Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Fauziyya Kabir Tukur

time_stated_uk

  1. Rufewa

    A nan za mu rufe wannan shafin da muke kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da suka shafi Najeriya da sassan duniya.

    Sai kuma gobe Idan Allah Ya kai mu. Da fatan za ku ci gaba da kasance da mu domin sanin halin da duniya ta ke ciki.

  2. An fara shari’ar ɗan tawayen da ya tafka ta’asa a Liberia

    Jibril Ealoghima Massaquoi
    Image caption: Jibril Ealoghima Massaquoi ya musanta zarge-zargen da ake masa

    An fara shari'ar wani madugun 'yan tawayen Liberia a kasar Finland wanda ake zargi da aikata ta'asa a lokacin yakin basasar kasar Liberia.

    Masu gabatar da kara sun ce Jibril Ealoghima Massaquoi daga Saliyo ya kasance wani kusa a wata kungiyar 'yan tawayen da ta yi yaki a Liberia daga 1999 zuwa 2003.

    Ana zarginsa da kashe fararen hula da kuma sojojin da ba a dade da karbe makamansu ba.

    Haka nan kuma an zarginsa da aikata fyade da kuma daukar kananan yara a sa su aikin soja.

    Jibril ya musanta zargin da ake masa yana cewa shi a lokacin yana daga cikin masu kokarin sasantawa ne a samar da zaman lafiya.

  3. Isra'ila ta rusa wani ƙauye a yankin Falasdinawa

    Isra'ila na rusa matsugunin Falasdinawa

    An yi amfani da manyan motoci domin rusa gidaje a ƙauyen

    Tun a watan Nuwamba aka rusa ƙauyen karon farko, amma mazauna ƙauyen suka dawo da zama.

    Isra'ila ta ce Falasdinawa sun yi ginin ne ba bisa kan doka ba wanda ke kusa da wani sansanin sojoji.

    Ta ce mazauna ƙauyen sun ƙi amincewa da tayin da aka yi masu na su tashi su koma wani kusa da ƙauye

    Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam B'Tselem, ta Isra'ila ta ce rusau ɗin yana cikin wani yunƙuri na raba Faladinawa da matsuguninsu tare da kwace filayensu.

  4. Labaran BBC cikin minti ɗaya

    Video content

    Video caption: Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 03/02/2021
  5. Ƴan bindiga sun kashe sojojin Mali 9

    Sojoji 9 sun rasa rayukansu a wani hari da mayaƙa masu da'awar jihadi suka kai wani sansanin sojoji a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar Mali.

    Mayakan sun tarwatsa Sansanin da ke Boni tare da wawushe makamai.

    Masu tayar da kayar bayan suna cikin motocin sulke wadanda ake tunanin sun karbe daga hannun sojoji a wani samame da suka kai a baya a kasashen Burkina Faso, da Nijar ko Mali.

    SojojinMali sun ce sun samu taimakon jirage ta sama daga sojojin Faransa da ke da sansani a yankin Sahel.

    Sun ce daga baya an kashe maharan da dama.

    Yankin ya kasance wata matattarar sojojin hadin gwiwa tsakanin Mali da Faransa.

    A watan jiya sojojin sun ce an kashe daruruwan mayaka.

  6. Wata ƙungiya ta kai ƙarar NAFDAC kotu kan sakaci da aiki

    An kai ƙarar NAFDAC game da yadda kamfanoni ke sayar da magungunan tari da aka haramta
    Image caption: An kai ƙarar NAFDAC game da yadda kamfanoni ke sayar da magungunan tari da aka haramta

    Wata kungiya mai fafutikar yaki da shan miyagun kwayoyi a Najeriya mai suna Society for Drug Enlightenment and Control SODEAC, ta kai kakar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa wato NAFDAC da kuma wasu kamfanonin harhada magunguna guda uku.

    Ta kai kararsu ne kotu dangane da sakamakon wani rahoton binciken kwakwaf da shirin BBC Afria Eye ya yi a 2018 game da yadda kamfanonin ke sayar da magungunan tari masu dauke da sinadarin Codeine wanda matasa da dama kan sha su bugu.

    Kungiyar dai na neman wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta duba zargin rashin gudanar da aikin sa ido yadda ya kamata a bangaren NAFDAC,sannan ta duba zargin cewa kamfanonin na sayar da magungunan tarin ba bisa ka’ida ba lamarin da ke illa ga dimbin matasan kasar.

    A zaman kotun na yau, an dage cikakken sauraren karar zuwa ranar 17 ga watan Maris, bayan amincewar lauyoyin bangarorin da suka halarci zaman na ranar Laraba

  7. Kotun ICC ta amince ta saurari koken Iran kan takunkuman Amurka

    Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta amince ta saurari ƙarar da Iran ta shigar tana ƙalubalantar takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba mata.

    Alƙalai shida da kotun da ke Hague sun amince cewa taƙadammar tana cikin ikonsu.

    Sun kuma yi watsi da yunƙurin Amurka na soke shari'ar.

    Amurka, ƙarkashi mulkin Trump ta ƙaƙaba takunkumai ga Iran, wanda ya raunata tattalin arzikin ƙasar. Amurka ta don tilastawa Iran ta amince a sake zama kan sabuwar yarjejeniyar Nukiliya.

    ICC
  8. Faransa ta damu da yadda Morocco ke saye masallatan ƙasar

    Babban Masallacin Paris a Faransa
    Image caption: Babban Masallacin Paris a Faransa

    Rahotanni daga Faransa sun ce yadda Morocco ke saye masallatan ƙasar ya janyo muhawara a majalisar Faransa.

    Jaridar L'Opinion a Faransa ta buga labari inda ta ce maajalisar dokokin Faransa na shirin mayar da martani ga Marocco kan yadda ta ke saye masallatanta.

    Jaridar ta kuma ce an tafka muhawara tsakanin ƴan majalisar game da batun musamman a daidai lokacin da ƙasar ke yaƙi da tsatsauran ra’ayin addini a Faransa.

    Jaridar L'Opinion ta ce ma’aikatar lamurran addini ta Morocco ta yi alƙawalin sayen wani masallaci kan yuro miliyan 4.5 wanda ake kan gininsa a Angers.

    Haka kuma Masallacin Puteaux wanda ake ginawa tun shekara ta 2011, shi ma yana iya zama mallakin ma'aikatar harakokin addinin Morocco, abin da ke haifar da martani tsakanin masu ibada da suka bayar da tallafi.

    A cikin 'yan shekarun nan, Morocco ta shiga aikin gina wa ko gyaran masallatai a Strasbourg, da Mantes-la-Jolie da Saint-Etienne da Evry. Ta ma riga ta mallaki biyu daga cikinsu.

    Ƴan majalisar Faransa na fargabar cewa sauran wuraren ibada a Montpellier da Argenteuil da Carpentras na iya zama mallakar masarautar.

    Akwai ƙudiri da ke gaban majalisar bayan batun ya janyo muhawara inda masu ibada da ƴan siyasa ke bayyana adawa da mallakar masallatan da Moroco ke yi.

  9. EFCC ta ce ta kama masu satar ATM suna wawushe kuɗaɗen mutane

    Hukumar EFCC a Najeriya ta ce ta kama wasu mutum biyu ƴan uwan juna da ta ke zargi suna satar abin cirar kuɗi na ATM suna wawushe kuɗaɗen mutane.

    Hukumar ta ce jami'an ofishinta da ke Makurdi jihar Benue ne suka kama mutanen biyu a ranar Laraba.

    Hukumar ta ce suna satar ATM sannan su cire kuɗin ta hanyar amfani da na'urar cirar kuɗi ta POS.

    Kuma suna da asusun banki da dama da suke aikata ɗanyen aikin.

    EFCC ta ce ta samu katin ATM 29 na bankuna da dama na mutane daban daban hannunsu da kuɗi da kuma wayoyin salula.

    Hukumar ta ce idan ta kammala bincike za ta maka su kotu.

    View more on twitter
  10. Jam'iyyar MNSD Nasara ta goyi bayan Bazoum Mohamed a zaɓen Nijar

    Jam'iyar MNSD Nasara ta tsohon shugaban ƙasa marigayi Tandja ta bayyana aniyarta na marawa ɗan takara Bazoum Mohamed a zaben Nijar.

    Za a tafi zagaye na biyu tsakanin Bazoum Mohamed ɗan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya da kuma tsohon shugaban ƙasa Mohamane Ousmane ɗan takarar jam'iyyar PJP a ranar 21 ga wannan wata na Fabrairu.

    Ƴan takarar biyu na samun goyon bayan sauran jam'iyyu kafin zaɓen yayin da aka fara yaƙin neman zaɓe zagaye na biyu.

    Bazoum wanda ya zo na farko a zagaye na farko ya kasa samun sama da kashi 50 na yawan ƙuri'u.

    Jam'iyyar MNSD
  11. Janar Djibo ya goyi bayan Mahamane Ousmane don kada Bazoum a zaɓen Nijar

    Tsohon shugaban mulkin soja na Nijar Janar Salou Djibo ya goyi bayan takarar tsohon shugaban ƙasa Mahamane Ousmane a zaɓen ƙasar zagaye na biyu da za’a gudanar a ranar 21 ga Fabrairu.

    Janar Djibo wanda ya zo na shida a zagayen farko ya ce da shi da jam’iyyarsa ta PJP Dubara ta zaɓi canji don haka ta goyi bayan takarar tsohon shugaba Mahamane Ousmane, kamar yadda jaridar L'Evenement ta ruwaito

    Mahamane Ousmane wanda ya zo na biyu a zagayen farko, tun kafin zaɓen ya samu goyon bayan madugun adawar ƙasar tsohon Firaminista Hama Amadou.

    Za a tafi zagaye na biyu ne a zaɓen shugaban ƙasa a Nijar tsakanin ɗan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya Bazaoum Mahamane da Mahamane Ousmane bayan babu wanda ya samu sama da kashi 50 na yawan ƙuri’u.

    Janar Djibo
  12. Babu yadda za a samar da rigakafin da zai halaka jama'a - Boss Mustapha

    Boss Mustapha

    Gwamnatin Najeriya ta kawar da fargaba dangane da ra’ayoyi da rashin fahimta da wasu ƴan ƙasar ke nuna wa kan cewa an samar da rigakafin korona ne domin “kashe ƴan Afrika.”

    Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da annobar korona a Najeriya ya ce babu wanda zai kashe biliyoyin daloli da nufin samar da rigakafi don kashe mutane a Afrika.

    Gwamnatin Najeriya dai na fuskantar aikin wayar da kan al’ummar ƙasar kan ingancin rigakafin cutar korona.

    Wasu ƴan ƙasar da dama na bayyana fargaba cewa rigakafin barazana ce ga lafiyar ƴan Afirka, tunanin da Boss Mustapha ya yi watsi da shi.

    Yawan masu kamuwa da korona a Najeriya na ci gaba da ƙaruwa, inda a ranar Talata mutum sama da 1,600 suka kamu da cutar.

    Najeriya ta ce ta yi odar allurar rigakafi miliyan 57 da ta ce tana fatan yi wa kashi 40 na ƴan ƙasar a wannan shekarar.

  13. Harin garin Sabuwa a jihar Katsina ya yi sanadin mutuwar mutum 13

    Gunmen

    An yi jana’izar wasu mutum 11 daga cikin 13 da ‘yan bindiga suka kashe a jiya Talata a garin Sabuwa da ke jihar Katsina.

    Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun far wa duk wanda suka yi tozali da shi ne a lokacin da suka shigo garin da asubahin ranar Talata.

    "Yara na dibar yashi a kan amalanken shanu lokacin da barayin dajin suka shigo suka ce su ba su shanun. Sai suka ba su.

    "Yaran sun dawo cikin gari suka bayyana abin da ya faru to sai aka taru aka bi barayin aka je aka karbo shanun da suka karba," a cewarsa.

    Mutumin ya ce ashe barayin sun koma sun sanar da 'yan uwansu, nan da nan sai suka dawo suka far wa garin suka kama kashe mutane.

    Ya ce barayin sun yi ayari ne a kan babura da yawansu ya kai dari suka shigo garin dauke da makamai.

    "Da suka shigo sai suka rarrabu, dama a baburan sun yi goyon mutum bibbiyu ne wasu kuma uku-uku. Wasu suka nufi kasuwa suka samu mutane suka kashe a nan ma," in ji shi.

    Ya ce jami'an tsaro ba su je inda tushen harin yake ba iyaka dai sun je kusa da garin amma babu wani mataki da ya ga an dauka.

    ‘Yan bindiga dai na ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin arewa maso yammacin Najeriya, duk da ikrarin da hukumomi ke yi na kokarin shawo kan al’amarin.

  14. Habasha ta musanta kashe mutum sama da 50,000 a Tigray

    Masu sukar gwamnati sun ce rikicin ya yi sanadiyyar dubban mutane

    Gwamnatin Ethiopia ta yi watsi da rahotanni da ke nuna cewa dubban fararen hula ne suka mutu a rikicin arewacin yanki Tigray.

    A ranar Talata ne jam'iyyun adawa uku a Tigray suka zargi sojojin Habasha da na Eritrea da aika manyan laifuka kuma fararen hula 52,000 ne aka kashe.

    Gwamnatin Ethiopia ta bayyana zargin a matsayin marar tushe kuma da kuma bi-ta-da-ƙullin siyasa.

    Haka kuma gwamnatin Ethiopian ta nuna rashin jin dadinta kan mutuwar duk wani farar hula yayin rikicin, inda ta ce adadin da ake ikirarin sun mutu, bai kai haka ba, saboda kwarewa ta sojojin kasar.

    A bangare guda kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ana cikin mummunan yanayi na matsi a yankin, kuma gwamnatin kasar na ta hana ma'aikatanta na bayar da agaji zuwa yankin.

  15. Za a fara raba magunguna da jirgi marar matuƙi a Kaduna

    Nasir El Rufa'i

    Gwamna Nasir El-Rufai na jihar kaduna ya sanya hannu a wata yarjejeniya da wani kamfani mai suna Zipline kan wani tsari na raba magunguna a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya ta hanyar amfani da ƙananan jirage masu sarrafa kawunansu (drones).

    Sanarwar da ta fito daga tawagar gwamnan ta yada labarai ta ce Gwamna El-Rufai ya ce wannan kamfani na Zipline na Kasar Amurka wanda ke da reshe a Ghana ya zabi Jihar Kaduna ne don ganin irin yadda jihar ta dauki sha’anin kiwon lafiya da muhimmanci.

    Gwamnan ya kara da cewa, “ wannan tsari zai taimaka mana wurin rarraba magani da allurar riga-kafi zuwa duk lunguna da sakunan da ke jihar nan musamman inda muke fama da matsalolin tsaro kamar Birnin Gwari da Chikun.

    Haka kuma, ya ce jirgin na da firij wanda zai kare ingancin magungunan kafin su isa inda ya kamata.

    "Kuma za su rika isa inda ya kamata cikin sauri a ko ina a fadin jihar Kaduna. Nan da ƙarshen watan Maris za a fara wannan tsari," a cewar El-Rufa'i.

    Sannan wannan tsarin zai taimaka mana wurin samar da ayyukan yi ga matasanmu tunda a nan Kaduna za su rika kera wadannan jirage masu sarrafa kawunansu”, a cewar gwamnan.

  16. Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Rana

    Ku saurari Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Rana, wanda Halima Umar Saleh ta karanta.

    Video content

    Video caption: Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Rana 03/02/2021
  17. INEC za ta samar da sabbin mazaɓu a faɗin Najeriya kafin zaɓen 2023

    Mahmoud Yakubu

    Gabanin zaɓukan 2023 da za a gudanar a Najeriya, hukumar zaɓe ta INEC ta fara shirye-shiryen samar da ƙarin mazaɓu a faɗin ƙasar.

    Shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe (IVEC), Festus Okoye ya bayyana haka a Abuja kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Jaridar ta ruwaito cewa a watan Agustan 2014 INEC ta gabatar da buƙatar samar da ƙarin mazaɓu 30, 027, inda arewacin ƙasar za ta samu muazaɓun 21,615 yayin da kudu za ta samu 8,412.

    Wannan ya janyo ce-ce-ku-cen da ya sa INEC ta watsar da shirin.

    Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa a halin yanzu Najeriya ba ta da isassun mazaɓu.

  18. Coronavirus: Saudiyya ta dakatar da ƴan wasu kasashe daga shiga ƙasarta

    King Salman

    Jaridar Saudi Gazette ta Saudiyya ta ruwaito cewa kasar ta dakatar da shiga ga wadanda ba ƴan kasar ba ciki har da jakadan kasashe da ma'aikatan lafiya da iyalansu.

    Wannan matakin dai zai shafi kasashe 20 ne yayin da Saudiyyar ke ƙoƙarin yaki da annobar korona.

    Rahoton ya bayyana ƙasashen da abin ya shafa sun haɗa da:

    Argentina da Haɗaɗɗiay Daular Larabawa da Jamus da Amurka da Indonesiya da Ireland da Italiya da Pakistan da Brazil da Portugal da Burtaniya da Turkiyya da Afrika ta Kudu da Sweden da Switzerland da Faransa da Lebanon da Masar da Indiya da Japan.

    Dokar za ta fara aiki da ƙarfe 9 na dare (agogon Saudiyya) ranar Laraba 3 ga watan Fabrairu.

    Haka kuma, dokar za ta shafi matafiya ƴan wasu kasashe da suka ratsa da waɗannan ƙasashe 2o da muka sa wa haramcin," a cewar jaridar.

    Ƙarin labarai:

  19. Ƙungiyar G7 ta bukaci sojoji a Myanmar su sako Aung San Suu Kyi

    Aung San Suu Kyi

    Ƙungiyar ƙasashe masu karfin arziƙi ta G7 ta yi kira ga rundunar sojin Myanmar da su saki shugabannin da suka kama ciki har da Aung San Suu Kyi.

    Ranar Talata, Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ba ta ce uffan ba kan juyin mulkin da aka yi ƙasar saboda China ta soki hakan.

    Kafar yada labarai a China ta bayyana abubuwan da suka faru a Myanmar a matsayin "sauya ministoci".

    A Myanmar, wasu ma'aikatan lafiya a birane sun bayyana cewa ba za su bai wa sojoji goyon baya ba.

    Ƴan Myanmar mazuna Japan da Australiya sun shirya zanga-zanga don nuna adawa da juyin mulki.

  20. Ɗan Iran ya tsere Burtaniya da ƙafa don gudun dauri a gidan kaso

    KAMEEL AHMADY

    Wani malamin makaranta ɗan asalin Iran kuma ɗan ƙasa a Burtaniya da ke fuskantar ɗaurin shekara 9 a gidan yari ya tsere daga Iran ɗin don fara sabuwar rayuwa a Burtaniya.

    An yanke wa Kameel Ahmady hukuncin ɗaurin ne watanni biyu da suka gabata bisa laifin haɗa kai da gwamnatin Burtaniya, laifin da ya musanta.

    An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 9 da watanni a gidan yari kuma an ci shi tarar sama da fam dubu ɗari biyar.

    Sai dai da aka ba da belinsa kuma ya ɗaukaka kara, ya tsere daga Iran, inda ya tsallake manyan duwatsu da ƙafa don gujewa jami'an tsaron ƙasar.

    Ahmady ya bayyana balaguron a matsayin mai tsananin wahala.

    An haifi Mista Ahmady a yammacin Iran amma iyayensa sun tura shi karatu Burtaniya a lokacin da yake da shekaru 18.

    Ya kasance a can tsawon shekaru, yana karatu a Jami'ar kent da Kwalejin Tattalin Arziki na Landan.

    Ya nemi takardar zama ɗan Burtaniya saboda soyayyar da yake yi wa kasar, kafin daga baya ya koma Iran a matsayin mai binciken tarihin ɗan Adam.

    Bincikensa ya mayar da hankali ne kan auren wuri da kaciyar mata a Iran. Wannan ya sa hukumomi suka sa masa ido saboda yana kira da a daina yi wa yara mata aure suna da shekaru 13.

    Sai dai a a yanzu ba a san matakin da Iran za ta ɗauka ba kuma laifinsa na iya shafar laifin wasu ƴan ƙasar da ke da shaidar zama ƴan Iran.