Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadi sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Hukumar leƙen asirin Amurka ta ce ba Putin ne ya bayar da umarnin kisan Navalny ba

    .

    Kafafen yada labaran Amurka, sun fitar da rahoton hukumar leƙen asirin Amurka wanda ya tabbatar da cewa duk da shugaba Putin na da alhakin kisan Alexei Navalny akwai yiwuwar ba shi ne ya bayar da umarnin kashe shi ba.

    Hukumar ta ce ta dogara ne da bayanan sirri da kuma shaidar da jama'a suka bayar, wadda ta haɗa da lokacin da jagoran adawar ya mutu a gidan kurkuku.

    Wasu rahotanni sun bayyana cewar makwonni kafin mutuwar Mista Navalny, sunansa na cikin waɗanda ake tattaunawa a kansu don musayar fursina.

  3. Hamas ta fitar da sabon bidiyon mutanen da take garkuwa da su

    .
    Image caption: Keith Siegal, mai shekara 64, na cikin sabon bidiyon

    Hamas ta fitar da wani sabon faifan bidiyo da ke nuna wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Gaza.

    A cikin bidiyon na minti uku, Keith Siegel mai shekara 64 da Omri Miran mai shekar 46, sun sun ce suna fatan yarjejeniyar da za ta sa su da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su komawa gida.

    Babu kwanan wata a jikin faifan bidiyon amma ɗaya daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da sun, ya ambaci bikin Idin Yahudawa abinda ke alamta bidiyon sabo ne.

    Wannan dai shi ne bidiyo na biyu da Hamas ta fitar a baya-bayan nan, to amma Isra'ila ta bayyana shi a matsayin farfaganda.

    Dandazon mutane ɗauke da tutar Isra'ila sun yi dafifi a titunan birnin Tel Aviv suna kiran gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen kuɓutar da sauran mutanen da suke tsare

  4. Gane Mini Hanya: Kan Inganta harkokin shari'a a Najeriya

    Wani babban taro don yi wa ɓangaren shari'a garambawul ya amince da Manufar Ƙasa da aka sake bita kan harkokin Shari'a ta 2024-2028, wadda ta fayyace wani jadawali na yin gagarumin gyaran fuska don inganta shari'o'i a kotunan Nijeriya.

    Taron na kwana biyu ya tattaro masu ruwa da tsaki da ƙwararru da tsoffin alƙalai, inda aka faɗa wa juna gaskiya kan yadda talakawan Najeriya ke yanke ƙaunar samun adalci a kotuna, da kuma hatsarin hakan.

    A kan haka ne, BBC ta tattauna da Honarabul Labaran Sha'aibu Magaji, kwamishinan shari'a kuma atoni jinar na jihar Nasarawa, ɗaya daga cikin mahalarta taron.

    Ya kuma fara da tambayarsa maƙasudin shirya babban taron.

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  5. Makarantar da ake zargin Yahaya Bello ya biya kuɗin karatun 'ya'yansa ta mayar wa EFCC kuɗin

    .

    Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya EFCC ta ce makarantar 'American international school' da ke Abuja ta tura dala $760,910.84 zuwa cikin asusun hukumar.

    Kuɗin wani ɓangare na dala 845,852 da ake zargin tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya biya a makarantar don karatun 'ya'yansa biyar da za su yi a makarantar nan gaba.

    Mai magana da yawun hukumar ta EFFC, Wale Oyewale ya shaida wa BBC, cewa tun da farko makarantar ta rubuta wa hukumar takarda, cewa za ta mayar da kuɗin zuwa asusun gwamnati kasancewar hukuma na bincike a kan lamarin.

    Daga nan ne kuma EFCC ta aike wa makarantar asusun da ta sanya kudin a ciki, kamar yadda mista Oyewale ya bayyana .

    EFCCn dai ta yi zargin cewa tsohon gwamnan na Kogi da cire kuɗin daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake jan ragamar jihar, inda ya kai su kasuwar musayar kuɗi, don biyan kuɗin karatun 'ya'yansa har zuwa wasu shekaru masu zuwa a nan gaba.

    A ranar 18 ga watan Afrilu ne dai hukumar EFCC ta ayyana neman Yahaya Bello ruwa-a-jallo, sakamakon zarginsa da ɓarnatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar kogi a lokacin da yake mulkin jihar.

    Bayan hakan ne kuma hukumar shige da fice ta Najeriya ta fitar da wata sanarwa tana umartar jami'an hukumar da su kama shi a duk inda suka gan shi a faɗin ƙasar.

    Hukumar shige da ficen ta kuma aike da kofin sanarwar ga rundunar 'yan sandan ƙasar da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya.

    Haka shi ma babban lauyan gwamnatin ƙasar, kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi, ya buƙaci tsohon gwamnan na Kogi ya miƙa kansa ga hukumar yaƙi da rashawa ta ƙasar.

    Yahaya Bello - wanda shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kogi na huɗu - ya mulki jihar wadda ke tsakiyar Najeriya, har tsawon wa'adi biyu, daga shekarar 2016 zuwa 2024.

    Tsohon gwamnan mai shekara 46, ya kuma tsaya takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023 da ya gabata.

  6. Rigimar Salah da Klopp: Idan na yi magana ɓaci za ta yi - Salah

    .
    Image caption: An ga Mohamed Salah na musayar yawu da Jurgen Klopp a lokacin da yake shirin shiga fafatawar

    Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya ce idan ya daɗi abin da ya shiga tsakaninsa da kocin ƙungiyar Jurgen Klopp a wasan da ƙungiyar ta tashi kunnen doki da West Ham ''ɓaci abin zai yi''.

    An ga Mohamed Salah na musayar yawu da Jurgen Klopp a lokacin da yake shirin shiga fafatawar a minti na 79.

    A nasa ɓangaren, Jurgen Klopp ya ce shi ma ba zai faɗi abin ya shiga tsakaninsa da Salah ba.

    Sai dai tsohon ɗan wasan ƙungiyar Peter Crouch ya faɗa wa kafar yaɗa labarai ta TNT Sport cewa lamarin ba zai zame wa ƙungiyar ''alkairi ba''.

    "Salah ɗan wasa ne da aka fara mafi rinjayen wasannin ƙungiyar da shi, don haka dole ba zai ji daɗi ba idan aka ajiye shi a benchi ," in ji Crouch.

    "Amma ba wanda zai so ganin irin wannan tsamin dangantaka tsakanin fitaccen ɗan wasa da kuma koci."

    An ga alamar Salah ya ji haushi kan wani abu da Klopp ya faɗa masa a lokacin da yake shirin shiga wasan, kuma da alama ya so ci gaba da mayar da martani kafin abokan wasansa Darwin Nunez da Joe Gomez su haƙurƙurtar da shi.

    Sakamakon wasan na nuna cewa Liverpool ta fice daga kokawar ɗaukar kofin Premier na bana.

    Ƙungiyar na mataki na uku, kuma a yanzu fatan da kawai ya rage mata, shi ne Arsenal da Manchester City su yi rashin nasara a wasanninsu na gaba.

  7. 'Yar wasan Brazil Marta za ta rataye takalmanta

    a

    Gwarzuwar Brazil Marta za ta yi ritaya daga bugawa ƙasarta wasa daga wannan shekarar.

    Yar wasan gaban mai shekera 38 ita ce ta fi cewa ƙasarta kwallo masu yawa a tarinhin kwallon ƙafar mata, tana da kwallo 123 cikin wasa 196.

    Idan aka zaɓi Marta a tawagar Brazil za ta buga wasanni shida na gasar Olympics da za a yi a Paris nan da tawanni biyu.

    "Idan naje Olympics zan more kowacce daƙiƙa ta lokacina, saboda ba wai maganar na taɓa zuwa ba ce ko ban taba ba, wannan shi ne Olympics dina na ƙarshe," kamar yadda ta bayyana wa kafar yaɗa labarai ta CNN.

    Ta lashe sarƙar Olympics a 2004 da wanda aka yi a Beijing 2008 kuma duka rashin nasara ta yi a hannun Amurka a wasanni.

    Marta ita ce ta fi yawan cin kwallo a kofin duniya ga ƙasarta Brazil a ɓangaren maza da mata, ta ci kwallo 17 cikin wasa 23 da ta buga a gasa shida da ta halarta.

  8. Bayanai kan yadda za ku samu bashin gwamnatin Najeriya

    Shin kuna buƙatar bashi daga gwamnatin Najeriya don sayen gida ko biyan kuɗin makaranta, amma ba ku san ta ya za ku samu ba?

    Ga cikakken bayani kan Tsarin karɓar kaya bashi da gwamnatin Najeriya ta fito da shi.

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
  9. 'Mun fi kwana 50 babu wutar lantarki a wasu sassan jihar Gombe'

    A

    Al'umma a wasu sassa na shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, na fama da wata matsananciyar matsalar wutar lantarki, wadda ke neman durkusar da harkokin rayuwar yau da kullum a jihohi kamar Adamawa da Taraba da Bauchi da Gombe.

    Matsalar rashin wuta ta yi kamari tun kwanaki shida da suka gabata, a wasu wuraren kuma ana kukan matsalar ta zarta wata guda.

    A jihar Gombe, a yankuna irin na su Liji da Bisije Fantami da Ɓogo da Taura da kuma Manawashi da dai sauran wurare.

    Wani mazaunin jihar da BBC ta zanta da shi, mai suna Yusuf Mahadi Pantami ya ce wutar lantarki ta fi man fetur wahala a wasu sassan jihar ta Gombe

    Ya ce ''matsalar wuta ta fi kwana 50 a wasu sassan jihar, domin kuwa tun cikin azumi muke fama da ita''

    Ruwan da ake samu a jihar Gombe ya ta'allaƙa ne da wutar lantarki da ake turo shi, rashin wutar inda rashin wutar ya sake jefa jihar cikin matsin wahalar ruwan sha.

    A Jalingo jihar Taraba, wurare kamar gidajen yaɗa labarai sun rage lokutan da suke gudanar da ayyukansu, saboda ba za su iya sayen man gas ɗin da ake gudanar da ayyuka ba.

    Faɗuwar turakun wutar da aka samu tsakanin jihar Bauchi da Plateau ne ya haifar da rashin wutar , a daidai lokacin da ake fuskantar matsanancin zafin da aka jima ba a ji irinsa ba a yanki.

  10. Leicester City ta koma gasar Premier bayan an doke Leeds

    a

    Leicester City ta samu tikitin komawa gasar Premier bayan Queens Park Rangers ta doke Leeds United.

    Da kashin da kungiyar ta Daniel Farke 4-0, yanzu akwai tazarar maki hudu tsakaninta da Leicester City da ke matsayi na daya kuma wasa guda ne ya rage.

    Foxes na neman haɗa maki 100 a hanyarsu ta komawa gasar Premier bayan fadawa gasar Championship.

    Yanzu Leicester za ta iya dukan ƙirji ta ce ta lashe kofin sannan kuma ta yi murnar lashewa a gidan Ipswich da ke matsayi na uku.

    Ipswich za ta iya biyo bayan Leicester zuwa Premier idan ta samu maki biyar cikin wasanni uku da suka rage mata.

  11. Saudiyya ta gargadin maniyyata game da kamfanonin bogi

    A

    Ma'aikatar aikin Hajji da Umara ta yi gargadi ga maniyyta aikin hajjin bana da su lura da su lura da kamfanonin bogi da ke tallata kansu a kafafen sada zumunta.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar ma'aikatar ta ce ya kamata maniyyata su sani cewa ana samun bizar aikin Hajji ne kawai ta hannun hukumomin Saudiyya ko kuma hanyoyin da hukuma ta san da zamansu.

    Ma'aikatar ta yaba wa hukumomin majalisar Iraƙi na aikin da suka yi tare domin tabbatar da an kama wasu kamfanonin bogi 25 da suke aiki.

    Irin kuma wannan haɗin kan Ma'aikatar ke fatan ganin an cimma da sauran kamfanonin ƙasashen duniya domin kama wandanda ba su da izinin gudanar da ayyukan Hajji da Umra.Ta kuma shawarci al'umma su zama ma su sanya idanu tare da shigar da rahoton duk wani kamfanin da suke zargi da ke tallan kansa.

  12. Guguwa ta afka wa wasu garuruwan Amurka

    BBC

    Guguwa sama da 70 ta afka wa tsakiyar birnin Amurka, inda ta tafka barna a yankunan Nebraska da Iowa, tare da lalata gidaje da jikkata akalla mutum uku.

    Akasari iskar ta fi shakar yankin Omaha da ke Nebraska.

    'Yan sanda yankin na cigaba da auna girma barnar da gidajen da suka lalace da kuma agazawa wadanda suka jikkata.

    Kusan gidaje dubu 11 guguwar ta kastewa wutar lantarki.

    Sannan mahukunta Amurka na gargadin mutane da su kasance cikin shiri saboda za a cigaba da fuskantar irin wannan gugguwa har zuwa yankun Texas da ke kudancin kasa

  13. Za a shafe shekaru 14 ba a gyara Gaza ba - MDD

    A

    Tarkace da aka bari a Gaza ta ko ina sakamakon hare-haren Isra'ila ciki harda abubuwan fashewar da aka harba ba su kai ga fashewa ba, za a dauki shekaru 14 ba a gama kwashe su ba, in ji MDD.

    Per Lodhamar ya yi bayanin cewa akwai tan miliyan 37 na ɓaraguzan da yaƙin ya bari a yankuna da suke da yawan jama'a, "kimanin kilogiram 300 na shara mai faɗin murabba'i."

    Da yake magana a wani taron manema labarai a Geneva ya ce duk da cewa babu wanda ya san adadin abubuwan fashewar da ke ƙasa ba ba su fashewa, amma yana zaton za a share shekara 14 kafin kwashe ɓaraguzan ginin da suka lalace.

    "Mun san cewa akwai kimanin kashi 10 na abubuwan da ba su fashe ba a yankin a yanzu," in ji shi.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce wakin Isra'ila ya mayar da Gaza wani wurin da ya fi ko ina buƙatar taimako, kuma ana fargabar za a iya fuskantar yunwa a nan gaba a Gaza.

  14. Liverpool ta ayyana wanda zai maye gurbin Klopp

    A

    Liverpool ta bayyana sunan Arne Slot a matsayin wanda zai maye gurbin kocinta Jorgen Klopp da zai bar ƙungiyar a ƙarshen wannan kakar da muke ciki.

    An cimma wannan yarjejeniya ne bayan biyan Feyernoord diyyar yuro miliyan 9.4 kafin su amince da yarjejeniyar.

    Dan ƙasar Netherland ɗin shi ne zai gaji Jurgen Klopp da zai bar Anfield a ƙarshen kakar 2023-24.

    Yanzu ƙungiyar za ta cimma yarjejeniyar zaman kocin mai shekara 45 gabanin ta naɗa shi a matsayin kocinta a hukumance.

    Liverpool ta amince da cewa za ta biya fan miliyan 7.7 da kuma ƙarin miliyan 1.7 a matsayin kudaden tsurfa.

  15. 'Ya kamata a rinƙa yi wa malaman jami'an Najeriya gwajin kwaya'

    A

    Shugaban Jam'iar Abubakar Tafawa Balewa ATBU da ke Jihar Bauchi, Farfesa Muhammad AbdulAziz ya nemi a riƙa yiwa malaman jami'a gwajin shan kwaya ba iya ɗalibai ba kawai.

    Ya yi wannan batu ne lokacin da yake bayanin bankwana ga majalisar jami'ar a jiya Juma'a.

    Ya ce " Ina ganin idan har za a riƙa yi wa ɗalibai irin wannan gwaji na shan kwaya, ina ganin mune ahaƙƙu da a yiwa, mu ma'aikata muma a mana ba kawai mu riƙa cewa a yi wa dalibai ba kawai."

    "Mu ma mu mika kanmu a yi mana wannan gwajin domin mu tsaftace jami'o'inmu. Halayen arziki na da muhimmanci a wurinmu baki ɗaya.

    "Idan har za a umarci dalibanka da su je su yi wannan gwajin domin tabbatar da lafiyar kwakwalwarsu, ina ganin babu wani abun damuwa idan suka malaman an yi musu irin gwajin. Ina ganin wannan ce hanyar daya da za a tabbatar da komai a jami'o'i," in ji Farfesan.

  16. An cimma yarjejeniyar samar da irin shinkafa tsakanin Najeriya da Japan

    A

    Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar da za ta taimaka wajen samar da irin shinkafa mai inganci tsakaninta da Japan.

    Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Atiku Bagudu ne ya sanya hannun a madadin gwamnatin kan yarjejeniyar.

    Ya ce Japan ta cimma abubuwa da dama ta bangaren aikin noma musamman samar da shinkafa da kuma noma ta hanyar fasaha.

    Japan ta ce za ta taimakawa ƙananan ma'aikata domin su samar da shinkafa ma'ana su mori ƙasar da suke rayuwa a cikinta.

    Babban burin shi ne taimakawa kowa a Najeriya, amma musamman kananan manoma.

  17. Sarki Charles zai koma ofis bayan an masa aiki kan cutar kansa

    A

    Sarki Charles zai koma aiki makon gobe bayan ci gaban da aka samu a rashin lafiyar kansa da yake fama da ita, kamar yadda fadar Buchingham ta bayyana.

    Hakan baya nufin ya gama warkewa baki ɗaya, amma dai fadar ta ce jikinsa ya yi kyau sosai.

    Sarkin zai sake komawa cibiyar da ake lura da masu kansa a ranar Talata mai zuwa.

    A tsare-tsaren da suke gabansa lokacin bazara, zai karɓi baƙuncin Sarki da Sarauniyar Japan.

    A makonni masu zuwa kuma fadar tace akwai wasu ayyuka da zai gudanar da suka shafi harkokin lamuran ƙasashen waje.

  18. Muna nazari kan buƙatar Isra'ila ta tsagaita wuta a Gaza - Hamas

    A

    Hamas ta ce tana nazatar daftarin yarjejeniyar da Isra'ila ta gabatar kan yiwuwar tsagaita wuta a Gaza.

    An gaggara cimma daidaituwa, inda a baya Hamas ta bukaci a tsagaita wutar dindindin na yakin da aka kwashe watanni shida ana fafatawa, ita kuma za ta saki fursunonin Isra'ila.

    Sai dai Isra'ila tayi watsi da tayin Hamas, inda ta fi mayar da hankali ko neman tsagaita wutar na wucin gadi.

    Jakadan Masar ya je Isra'ila a jiya Juma'a, a kokarin ganin ya sake farfado da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu domin kawo karshen wannan yaki.

  19. An kashe fitacciyar 'yar TikTok a Iraƙi

    A

    Jami'an tsaro a Iraki sun ce wani dan bindiga da ba a gane daga ina ya fito ba, ya harbe wata fitacciyar 'yar Tiktok a wajen gidanta da ke Bagadaza har lahira.

    Om Fahad sananiya ce wajen wallafa bidiyoyi tana rawa sanye da tufafi masu kama jiki.

    A shekarar da ta gabata kotu ta yanke mata hukuncin dauri wata shida saboda nuna rashin da'a da saɓa dokokin kasar a irin bidiyoyin da take wallafawa a shafukanta na sada zumunta.

    Iraki dai ta kafa wani kwamiti karkashin ma'aikatar cikin gida, da ke sa ido da bibbiyar irin waɗannan mutane da take ganin suna saɓa ka idoji, addini da al'adun kasar a irin abubuwan da ke suke watsawa a kafofinsu na sada zumunta.

  20. Ukraine ta kai hari kan matatar mai a Rasha

    A

    Ukraine ta kai hari kan wata matatar mai da ke kudancin Rasha da jirage marasa matuka.

    Gwamnan yankin Krasnodar ya ce sun yi nasarar kakkabo 10, Kuma babu asarar rai ko mutumin da ya samu mumunan rauni.

    Amma hotunan bidiyo da ke yawo na nuna yadda harin ya haddasa gagarumar gobara a matatar Slavyansk.

    Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da Amurka ta sanar da tallafin bilyoyin daloli na kayayyakin yaki ga Ukraine.

    Ukraine a 'yan kwanakin nan na kara kaimi wajen amfani da irin wadannan jirage a hare-haren da take kai wa Rasha a matsayin martani kan luguden wuta da barnar da Rasha ta tafka mata a birane da gine-gine masu muhimmanci.