Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Mutum bakwai ciki har da ƙananan yara sun mutu a harin da Rasha ta kai Ukraine

    .

    Jami'an Ukraine sun ce wasu hare-hare guda biyu da Rasha ta kai yankin Dnipropetrovsk da ke tsakiyar Ukraine sun yi sanadin mutuwar mutum bakwai ciki har da ƙananan yara biyu.

    An kai hari kan tashar mota a birnin Dnipro, sannan aka kai wani harin tare da lalata gidaje da dama a gabashin Synelnykove.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce hare-haren sun nuna cewa biranen Ukraine na buƙatar na'urorin kakkaɓo makamai.

    A wani harin na daban, Ukraine ta ce a karon farko ta harbo wani bam mai dogon zango da Rasha ta harba cikin ƙasar.

    Jami'ai sun ce wani ƙaramin yaro mai shekara takwas, da wata yarinya mai shekara 14 na daga cikin mutum biyar da aka kashe a wani gida da hare-haren Rashar suka faɗa a Synelnykove.

  3. Belgium ta ce za ta shigar da Rwanda ƙara zuwa Kotun Duniya

    Jakadan Belgium a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo ya ce ya kamata ƙasar ta shigar da ƙara Kotun Duniya a kan gazawar Rwanda na mutunta mata iyakoki.

    Da yake jawabi a wajen wani taro da ake a kan yadda za a shawo kan rikicin gabashin Congo, Roxane de Bildering, ya ce binciken da Majalisar Dinkin Duniya suka yi ya nuna cewa Rwanda na goyon bayan 'yan tawayen M23.

    Dakarun Kongo na ta ƙoƙari wajen magance hare-haren 'yan tawayen.

    Mai magana da yawun gwamnatin Rwanda ya ce gara Kongo ta kai tsohuwar ƙasar da ta yi mata mulkin mallaka zuwa kotun saboda kisan kiyashin da aka yi a lokacin mulkin mallaka.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce faɗan da ake a gabashin Congo ya raba mutane fiye da dubu 700 da muhallansu a ciki watanni uku na farkon shekarar da muke ciki.

  4. An kama mutum uku kan harin da aka kai wa abokin Navalny

    ..

    An kama mutum uku kan wani hari da aka kai wa babban mashawarcin jagoran adawan Rasha da ya mutu Alexei Navalny.

    Leonid Volkov, ya ce an karya masa kafaɗa a wani hari da aka kai masa a gidansa da ke Vilnius, babban birnin Lithuania cikin watan Maris da ya gabata.

    Firaministan Poland ya ce mutumin da ake zargi da kitsa harin ɗan ƙasar Belarus ne da ke yi wa Rasha aiki.

    An yi zargin cewa wasu 'yan ƙasar Poland magoya bayan wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar da kai harin.

    Tun da farko, hukumar leƙen asirin Lithuania ta ce akwai yiwuwar 'Rasha ce ta shirya harin''.

    A watan Fabrairu ne dai jagoran adawar Rasha Alexei Nanalny ya mutu a wani gidan yarin da yake tsare, cikin wani yanayi da ya janyo ruɗani.

  5. Wani mutum ya cinna wa kansa wuta a wajen harabar kotun da ake sauraron ƙarar Trump

    ..

    Wani matashi ya cinna wa kansa wuta bayan watsawa kansa wani abu mai ruwa-ruwa a wajen harabar kotun da ake sauraron ƙarar tsohon shugaban Amurka, Donal Trump Trump.

    Manema labaran da ke kawo yadda zaman kotun ke gudana, sun ga yadda lamarin ya faru, inda mutane suka fara kururuwa a wurin.

    Akwai tarin jami'an 'yan sanda - waɗanda suka ruga inda lamarin ke faruwa suna kiran a kunna tukunyar kashe gobara.

    Duk da cewa jikinsa ya ƙone sosai, an samu nasarar ceto shi tare da ɗora shi a gadon marasa lafiya, inda aka garzaya da shi asibiti.

    Kawo yanzu dai ba a san dalilin da ya sa mutumin ya cinna wa kansa wutar ba.

    Tuni dai jami'an 'yan sandan New York suka hallara inda lamarin ya faru.

  6. Adadin mutanen da aka kashe a Gaza sun haura 34,000 - Ma'aikatar lafiyar Hamas

    Ma'aikatar Lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren Isra'ila a Gaza sun kai 34,012.

    Cikin wata sanarwar da ta fitar a shafinta na Telegram, ma'aikatar ta ce wasu ƙarin mutum 42 ne aka kashe tare da jikkata 63 cikin kwana guda da ya gabata.

    Jimillar mutanen da suka jikkata sakamakon rikicin sun kai mutum 76,833, kamar yadda ma'aikatar ta nuna

  7. Isra'ila ta kai hari kusa ta tashar nukiliyar Iran - Amurka

    Wani babban jami'in Amurka ya ce Isra'ila ta kai hari kan na'urorin kakkaɓo makamai da ke kusa da Isfahan - wanda shi ne ke kare tashar nukiyar Iran ta Natanz, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta ABC ta ruwaito.

    Jami'an ya shaida wa kafar cewa makamai masu linzami uku ne wani jirgin saman Isra'ila ya harba a wajen Iran ranar Juma'a, kuma binciken farko ya nuna cewa an lalata inda na'urorin suke.

    Tun da farko, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato ministan harkokin wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian na cewa harin na Isra'ila bai haddasa rasa rai ko yin wata ɓarna.

  8. Ecowas ta ware dala miliyan 25 don yaƙi da ta'addanci a Najeriya da Nijar

    Ecowas
    Image caption: Shugaban Najeriya Bola Tinubu ne jagoran shugabannin ƙasashen ƙungiyar ta Ecowas mai hedikwata a Abuja

    Ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ware dala miliyan 25 da zimmar yaƙi da ta'addanci a ƙasashen Najeriya, da Nijar, da Mali, da Burkina Faso.

    Ecowas ta tsara kashe kuɗin ne a shekarar 2024, kamar yadda Kwamashinar Raya Al'umma ta Ecowas Farfesa Fatou Sarr ta bayyana a hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja yau Juma'a.

    Farfesar ta ce an ware miliyan huɗu daga cikin kuɗin don ayyukan agaji musamman ga mutanen da bala'o'i suka shafa.

    "Haka nan, Ecowas ta ware dala miliyan ɗaya da zimmar daidaita rayuwar mutanen da ta'addanci ya shafa, kamar 'yan gudun hijira da kuma waɗanda aka ji wa rauni," in ji ta cikin rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.

    Ta ƙara da cewa a 2023 kaɗai, Ecowas ta ba da tallafin dala miliyan 12.6 ga mutane sama da miliyan huɗu da ta'addanci ya shafa a yammacin Afirka

  9. 'Yansandan Faransa sun kama mutum kan yunƙurin kai hari ofishin jakadancin Iran

    Paris

    'Yansanda a birnin Paris na Faransa sun kama wani mutum da aka gani yana shiga ƙaramin ofishin jakadancin Iran.

    Dakarun 'yansandan sun kewaye ginin ne bayan wani mutum ya ce ya ga mutumin ya shiga ginin ɗauke da gurneti ko kuma wani abin fashewa.

    Rahotonni sun ce mutumin ya fice daga ginin daga baya, inda aka kama mutumin da misalin ƙarfe 2:45 agogon Paris.

    Hotunan da aka ɗauka daga wurin sun nuna yadda 'yansandan suka kama mutumin a kusa da ginin, sannan suka caje shi kuma ba su ga wani abin fashewa a jikinsa ba.

    Tun da farko rahotonni sun ce mutumin ya shiga ginin da misalin ƙarfe 11:00 na safe yana cewa zai ɗauki fansar kisan ɗan uwansa.

  10. Masu zanga-zanga a Iran na yin tir da Isra'ila

    Tehran

    Ɗaruruwan mutane sun hau kan titunan birnin Tehran na Iran ɗauke da take iri-iri na yin tir da Isra'ila.

    Kazalika wasu da yawa sun riƙe tutocin ƙasar da kuma na Falasɗinawa.

    Da yawan waɗanda suka taru sun kuma riƙe hotunan jagoran addini na ƙasar, Ayotollah Ali Khamenei.

    Zanga-zangar na zuwa ne awanni bayan harin da Isra'ilar ta kai yankin Isfahan mai ɗumbin tarihi a matsayin ramuwa kan harin da Iran ta kai mata a makon da ya wuce.

    Tehran
  11. Farashin man fetur ya tashi bayan harin da Isra'ila ta kai wa Iran

    ..

    Farashin man fetur da na zinare sun yi tashin gwauron zabi bayan da jami'an Amurka suka ce Isra'ila ta kai wa Iran hari da makami masu linzami inda danyen mai nau'in Brent ya haura dala 90 kan ganga guda kafin ya ja da baya yayin da Iran ta rage tasirin lamarin.

    Farashin zinare kuma ya kai kusan dala 2,400 a kan kowane ma'auni guda ɗaya.

    Akwai fargabar ɓarkewar rikici a Gabas ta Tsakiya na iya kawo cikas ga samar da mai.

    Masu zuba jari suna zuba ido sosai kan matakin da Isra'ila ta ɗauka game da harin da Iran ta kai mata da jirage marasa matuka da makamai masu linzami a ƙarshen makon da ya gabata.

    Farashin mai ya tashi da kusan kaso 3.5 da farko amma kuma ya faɗi daga baya zuwa dala 87 kan ganga guda daga dala 90 bayan da kafar yaɗa labaran Iran ta yi ikirarin cewa babu ɓarna a lardin Isfahan inda aka samu rahotannin fashewar abubuwa.

    Ci gaban tashin farashin mai na haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

    Ƙasashe sun dogara kacokan kan kayayyakin da ake amfani da su wajen samar da mai kamar man fetur da dizal.

    Farashin man fetur da makamashi sun kasance babban abin da ke haifar da tsadar rayuwa a duniya a cikin shekaru biyu da suka gabata.

    Randeep Somel, manajan asusu a M&G Investment Management a tattaunawarsa da BBC ya nuna damuwarsa game da hauhawar farashin kayayyaki, musamman yadda hauhawar farashin kayayyaki na Burtaniya ya kasance sama da abin da Bankin Ingila ke son cimma na kashi 2 cikin 100.

    "A Burtaniya, hauhawar farashin kayayyaki har yanzu yana kusa da kaso 3.2 inda har yanzu ba a kai ga cimma burin ƙasar ba - kuma ya zama abin damuwa ga masu tsara manufofi," in ji Mista Somel

    Farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabo zuwa dala 125 a cikin wannan lokacin, wanda ya haifar da tsawaita wahalhalun kudi ga masu sayen kayayyaki.

  12. Hukumomi sun tabbatar da mutuwar mutum 23 a harin Birnin Gwari

    ..

    Al’ummar Anguwar Danko da ke ƙaramar hukumar Birnin gwari a Jihar Kaduna na cikin zaman zullumi da tashin hankali sakamakon kashe muum 23 da 'yan bindiga suka yi.

    Yan bindiga da dama ne suka kai hari a ƙauyen a ranar Laraba, inda suka yi ta harbin mai uwa da wabi, tare da yin awon gaba da wasu mazauna kauyen.

    BBC ta tuntuɓi kantoman ƙaramar hukumar Birnin Gwari, Hon Salisu Isah inda ya ce ɓarayin dajin sun harbe mutum 22 yayin da ɗayan kuma da harin ya rutsa da shi ya mutu nan take.

    Ya kuma ce wasu biyar da lamarin ya shafe su waɗanda suke jinya a asibiti.

    Ga ƙarin bayanin da ya yi wa BBC.

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraron tattaunawar
  13. Senegal ta saki ƙarin fursunonin siyasa

    Mahukunta a ƙasar Senegal sun saki “ƙarin wasu fursunonin siyasa da dama” a karkashin dokar afuwa da majalisar dokokin ƙasar ta kafa a watan Maris, kuma tsohon shugaban kasar Macky Sall ya sanya wa hannu, kamar yadda kafar yada labarai ta Press Afrik ta ruwaito.

    Sai dai rahoton bai bayar da cikakken bayani kan adadin waɗanda aka sako ba.

    A cikin watan Fabrairu, ministan shari'a na lokacin Aissata Tall Sall ya ce an sako mutum 344 cikin 'yan kwanaki a wani yunƙuri na kwantar da hankula a siyasar ƙasar gabanin sake zaɓen shugaban ƙasar da aka yi cikin gaggawa a ranar 24 ga Maris.

    Shugaban ƙasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya kasance wanda ya ci gajiyar dokar afuwa.

    Ya lashe zaben shugabancin ƙasar ne kwanaki 10 kacal bayan an sako shi daga gidan yari.

  14. Yan sanda sun kama ƴan jagaliya takwas a Kano

    ..

    Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke mutum takwas da ake zargi da yunƙurin kawo tarnaƙi a bikin ƙaddamar da sabbin kwamishinoni da aka yi a baya-bayan nan.

    Kakakin rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na fesbuk, ya ce an kama mutanen ne da ke bayyana kansu a matsayin magoya bayan ɗaya daga cikin ƴan siyasa da ke neman barazana ga doka da oda.

    Kwamishinan ƴan sanda CP Usaini Gumel ya gargarɗi ƴan jagaliya da masu tallafa masu da su guji tayar da zaune tsaye inda ya ce "za a kama duk wani da ke son haifar da barazana ga tsaro da zaman lafiya a wurin da ake gudanar da tarukan gwamnati, sannan zai fuskanci hukuncin abin da ya aikata."

    Sanarwar ta ce mutanen da aka kama a yanzu na sashen binciken manyan laifuka inda ake gudanar da bincike mai zurfi domin hukunta su bisa tanadin doka.

    Rundunar ta ce ta ɗauki matakin ne domin tabbatar wa al'ummar jihar cewa ana ɗaukan matakan da suka dace na hana duk wani abu da zai kawo hargitsi da barazanar tsaro a sassan jihar Kano.

  15. Kotu ta yi watsi da tuhumar da ake yi wa Adoke kan halasta kuɗin haram

    Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya a Abuja ya yi fatali da tuhumar halasta kuɗin haram da hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa take yi wa tsohon atoni janar na Najeriya, Mohammed Adoke.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa da yake yanke hukunci kan ƙarar da tsohon babban jami'in ya shigar ta neman a soke ƙarar, alƙali Ekwo ya ce EFCC ta gaza gabata da shaida kan Adoke.

    EFCC ta tuhumi Adoke da Abubakar Aliyu, wani mai harkar gine-gine a 2017, da almundahana da naira miliyan 300.

    Alƙali Ekwo ya kori ƙarar tare da wanke shi.

    Sai dai Ekwo ya yanke cewa Aliyu Abubakar, mutum na biyu da ake ƙara, dole ya nemi shaida saboda akwai zarge-zargen da ya kamata ya kare kansa.

  16. Sabon jirgin ƙasan Ghana ya yi haɗari yayin gwajin ingancinsa

    ..

    Wani jirgin ƙasa da Ghana ta siya a baya-bayan nan daga Poland ya yi taho mu gama da wata babbar mota a lokacin da ake gwajinsa a gabashin ƙasar, kamar yadda hukumomi suka ce.

    Jirgin ya afka kan motar da aka ajiye kan layin jirgin na Tema-Mpakadan ranar Alhamis, abin da ya yi lalata gaban jirgin, in ji ma'aikatar kula da harkokin jiragen ƙasa.

    Babu wanda ya jikkata cikin direban jirgin da masu sa ido kan layin dogo da kuma fasinjojin.

    Babu kowa a cikin motar lokacin da hadarin ya faru sannan inda aka ajiye motar ba a yi masa alamar mahada ba, kamar yadda sanarwar ma'aikatar ta shaida.

    Ministan harkokin jiragen ƙasa John Peter Amewu ya bayyana lamarin a shafinsa na fesbuk a matsayin abin takaici da kuma rashin kishin ƙasa.

    Binciken farko da aka yi ya nuna direban da ake zargi ya bar motar babu kowa ciki kan layin dogo, abin da ya janyo suka yi taho mu gama da jirgin, kamar yadda sanarwar da rundunar ƴan sandan ƙasar ta fitar.

  17. Jama'a na tafiyar da harkokinsu a birnin Tehran duk da harin Isra'ila a Iran

    Kafofin yaɗa labaran Iran da jami'ai sun rage kaifin rahotannin wani hari da aka kai kan wurare daban-daban a birnin Isfahan da Tabriz.

    Hossein Dalirian, kakakin hukumar kula da sararin samaniyar Iran, a shafinsa na X ya ƙaryata labarin harbo makami mai linzami kai tsaye daga wajen ƙasar abin da ya sha banbam da bayanan jami'an Amurka cewa makami mai linzami na Isra'ila ya kai hari kan Iran.

    ..
    Image caption: Mutane na tafiya kan titunan Tehran, babban birnin Iran da safiyar yau
    ..
    Image caption: Wani mutum ke nan yake ciyar da tattabaru a gaban wani ɓutunɓutumi a Tehran
    ..
    Image caption: Mutane da direbobi na harkokinsu a birnin
  18. Amurka ba ta da hannu a hare-haren da aka kai Iran - Blinken

    ..

    A lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jaridu, sakataren harkokin tsaron Amurka, Anthony Blinken a taron ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziki na duniya, ya shaida wa 'yar jaridar BBC, Jessica Parker cewa Amurka ba ta da hannu a hare-haren da Isra'ila ta kai wa kasar Iran a daren Juma'a.

    Sai dai kuma ya ce sun ƙudirin niyyar bai wa Isra'ilar duk wata kariya da take buƙata "kamar yadda kuka gani a baya-bayan nan."

  19. 'Iran ba ta da burin kai harin ramuwar gayya nan take'

    Wani babban jami'in Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "Iran ba ta da wani shirin kai ramuwar gayya nan take kan Isra'ila" sa'oi bayan da wani hari kan birnin Isfahan da aka ruwaito cewa Isra'ila ta kai.

    Jami'an gwamnatin Amurka biyu sun shaida wa kafofin yaɗa labarai cewa harin daga Isra'ila ne amma Isra'ila ba ta ɗauki nauyinsa ba.

    "Majiyar lamarin ba ta tabbatar da harin ba. Ba mu ga wani hari daga waje ba kuma tattaunawa ta fi karkata ga kutse fiye da hari," in ji jami'in Iran da ya nemi a ɓoye sunansa.

    Tun farko, wani mai sharhi kan al'amuran Iran ya faɗa wa gidan Talabijin na Iran cewa "an tura ƙananan jirage marasa matuƙa a Isfahan da aka daƙile su", tare da rage kaifin rahotannin cewa Isra'ila ce ta kai hari.

  20. Fitattun ƴan fim a Tamil Nadu sun fita kaɗa ƙuri'a

    Yayin da al'umma a Indiya suke ci gaba da kaɗa ƙuri'a a babban zaɓen ƙasar, suma fitattun mutane kamar ƴan fim ba a bar su a baya ba.

    Ga hotunan wasu shahararrun masu fina-finai a Indiya da suka kaɗa ƙuri'arsu.

    ..
    Image caption: Ɗan fim da ya rikiɗe ya shiga siyasa Kamal Haasan, da ake kira 'jarumin duniya' ya kaɗa ƙuri'arsa
    ..
    Image caption: Trisha Krishnan fitacciyar ƴar fim ce da ta yi fina-finai da dama
    ..
    Image caption: Dhanush ɗan fim ne da ya yi suna ga mutanen da ke wajen Tamil Nadu
    ..
    Image caption: Ajith Kumar ɗaya ne cikin manyan ƴan fim da ake ganin fina-finansu a gidajen kallo