa umarnin mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro, Nuhu Ribadu.

    Daga bisani kuma Anjarwalla ya tsere inda aka gano shi a Kenya.

    A martaninsa, kakakin ofishin Ribadu, Zakari Mijinyawa ya bai wa gwamnati tabbacin bin ƙa'ida.

    Mijinyawa a cewar wani saƙo da aka aike wa jaridar New York Times, gwamnati za ta bayyana hujjojinta, bisa tsarin doka.

  16. Mutum 44 sun kamu da kwalara sakamakon ambaliya a Kenya

    ..

    An samu rahoton mutum 44 sun kamu da cutar kwalara a lardin Tana River da ke Kenya yayin da ambaliyar ruwa ke ƙara buɗe ƙofar yaɗuwar cututtukan da ake iya ɗauka ta ruwa.

    Sanarwa da Hukumar lafiya ta duniya ta fitar wadda ta bayyana adadin, inda ta ce hukumomi a Kenya tare da goyon bayan WHO da kuma sauran hukumomi na sa ido a kan cutar da matakan da za a ɗauka a faɗin ƙasar yayin da ake fama da ambaliyar.

    Ambaliyar ta shafi kashi ɗaya cikin huɗu na mutane miliyan ɗaya tare da samun rahoton mutuwar mutum 238 a faɗin ƙasar. Tana River na ɗaya daga cikin lardunan da ambaliyar ta fi shafa a Kenya.

    A ranar Talata ne babbar sakatariyar lafiya ta Kenya Mary Muthoni ta ce akwai babbar barazana na yiwuwar cututtukan da ke yaɗuwa ta ruwa su zama annoba idan ba a ɗauki mataki da wuri ba.

    Ms Muthoni ta yi magana ne yayin da ita da sauran jami'an lafiya suke raba kayayyakin tsabtace ruwa a babban birnin Nairobi.

    Ta kuma yi magana a kan haɗarin cututtukan da ake samu a lalataccen abinci da abincin da aka samu daga hanyoyi marasa nagarta da ambaliyar ta janyo ƙaruwarsu.

    WHO ta ce za ta ci gaba da ba da goyon baya ga matakan gaggawa na gwamnati kuma za ta "ci gaba da sa ido kan ɓarkewar cututtuka da ka iya saurin yaɗuwa idan ba a yi saurin magance su ba".

    Ta kuma ce, "WHO ta kuma samar da kayayyakin magance cutar ta kwalara da ake rarrabawa a muhimman larduna wanda za su iya warkar da mutum 10,000".

  17. Jami'ar jihar Ekiti ta kori ɗalibai biyu kan bidiyon cin zali

    ..

    Hukumar gudanarwar jami'ar jihar Ekiti, Bouesti ta kori ɗalibai biyu bayan ɓullar wani bidiyo da ya nuna yadda suke cin zalin wata abokiyar karatunsu.

    Bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta ya nuna wata ɗaliba Opemiposi Precious Bolaji, ƴar shekara 18 da take aji ɗaya a sashen koyon aikin jarida tana dukan abokiyar karatunta mai suna Gloria Ajayi a gidan kwanansu da ke wajen harabar jami'ar.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jami'ar Temitope Akinbisoye ta fitar, an gayyaci ɗaliban da aka gani a bidiyon a ranar Litinin inda aka yanke masu hukunci kan abin da suka aikata.

    Sanarwar ta ce "bisa tsare-tsaren jami'ar da dokokinta, ɗaliban da aka gani a bidiyon sun bayyana gaban kwamitin ladabtar da ɗalibai na jami'ar a wani taron gaggawa da aka yi ranar Litinin, domin yi masu tambayoyi da bayar da shawarwarin da suka dace, an kuma miƙa rahoton ga hukumar jami'ar."

    "Hukumar jami'ar ta yi allah-wadai da lamarin, da duk wani nau'in cin zarafi ko rashin ɗa'a a jami'armu. Irin wannan ɗabi'a ta ci karo da tsarin mutuntawa da girmamawa da muke tsammanin gani daga ɗalibanmu."

    "Ita kuma Opemiposi Precious Bolaji ƴar aji ɗaya da ke karatu a sashen koyar da aikin jarida da ke dukan abokiyar karatunta da sanda tare da yin barazanar ji mata munanan raunuka a jiki saboda zarginta da lalata soyayyarta ta shekara uku da saurayinta, an same ta da laifi inda aka kore ta nan take."

    Sanarwar ta ƙara cewa "An sami Miss Genesis Osaro, ɗaliba ƴar aji ɗaya da ke karatu a sashen koyar da aikin jarida, wadda ta samar da sandar da aka zane Gloria Ajayi da ita da laifi kuma an kore ta nan take."

    "Gloria Ajayi da aka gani ana duka a bidiyon an wanke ta saboda ba ta ɗauki mataki kan dukan da abokiyar karatunta ta yi mata ba."

    "An kuma gargaɗi Mistura Eniola Adejuwon da Precious Oluwapelumi Olanrewaju da suka naɗi bidiyon da wallafawa a shafin sada zumunta tare da ba su shawarar da su kai rahoton irin haka ga sashen da ke lura da al'amuran ɗalibai da kuma sashen samar da tsaro a jami'ar a maimakon su yaɗa a shafukan sada zumunta."

    A ranar Talata ne kwamishinan ƴan sandan jihar ta Ekiti ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin domin gano masu laifi tare da hukunta su.

  18. Kungiyar agajin Red Cross ta Kenya na neman dala miliyan 50 don rage illar ambaliyar ruwa

    Ƙugiyar agajin Red Cross ta Kenya tace tana buƙatar aƙalla dala miliyan 51.9 domin rage raɗaɗin illar da ambaliyar ruwa yayi a ƙasar acewar rahoton gidan labarai mai zaman kansa Citizan Digital

    Babban sakataren hukumar, Ahmed Idris, ya ce adadin kuɗin zai biya bukatun sama da mutane 47,000 da suka rasa matsugunansu a kananan hukumomi 34.

    Haka kuma za ta kunshi abinci da ruwa da magunguna ga wadanda ambaliyar ruwan ya shafa ya wa rauni.

    "Ba mu taɓa ganin irin wannan girman rasa matsuguni a matsayin kasa ba tun bayan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben ƙasar," in ji Idris, yayin da yake tunawa da tashin hankalin da aka gani a shekarar 2007 da 2008.

    Ambaliyar ruwan da ta yi ajalin mutane kusan 238 da barnata filayen noma ta haifar da fargabar afkuwan karancin abinci da tsadar rayuwa

  19. Hotunan yadda ambaliya ta kusa shafe gine-gine a Brazil

    Mamakon ruwan sama da ya janyo ambaliyar ruwa a sassan jihar Rio Grande do Sul da ke kudancin Brazil ya kusa shafe ɗaruruwan garuruwa.

    Aƙalla mutum 85 ne suka mutu yayin da kusan 150,000 suka rasa gidajensu, a cewar mahukunta.

    An ƙauracewa wasu garuruwan yayin da aka fara cire ran gano mutum sama da 130 da zuwa yanzu ba a gani ba.

    Hasashen masana na makon nan ya nuna ana tsammanin za a ci gaba da samun mamakon ruwan sama wanda zai iya ƙara ta'azzara halin da yankin ke ciki.

    Lamarin ya tilasta wa mazauna yankin barin gidajensu yayin da masu aikin ceto suka mutanen da suka fi rauni.

    Ga wasu hotuna na yadda ambaliyar ta kusa shafe gine-gine a jihar.

    ..
    ..
    ..
    ..
    ..