Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Umar Mikail da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. 'Za a shafe shekara fiye da 30 kafin kwashe ɓaraguzan da yaƙin Isra'ila ya haifar a Gaza'

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa za a kwashe sama da shekara 10 kafin a kammala kwashe ɓaraguzan da yaƙin Isra'ila ya haifar a Gaza.

    Wani jami'in Majalisar, Pehr Lodhammar ya ce akwai tan miliyan 37 na tarkacen ɓaraguzan, cikin har da bama-baman da ba su fashe ba.

    Ya ce manyan motoci 100 za su yi kimanin shekara 14, kafin su kammala kwashe tarkacen.

    Hare-haren na Isra'ila sun ruguza yawancin gine-gine a yankin, kamar yadda hotunan tauraron ɗan'adam suka nuna.

    Jami'an kiwon lafiya na Hamas sun ce a yanzu sama da mutum 34,000 ne aka kashe a harin da Isra'ila ta ƙaddamar bayan harin da Hamas ta kai mata a ranar bakwai ga watan Oktoba.

  3. Tinubu ya isa Saudiyya don halartar taron Tatalin Arziki na Duniya

    .

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Riyadh na Saudiyya don halartar taron Tattalin Arziki na Musamman na Duniya da za agudanar a ƙasar.

    Taron zai mayar da hankali wajen haɗin kai don bunƙasa samar da makamashi a duniya.

    Shugabannin gwamnatoci da na cibiyoyin kasuwanci da masana fiye da 1,000 ne daga ƙasashe 90 ake sa ran za su halarci taron da za a gudanar a birnin Riyadh.

    Manufar taron ita ce ɗora wa kan nasarorin da ka cimma a taron shekarar da ta gabata da aka gudanar birnin Geneva na ƙasar Switzerland.

    Mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya ce ya ce shugaba Tinubu zai yi amfani da taron wajen ƙarfafa manufofin gwamnatinsa da ake yi wa laƙabi da "Renewed Hope Agenda".

    Tun da farko shugaba Tinubu na ziyarar aiki a birnin Hague na ƙasar Netherlands, bisa gayyatar da firaminstan ƙasar ya yi masa don wata tattauna hanyoyin zuba jari tsakanin ƙasashen biyu.

  4. MDD ta rufe binciken zargin da Isra'ila ta yi wa jami'anta na hannu a harin da Hamas ta kai mata

    Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya da ke nazarin zargin da Isra'ila ta yi na cewa jami’an hukumar kula da ƴan gudun hijirar Falasɗinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, 12 na da hannu a harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, sun rufe bincike kan ƙara guda ɗaya tare da dakatar da wasu uku.

    Wani mai magana da yawun majalisar, Stephane Dujarric ya ce a binciken da aka rufe, Isra'ila ba ta bayar da wata hujja da za ta tabbatar da zargin da ake yi wa ma'aikacin hukumar ba.

    Mista Dujarric ya ce an dakatar da wasu ƙararraki uku saboda bayanan da Isra'ila ta bayar ba su gamsar ba.

    Ya ce ana ci gaba da bincike kan sauran ƙararraki takwas da suka rage, da kuma wasu ƙararraki bakwai da Isra'ila ta gabatar daga baya

  5. Za mu ɗauki mataki kan China kan tallafa wa Rasha a yaƙin Ukraine - Blinken

    ..

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya shaida wa BBC cewa, a shirye Amurka take ta ɗauki matakai kan China idan har ta ci gaba da bai wa Rasha kayayyakin da take amfani da su wajen yaƙin da take yi a Ukraine.

    Da yake jawabi bayan tattaunawa da shugaba Xi Jinping, Mista Blinken ya ce, ya bayyana ƙarara cewa, China na taimakawa wajen ƙara rura wutar babbar barazana da tsaron Turai ke fuskanta tun bayan kawo ƙarshen yaƙin cacar baka.

    Mista Blinken ya ce China ce ke samar da kashi 70 cikin dari na injuna da kuma, kashi 90 cikin dari na na'urorin lantarki da Rasha ke samu daga ƙasashen ƙetare.

    Sakataren wajen na Amurka bai bayyana matakan da Amurka ke shirin ɗauka kan Chinar ba.

  6. Tinubu ya naɗa shugaban asusun bai wa ɗalibai bashin karatu

    .

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin Jim Ovia, CFR a matsayin shugaban asusun bai wa ɗalibai bashin karatu.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce yana da yaƙinin mista Ovia zai yi amfani da ƙwarewarsa ta aiki wajen ganin ɗaliban ƙasar sun samu damar faɗaɗa karatu ta hanyar samun bashi daga shirin da gwamnatinsa ta ɓullo da shi.

    Mista Ovia - wanda fitaccen ma'aikacin banki ne, kuma ɗan kasuwa - na da digiri na biyu a fannin kasuwanci daga kwalejin kasuwanci ta Harvard da ke Amurka.

    Bai wa ɗalibai bashin karatu wani shiri ne da gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shi, don bai wa ɗalibai damar yin karatu a manyan makarantun ƙasar tare da samun cikakkiyar ƙwarewa, musamman tsakanin matasan ƙasar.

    Shugaba Tinubu ya yi fatan cewa mista Ovia zai gudanar da ayyukansa don tabbatar da cewa ɗaliban ƙasar sun samu ƙwarewar da suke buƙata, a duka fannonin ilimi.

    A shekarar da ta gabata ne gwamnatin ƙasar ta ɓullo da shirin kafa asusun bai wa ɗaliban ƙasar bashi don ci gaba da karatunsu, a wani mataki na sauƙaƙa wa ɗalibai raɗaɗin ƙarin kuɗin makaranta da jami'o'in ƙasar suka yi.

  7. Ɗan Ghana ya kafa tarihin rungumar bishiyoyi a duniya

    ..

    Wani ɗalibi ɗan gwagwarmayar kare muhalli da gandun daji a Ghana ya kafa tarihin rungumar bishiyoyi masu yawa cikin sa'a ɗaya.

    Kundin Adana Kayan Tarihi na Guinness ya wallafa a shafinsa cewa Abubakar Tahiru, mai shekara 29 ya rungumi bishiyoyi 1,123 cikin sa'a guda.

    Abubakar ya taso ne a garin Tepa da ke albarkatun noma a Ghana, inda ya samu sha'awar abubuwan da suka shafi gandun daji da yanayi.

    Bayan kammala karatunsa na digirin farko a fannin gandun daji a ɗaya daga cikin manyan jami'o'in Ghana, Abubakar ya ci gaba da karatu a fannin gandun daji a jami'ar Auburn da ke jihar Alabama da ke Amurka a shekarar da ta gabata.

    Ya kafa tarihin ne a gandun dajin Tuskegee, ɗaya daga cikin manyan gandun daji mai albarkatun bishiyoyin timber da ake katako da ita, a jihar ta Alabama.

    Yadda yake rungumar bishiyoyin shi ne yakan rungume duka hannayensa a jikin bishiyar, kuma babu bishiyar da ya runguma fiye da sau ɗaya, kuma babu wata illa za dai yi wa bishiyar sakamakon rungumar.

    .
  8. Jirgin Air Peace ya yi saukar gaggawa a Legas

    ..

    Wani jirgin saman kamfanin Air Peace da ya taso daga birnin Fatakwal zuwa Legas ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.

    Cikin wata sanarwa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis.

    “Muna sanar da al'umma lamarin da ya faru da jirginmu da ya taso daga birnin Fatakwal zuwa Legas ranar 25 ga watan Afrilu''.

    “Mintuna kafin saukar, sai matuƙin jirgin ya fahimci wata alamar ƙarar gargaɗin wuta a inda direban ke zama. Direban ya yi ƙoƙarin ɗaukar duka matakan kariya, kodayake daga baya ƙarar ta daina''.

    Sanarwar ta ƙara da cewa “Direban ya yi gaggawar sanar da masu kula da filin jirgin na Legas, inda bayan saukar jirgin aka gano cewa ƙarar ta fara kaɗawa ne bisa kuskure, amma babu wata wuta da kama a jirgin''.

    Jirgin - wanda ke ɗauke da fasinjoji 243 tare da ma'aikatan jirgin 12 - ya sauka lafiya ba tare da wata matsala ba.

    Batun na zuwe ne kwanaki bayan jirgin kamfanin Dana Air ya zame daga kan hanyarsa a filin jirgin saman Legas, lamarin da ya sa gwamnatin ƙasar da dakatar da kamfanin daga aiki, tare da ƙaddamar da bincike kan batun.

    Saukar gaggawa da zamewar jirage daga kan titunansu dai wasu abubuwa ne da suka jima suna sanya fargaba a zukatan fasinjoji a Najeriya.

  9. Muhuyi Magaji ya yi ƙarin bayani kan janye musu 'yansanda a Kano

    Hukumar yaki da cin hanci da karɓar korafe-korafe ta jihar Kano ta yi karin haske game da janye jami'an ƴan sandan da suke aiki a hukumar.

    Hukumar ta ce kawo yanzu rundunar ƴan sandan Kano ta mayar da jami'an bayan aikin tantance ƴan sandan a hedkwatarsu wanda ake cewa dama an saba yi duk shekara.

    Rundunar ƴan sanda Kano ta fitar da sanarwa inda suka tabbatar da janye jami'an amma ta ce ba wai janye su aka yi ba, illa dai tantance su game da aikin da suke yi a hukumar.

    Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado shi ne shugaban hukumar kuma ya yi wa Zahraddeen Lawan karin bayani kan abin da ya faru:

    Video content

    Video caption: Dannan hoton domin sauraron hirar
  10. MDD ta damu kan dakatar da BBC da VOA a Burkina Faso

    Ofishin kare haƙƙi na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce "ya damu" game da umarnin da hukumomin Burkina Faso suka bayar na dakatar da shirye-shiryen BBC da na VOA a ƙasar.

    Kamar yadda muka ruwaito ɗazu, hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Burkina ta dakatar da kafofin biyu tsawon mako biyu bayan sun ba da rahoton binciken ƙungiyar kare ta Human Rights Watch da ya zargi rundunar sojin ƙasar da kashe fararen hula.

    Mai magana da yawun ofishin, Marta Hurtado, ta faɗa cikin wata sanarwa cewa: "Dole a dakatar da take 'yancin yaɗa labarai nan take.

    "'Yancin faɗar albarkacin baki da na samun labarai na da muhimmanci a kowace al'umma, har a Burkina Faso."

  11. 'Ana iya yin shekara 14 kafin kwashe ɗumbin ɓaraguzan da yaƙi ya bari a Gaza'

    ..

    Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai dauki shekara goma sha hudu kafin a iya kwashe dumbin baraguzan da suka hada da bama-bamen da ba su fashe ba, da ke jibge a Gaza sakamakon yakinta da Isra’ila.

    Pehr Lodhammar - daga Hukumar Kula da Ma'adanai ta Majalisar Dinkin Duniya - ya ce ana bukatar a kwashe tarkacen da yawansu ya kai tan miliyan talatin da bakwai.

    Mista Lodhammar ya ce ba za a iya kiyasta adadin bama-bamen da basu fashe ba wanda ke binne a cikin baraguzan.

    Ya ce Ba zai yiwu a yi hasashe ba, amma abin da zan iya cewa shi ne, akalla kashi goma cikin dari na bama-baman da ake harbawa, na iya kin fashewa.

  12. Yadda ƴan bindiga suka sace aƙalla mutum 50 a Zamfara

    Wasu ƴan bindiga a jihar Zmfara sun yi garkuwa da mutum aƙalla 50 a ƙaramar hukumar Maradun bayan wani hari da suka kai da tsakad dare.

    Wasu maharan kuma sun kashe aƙalla mutum ɗaya da raunata ƙarin mutum biyu.

    Haka nan ƴan bindigar sun kai wani hari makamancin wannan a masarautar Zurmi inda suka kashe aƙalla mutum uku tare da sace wasu da dama.

    Ga ƙarin bayani a rahoton Zubairu Ahmad.

    Video content

    Video caption: Danna hoton don jin rahoton
  13. Kenya na shirin ko ta kwana yayin da ambaliya ta halaka mutum 60

    ..

    Mummunar ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita dubban mutane a sassan gabashin Afirka - sannan a Kenya masu aikin ceto da hukumomi sun yi shirin ko ta kwana.

    "Lamarin na ci gaba da haifar da fargaba. Zuwa daren jiya, mun bayar da rahoton mutuwar fiye da mutum 60 a sassan ƙasar," in ji Sanata Edwin Sifuna, mai wakiltar lardin Nairobi da ambaliyar ta fi shafa.

    Mamakon ruwan sama da aka alaƙanta da yanayin El Nino ne ya haifar da ambaliyar ruwan.

    "Idan na duba waje ta taga, ina iya ganin hadari ya haɗu. Masana yanayi sun faɗa mana mu tsammaci ruwa mai ƙarfi cikin sama da sa'a 72," in ji Sifuna inda tawagar masu ceto suka ƙiyasta cewa kimanin mutum 100,000 ne aka ɗaiɗaita.

    Micheal Aiyabei, shugaban hukumar da ke sa ido kan afkuwar haɗari, ya nuna damuwarsa ga lamarin.

    Kimanin mutum 155 ne suka mutu a Tanzaniya mai maƙwabtaka. A Burundi kuma kusan mutum 100,000 sun rasa muhallansu.

  14. Whatsapp ya yi barazanar ficewa daga Indiya

    ..

    Kamfanin sadarwa na WhatsApp, ya yi barazanar ficewa daga Indiya idan har aka tilasta masa cire matakan sirranta hira tsakanin masu amfani da dandalin.

    Lauyan kamfanin ya shaida wa wata kotu a Delhi cewa matakan da WhatsApp ke dauka na kare bayanan sirrin masu amfani da manhajar ne.

    Kamfanin ya mayar da martani ne yayin da yake kalubalantar bukatar hukumomin Indiya na bin diddigin hirar da ake yi a manhajar da niyyar gano inda labarai ke fitowa.

    Gwamnati ta ce tana bukatar yin hakan ne domin a bi diddigin labaran karya da kuma bayanan da za su tayar da hankali da ake yadawa a shafukan sada zumunta wadanda ka iya jawo tashin hankali.

    Indiya ita ce kasuwar WhatsApp mafi girma a duniya, inda kimanin mutane miliyan dari biyar ke amfani da manhajar.

  15. An dakatar da kafafen yaɗa labaran BBC da VOA a Burkina Faso

    Hukumar da ke sa ido kan kafafen yaɗa labarai a Burkina Faso ta ƙaƙaba dakatarwar mako biyu kan kafar yaɗa labarai na BBC Afrique da Muryar Amurka (VOA) saboda yaɗa rahoton da ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta fitar da ke zargin sojojin ƙasar da cin zarafin farar hula.

    Kazalila, hukumar ta dakatar da shafukan intanet na kafofin yaɗa labaran da ƙungiyar Human Rights a cikin ƙasar.

    Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ruwaito cewa "An umarci BBC da VOA ta hannun wakilansu a Burkina Faso da su gaggauta daina watsa shirye-shirye a dukkanin kafofinsu,"

    Hukumar kula da harkokin sadarwa ta sake gargaɗin kafafen yaɗa labarai a ƙasar da su kaucewa yaɗa labarin inda ta yi barazanar ƙaƙaba wa waɗanda suka bijire takunkumi.

    A ranar Alhamis ne ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi sojojin Burkina Faso da kashe farar hula aƙalla 223 a arewacin ƙasar ranar 25 ga watan Fabarairu.

    A Disamban 2023 ne Burkina Faso ta dakatar da jaridar French daily Le Monde kan zargin nuna son kai a rahotannin da suke yaɗawa.

  16. Gini mai hawa biyu ya rufta kan magina fiye da 15 a Kano

    Ana fargabar wani gini mai hawa biyu da ya ruguje ya faɗa kan wasu magina da ake aikin gini a yankin Kuntau da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

    Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa ginin ya rufta kan magina fiye da 15.

    Tuni dai masu aikin ceto suka fara zaƙulo mutanen da suka maƙale a ginin.

    Zuwa lokacin da BBC ta yi magana da majiyarta, an zaƙulo mutum uku sai dai ɗaya a cikinsu ya mutu yayin da biyun ke cikin mawuyacin hali.

    Kawo yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da ibtila'in ya rutsa da su ba.

  17. Jaririyar da aka ciro daga cikin mahaifiyarta bayan mutuwarta ta rasu

    ..

    Jaririyar da aka ciro daga cikin mahaifiyarta bayan ta mutu a harin da Isra'ila ta kai kudancin Gaza ta mutu, kamar yadda BBC ta samu labarin.

    An ciro jaririya Sabreen al-Sakani bayan yi wa mahaifiyar tiyata a asibitin Rafah a ranar Lahadi.

    Likitoci sun yi nasarar ceto rayuwarta ta hanyar tattaɓa ta domin ta yi numfashi.

    Sai dai Sabreen ta mutu ranar Alhamis kuma an binne ta kusa da kabarin mahaifiyarta da ta gaji sunanta.

    Jaririya Sabreen na cikin yara 16 da aka kashe sanadin hare-haren da aka kai Rafah a ƙarshen makon da ya wuce. Dukkansu sun mutu a lugudan wutar da aka kai kan wani rukunin gida da suke zama.

    Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce sun kai harin ne kan mayaƙan Hamas da gine-ginensu.

    Mahaifiyar Sabreen na ɗauke da cikin wata bakwai da rabi lokacin da Isra'ila ta kai hari a gidan iyalin al-Sakani a ranar Asabar yayin da ita da mijinta Shukri da ƴarsu mai shekara uku, Malak ke barci.

    Sabreen ta gamu da munanan raunuka kuma an kashe mijinta da Malak sai dai jaririyar na da rai a cikin uwarta lokacin da ma'aikatan ceto suka isa wurin.

    Sun gaggauta kai Sabreen asibiti inda likitoci suka yi mata tiyata aka kuma ciro jaririyar.

  18. 'Mun janye wa Muhuyi ƴansanda ne saboda aikin tantance su da muke yi'

    ..

    Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta yi ƙarin haske game da janye jami'an ƴan sandan da ke samarwa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano tsaro inda ta ce an ɗauki matakin ne saboda za a yi aikin tantance yawan ƴan sandan da ke ƙarƙashin hukumar da kuma fahimtar yanayin ayyukansu tun 2015 da aka tura su yin aiki a hukumar.

    Bayanin na ƙunshe cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar inda ta ce za a tantance su ne bayan rahotannin da aka samu ta hannun sashen karɓar ƙorafe-ƙorafe na rundunar da ke nuna cewa ana amfani da ƴan sandan da ke aikin samar da tsaro a hukumar wajen cimma wasu ƙudurori da ba aikinsu ba.

    Sanarwar ta ce akwai buƙatar mutane su fahimci cewa ana tantance ma'aikatan domin martani ga rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke watsawa.

    Matakin, a cewar sanarwar, ya zama wajibi domin gyara matsalolin da aka gano game da yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta ganin cewa ana amfani da ƴan sandan da aka tura su samar da tsaro wajen yin kame da gudanar da bincike kan ƙararraki, wanda ƙarara ya nuna cewa sun sauka daga tsarin gudanar da aikin da ya rataya a wuyansu - wani abu da ya zama dole a yi gyara a kai.

    Rundunar ta ce a baya ma an gudanar da irin wannan aikin tantance ƴan sandan daga lokacin da aka kafa hukumar a 2015 kuma ƴan sandan suka koma bakin aiki bayan kammala aikin.

    Sanarwar ta ce babban sufeton ƴan sanda ya umarci ƴan sandan da aka gama tantancewa su gagauta komawa bakin aiki.

    Kazalika rundunar ta ce idan har hukumar na son ƙarin jami'an ƴan sanda da za su yi mata wasu ayyukan da ba sa cikin waɗanda babban sufeton ya amince, hukumar na iya neman izini daga shugaban ƴan sandan.

  19. Amurka za ta janye sojojinta daga Chadi na ɗan lokaci

    ..

    Amurka za ta janye wasu daga cikin dakarunta daga Chadi na wani ɗan lokaci, kwanaki bayan da ta amince ta janye duka dakarunta daga Nijar mai maƙwabtaka.

    Sakataren yaɗa labarai na ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon, Manjo Janar Pat Ryder ya ce Amurka za ta sakewa wasu daga cikin sojojin wuri daga Chadi amma bai ce suwa ne waɗanda matakin zai shafa ba ko kuma inda za a kai su.

    "Wannan mataki ne na wucen gadi a yunƙurin sake nazari kan haɗin gwiwar tsaro da za a ci gaba da yinta bayan zaɓen shugaban ƙasar Chadi na ranar 6 ga watan Mayu." kamar yadda ya bayyana.

    Sanarwar ta zo ne bayan da shugaban hafsan sojin saman Chadi, a farkon watan nan, ya umarci Amurka ta dakatar da ayyukanta a sansanin sojin sama da ke N'Djamena, babban birnin Chadi, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Gen Ryder ya kuma ce an soma tattaunawa da sojojin da ke mulki a Nijar da majalisar tabbatar da tsaron ƙasa CNSP ranar Laraba domin tabbatar da janye sojojin Amurka daga ƙasar cikin lumana.

    Amurka ta dogara kan Nijar a matsayin babbar sansaninta ta bibiyar ayyukan ƴan ta'adda a yankin Sahel.

    Sai dai sojojin Nijar da ke mulkin ƙasar tun Yuli, sun kawo ƙarshen yarjejeniyar tsaro da ƙasar tare da korar sojojin Faransa, wani yunƙuri na yanke alaƙa da ƙasashen yamma.