Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Sai da safenku

    Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafin.

    Mu haɗu da ku gobe da safe don kawo wasu sababbi.

    Umar Mikail ne ke muku fatan alheri.

  2. Yaƙin Gaza: Hankali ya karkata kan Hamas game da yarjejeniyar tsagaita wuta

    Gaza

    Ana kara masta wa kungiyar Hamas lamba kan ta amince da abin da Amurka ta bayyana a matsayin "abin alheri" da Isra’ila ta yi dangane da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin gaza.

    An ba da rahoton cewa wani jami'in Hamas ya ce ƙungiyar ba ta da "wata babbar matsala" da abubuwan da ke kunshe a sabuwar yarjejeniyar.

    Sakateren Harkonin Wajen Amurka Anthony Blinken ya yi kira ga Hamas da ta yanke shawarar da ta dace.

    "Dole ne su yanke shawara kuma su yanke shawara cikin hanzari," in ji shi. "Hakan dai muke sa rai kuma muna sa ran za su yanke shawarar da ta dace."

  3. Amurka ta ce bataliya biyar na sojin Isra'ila sun take haƙƙin Falasɗinawa

    Sojojin Israila

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana cewa rukunin sojojin Isra'ila biyar na da alhakin take haƙƙin dan'adam.

    Hukuncin ya shafi al'amuran da suka faru a wajen Gaza kafin a fara yaƙi a watan Oktoba.

    Ta ce hudu daga cikin rukunnen sun yi maganin cin zarafi yadda ya kamata, yayin da Isra'ila ta gabatar da ƙarin bayani game da runkiuni na biyar.

    Amurka na ci gaba da tattauna batun da gwamnatin Isra'ila.

  4. Wahalar man fetur: 'Da kuɗinmu ma mun rasa mai tsadar'

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

    Yayin da ƴan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan wahalar man fetur da tashin farashinsa cikin ƴan kwanakin nan, su kuwa 'yan bumburutu kasuwarsu ce ta buɗe.

    Farashin kowace lita ta man ta kai kusan N800 a gidajen mai na Abuja, su kuwa 'yan bumburutu kan sayar da shi har N1,100.

    Lamarin ya zarta haka a sauran jihohin ƙasar.

    Wasu mazauna birnin Kano a arewacin ƙasar sun ce yanzu mai tsadar ma suke nema da kuɗinsu amma sun rasa saboda akasarin gidajen man a kulle suke.

  5. 'Yansandan jihar Rivers sun kama mutum 16 da zargin kisan 'yarsanda

    'Yansandan Najeriya

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Rivers ta ce ta kama mutum 16 da zargin kisan wata sufeton 'yarsanda a ƙaramar hukumar Khana da ke jihar.

    Lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Afrilu lokacin da 'yarsandan mai suna Christiana Erekere ke bakin aiki a ofishin 'yansanda na Bori.

    Wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar, Grace Iringe-Koko, ta ce wasu mutane ne da aka tare domin duba abin hawansu suka halaka jami'ar.

    "Bayan kammala duba abin hawan nasu ne aka nemi su tafi, amma sai suka ƙi kuma suka rufe titin gaba ɗaya, inda suka yi zargin cewa matar ta naɗi fuskokinsu a waya," in ji sanarwar.

    "Bayan yunƙurinsu na ƙwace wayar daga hannunta ya gaza, sai suka kai mata hari inda suka jefe ta da duwatsu. Dukan da suka yi mata ya sa sufeton ta sume kuma ta rasu bayan kai ta asibiti."

    Ta ƙara da cewa tuni rundunar 'yansandan jihar ta miƙa ta'aziyyarta ga iyalin sufeton da kuma abokan aikinta.

  6. Muna sa ran Hamas za ta amince da tayin yarjejeniyar tsagaita wuta - Amurka

    Antony Blinken

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce yana sa rana ƙungiyar Hamas za ta amince da tayin da Isra’ila ta yi mata na tsagaita wuta a zirin Gaza.

    Mista Blinken, wanda ke halartar tattaunawa da takwarorinsa na yankin a Saudiyya, yana magana ne kan tawagar Hamas da za ta halarci wata tattaunawar tsagaita wutan a Masar.

    Wakilin BBC ya ce akwai abubuwa a cikin tsarin da Mista Blinken ya ce sun cika wasu sharuɗɗan da Hamas ta gindaya, kamar barin mutane su koma gidajensu a wasu yankunan arewacin Gaza da kuma janye sojojin Isra’ila daga wasu ɓangarorin zirin.

    Mista Blinken ya sake jaddada rashin amincewar Amurka da harin da Isra'ila ke shirin kai wa birnin Rafah - yana mai cewa bai ga wani shiri da zai kare fararen hula a yankin ba.

    Mutum20 ne suka mutu a wasu hare-haren da Isra'ila ta kai cikin dare.

  7. 'Yansandan Kano sun kama 'riƙaƙƙen dillalin ƙwaya' Badoo

    ..

    Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wani riƙaƙƙen "dillalin ƙwaya" da ta daɗe tana nema ruwa a jallo tare da wasu mutum takwas.

    Wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya fitar a yau Litinin ta ce sun yi nasarar kama Sadam Mu'azu, wanda aka fi sani da Badoo, ne bayan ƙorafe-ƙorafen da mazauna unguwar Takuntawa suka kai mata.

    "An yi nasarar kama shi ne sakamakon bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da mazauna yankin wanda rundunar Anti-Daba ta jagoranta,," in ji sanarwar.

    Ta ƙara da cewa dakaru sun kama ƙarin mutum takwas daga cikin 'yan tawagar matashin mai shekara 33, "waɗanda ke samun tabar wiwi daga kudancin ƙasar nan kuma yake rarraba wa mutane har da matan aure a gidaje".

    Haka nan, rundunar ta ce ta ƙwace ƙunshi 11 na abin da take zargin tabar wiwi ce, da gatari, da babura biyar da ake "amfani da su wajen rarraba kayan", da kuma kuɗi naira 111,500 da ga hannunsu.

    Za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike, a cewar rundunar.

    ..
    ..
    ..
    ..
    ..
    ..
  8. Shugaban Gwamnatin Scotland Humza Yousaf ya yi murabus

    Humza Yousaf

    Shugaban gwamnatin Scotland, Humza Yousaf, ya sanar da cewa zai yi murabus daga mukaminsa bayan wata 13 a kan mulki.

    Zai fuskanci kuri'u biyu na rashin ƙwarin gwiwa kan shugabancinsa cikin wannan makon bayan ya kawo ƙarshen ƙawance da jam'iyyar Scotland Green Party.

    Shugaban jam'iyyar ta Green Party, Patrick Harvie, ya ce Mista Yousaf ya sanya kansa cikin tsaka-mai-wuya.

    Ya ce: "Ba na tunanin akwai wani abu da Humza Yousaf zai iya cewa da zai wanke cin amanar da ya yi, kwana biyu kafin ya yi watsi da yarjejeniyar haɗin gwiwa, ya yi ikirarin cewa yana son a ci gaba da tafiya tare amma kwatsam ba tare da wani bayani ba sai ya sauya ra’ayinsa baki daya."

    Mista Yuosaf zai ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban jam'iyyar SNP mai mulki, kuma shugaban gwamnati, har sai an samu wanda zai maye gurbin sa.

  9. Gwamna Obaseki ya sanar da mafi ƙarancin albashin N70,000 ga ma'aikatan Edo

    ..

    Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya ƙara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati daga N30,000 zuwa N70,000 a jihar.

    Gwamna Obaseki ya bayyana haka ranar Litinin lokacin da yake ƙaddamar da ginin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar.

    A cewar gwamnan, sabon mafi ƙarancin albashin zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu.

    Matakin gwamnan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ƙwadagon ke matsa wa gwamnatin tarayya lamba don ta ƙara mafi ƙarancin albashin domin rage wa ma'aikata raɗaɗin hauhawar farashi.

    NLC da TUC sun nemi gwamnati ta mayar da mafi ƙanƙantar albashin ya zama N615,000.

    Tun a watan Janairu ne gwamnatin Bola Tinubu ta kafa kwamitin mutum 37 da ke da wakilci daga ɓangarori da dama - gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyar ƙwadago.

    Kwamitin zai tattauna domin tsayar da mafi ƙarancin albashin da zai gabatar wa gwamnati domin amincewarta.

    A lokacin ƙaddamar da kwamitin, mataimakin shugaban ƙasa, Kassim Shettima ya nemi kwamitin ya gaggauta wajen cimma matsaya, ya kuma miƙa rahotonsa da wuri.

    View more on twitter
  10. Kwamitin da aka kafa don bincikar gwamnatin Ganduje ya fara aiki

    ..

    Kwamitin bincike da gwamnatin Kano ta kafa domin binciken batun zargin wadaƙa da dukiyar al'umma ya fara zamansa na farko.

    Kwamitin zai yi bincike ne tsakanin 2015 da 2023, wato zamanin mulkin, Dr Abdullahi Umar Ganduje, inda ake fatan kwamitin zai karɓi ƙorafe-ƙorafe daga jama’a da kuma ‘yan ƙungiyoyi a kan yadda tsohon gwamnan ya yi tasarrufi da kadarorin gwamnati.

    A kwanakin baya ne gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamatocin bincike biyu da za su binciki zargin al’mundahana da rikicin siyasa da ɓatan mutane a jihar, al’amarin da ya haifar da zazzafar muhawara.

    Kwamitin binciken ƙarkashin jagorancin mai shari’a Faruk Lawan Adamu, ya ce al'umma suna da damar zuwa kwamitin, su gabatar da duk wani ƙorafi ko rashin gamsuwa da yadda aka tafiyar da gwamnatin jihar Kano daga 2015 zuwa 2023.

    Barista Bashir Sale mamba ne a kwamitin binciken kuma ya yi wa BBC ƙarin bayani game da farko da kwamitin ya yi.

    Ya ce "kadarorin gwamnati - makarantu da filaye da gidaje, maƙabartu da burtali, ya ya aka yi da su? An sayar? bisa ƙa'ida aka sayar? Idan ba bisa ƙa'ida aka sayar ba, wa ya siya, idan kuma ka siya, wa ka siyarwa?

    Ya kuma ce za su bi ƙa'ida da yin adalci a binciken da za su yi.

    Nan gaba ne kuma za a fara sauraron bahasi daga ɓangarori daban-daban ciki har da duk wanda yake ji an aiwatar da wani aiki a yankinsa da bai gamsu da shi ba.

    Akwai kuma kwamitin da zai yi bincike a kan rikice-riciken siyasa da mutanen da suka ɓata da tashin hankalin da aka yi a 2015 da 2019 da kuma 2023.

    Kafa wannan kwamatocin bincike dai ya haifar da ce-ce-ku-ce da kace-na-ce tsakanin ɓangaren tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma gwamnatin NNPP, inda bangaren Gandujen ke zargin akwai bita-da-ƙulli a binciken da ake ƙoƙarin yi, kasancewar an zaɓi tsohon gwamna ɗaya ne wajen yin binciken, zargin da gwamnatin kwankwasiyya ta musanta.

  11. Fiye da mutum 40 sun mutu bayan fashewar madatsar ruwa a Kenya

    ..

    Mutane da dama sun rasa rayukansu bayan fashewar wata madatsar ruwa a yankin Mai Mahiu da ke Kenya, kamar yadda ƙungiyar agaji ta Kenya Red Cross ta shaida wa BBC.

    Gwamna a yankin, Susan Kihika ma ta tabbatar da mutuwar mutanen ga kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Ruwa ya ɓalle inda ya tafi da gidaje da motoci da dama a ƙauyen Kamuchiri sakamakon mamakon ruwan sama da ake yi a yankuna da dama na ƙasar.

    Tawagar agaji na lalube cikin taɓo domin zaƙulo masu sauran numfashi, in ji kafafen yaɗa labaran ƙasar inda kuma suka yi gargaɗin adadin mutanen da suka mutu na iya ƙaruwa.

    Lamarin ya datse babban titin da ya tashi daga Nairobi zuwa Mai Mahu bayan da manya-manyan duwatsu da taɓo suka rufe hanyar.

    Tun farko, ƙungiyar agaji ta Kenya Red Cross ta ce ta kai mutane da dama zuwa asibiti a Mai Mahiu saboda ambaliya.

    Adadin mutanen da suka mutu a yanzu sakamakon mamakon ruwan sama da ambaliya a ƙasar tun watan da ya gabata sun zarce 100.

  12. An jinkirta buɗe makarantu a Kenya saboda ambaliyar ruwa

    ...

    Gwamnatin Kenya ta tsawaita lokacin buɗe makarantu da mako ɗaya saboda matsalar ambaliyar ruwa da ake fama da ita wadda kuma ta halaka fiye da mutum 80 zuwa yanzu.

    Ƙididdiga ta nuna cewa ambaliyar ta yi wa makarantu a sassan ƙasar gagarumar ɓarna, kamar yadda ministan ilimi, Ezekiel Machogu ya faɗa cikin wata sanarwa.

    "Mamakon ruwan sama ya yi ɓarna sosai a makarantu da zai iya zama haɗari idan ɗalibai da malamai suka koma karatu kafin a ɗauki ƙwararan matakan da suka dace," in ji ministan.

    Duka makarantun da aka tsara buɗe su domin fara zango na biyu yau Litinin, a yanzu za a buɗe su ranar 6 ga watan Mayu.

    Mutanen da suka ɗaiɗaita kuma suna amfani da wasu makarantun a matsayin mafaka.

    Zuwa ranar Asabar, adadin mutanen da aka tabbatar sun mutu sakamakon ambaliyar sun ƙaru zuwa 83 bayan da aka gano fiye da gawarwaki 13 a wurare daban-daban na ƙasar.

    Da yiwuwar adadin mutanen ya ƙaru yayin da ake ci gaba da yin ruwa kamar da bakin ƙwarya a ƙasar.

    Fiye da mutum 130,000 ne suka ɗaiɗaita sakamakon ambaliyar, in ji hukumomi inda aka ba da rahoton ɓatar mutane da dama.

    Kenya sa sauran ƙasashe a gabashin Afirka na fuskantar ƙalubale sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ake yi a makonnin baya-bayan nan.

    Kusan mutum 100,000 ne suka ɗaiɗaita a Burundi yayin da aƙalla 150 suka mutu a Tanzania.

  13. Ƙarin mayaƙan Boko Haram shida sun miƙa wuya ga dakarun MNJTF

    ..

    Rundunar dakarun ƙasashen da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram ta MNJTF ta ce ƙarin ƴan ta'adda shida sun sake miƙa wuya tare da ajiye makamansu.

    Jami'in yaɗa labarai na rundunar, leftena kanar, Abubakar Abdullahi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

    A cewar sanarwar, wani ɗan Boko Haram mai shekara 19 ya miƙa wuya ga sojojin runduna ta 403 da ke Monguno.

    Binciken farko, a cewar sanarwar ta nuna cewa matashin na da alaƙa ta kusan shekara uku da ɓangaren Buduma na Boko Haram.

    Ƙarin mayaƙa biyu - ɗan shekara 37 da 21 sun miƙa kansu a Blangua da ke Kamaru ga dakarun runduna ta ɗaya da ke yankin Darak a kudancin tafkin Chadi. Binciken da aka yi a kansu ya nuna ƴan asalin Chadi ne da ke zama a yankunan Kami-Wari da Kourea.

    Sai kuma wani ɗan shekara 38 da mai ɗakinsa da ƴaƴansu biyu - ɗan shekara 13 da jaririya sun kai kansu ga sojojin runduna ta uku a yankin Baga da ke Najeriya.

    Haka nan, sanarwar ta ce wani ɗan shekara 25 shi ma ya miƙa kansa ga sojojin runduna ta uku a Kekeno da ke ƙarmar hukumar Kukawa a jihar Borno inda ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun yi garkuwa da shi a kan titin Monguno zuwa Maiduguri a shekarar 2020.

    Ya bayyana cewa a lokacin da aka kama shi, an tilasta masa yin aiki a matsayin mai gadi a ɗaya daga cikin sansanonin ƙungiyar da ke tafkin chadi.

    ..
    ..
  14. Tinubu na jimamin mutuwar mutane a fashewar tankar mai a Rivers

    ..

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da suka mutu sakamakon tashin gobara a wata tankar mai a Patakwal da ke jihar Rivers.

    Cikin wata sanarwa da kakakinsa, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Lahadi, shugaba Tnubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga gwamnati da al'ummar jihar Rivers game da ibtila'in da ya faru har mutane da dama suka rasa rayukansu baya ga asarar dukiya.

    Shugaba Tinubu ya yi addu'ar samun sauƙi ga waɗanda suka ji rauni sakamakon lamarin.

    Shugaban ya umarci hukumomin gwamnati a jihar su ci gaba da aiki da gwamnati domin samar wa mutanen da lamarin ya ritsa da su tallafi.

    Shugaba Tinubu ya yaba wa jami'an da suka yi gaggawar agazawa mutanen da suka gamu da ibtila'in .

    Ita ma uwargidan shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta miƙa saƙon ta'aziyyarta ga gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a fashewar tankar man.

  15. Ƴan Najeriya na murna kan ziyarar da Harry da Meghan za su kai ƙasar

    ..

    Yarima Harry da mai ɗakinsa Meghan Markel za su ziyarci Najeriya a wata mai kamawa bayan goron gayyatar da suka samu daga babban hafsan tsaron ƙasar, Janar Christopher Gwabin Musa, kamar yadda wani jami'in soji ya bayyana.

    "Ziyarar za ta ƙarfafa tasirin Najeriya a taron wasanni na 'Invictus Games' da kuma yiwuwar karɓar baƙuncin taron a shekaru masu zuwa," in ji kakakin hedikwatar tsaron Najeriya, Tukur Gusau, cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi.

    Ana shirya taron na invictus games domin tallafa wa dakarun tsaro da aka ji wa rauni ko suke fama da rashin lafiya da waɗanda suka yi ritaya.

    Yariman Duke da Gimbiyar Duchess na Sussex na da alaƙa mai ƙarfi da Najeriya.

    A shekarar da ta gabata, Najeriya ta halarci taron wasannin inda ta lashe kyautar zinare da tagulla, sannan ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta shiga wasannin.

    Yarima Harry ya ƙaddadamar da Invictus Games a shekarar 2014.

    Lokacin da Najeriya ta shiga wasan a bara da aka yi a Jamus, ministan tsaron Najeriya Mohammed Badaru Abubakar ya nuna sha'awar karɓar baƙuncin wasan, kamar yadda Brigediya Janar Gusau ya ce.

    Zuwa yanzu babau cikakken bayani kan ranar da Harry da Meghan za su ziyarci Najeriya sai dai za su gudanar da ayyuka da dama yayin ziyarar ciki har da ganawa da rudnunar tsaron Najeriya da kuma halartar bukukuwan gargajiya.

    Labarin ziyarar tasu ya faranta ran mutane da dama a Najeriya.

    Wani mai amfani da shafin X ya wallafa cewa "Najeriya na maraba da ɗiyarmu!".

    Zuwa yanzu dai Harry da Meghan ba su ce komai ba game da gayyatar.

  16. Burkina Faso ta sake dakatar da ƙarin kafofin labaran ƙetare

    Burkina Faso ta sake dakatar da karin kofofin yaɗa labaran ƙasashen ƙetare daga ƙasar kan labaran da suka yaɗa na ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch da ke zargin sojoji sun kashe sama da mutum 200.

    Gwamnatin Sojin ƙasar a yanzu ta haramta kafofin yaɗa labaran Faransa, na TV-cinq da shafin Le Monde da Guardian da kuma tashar DW ta Jamus

    Wakilin BBC, ya ce a ranar Alhamis da ta gabata, gwamnatin sojin Burkina Faso ta umarci a dakatar da BBC da kuma Muryar Amurka wato VOA.

    Kakakin gwamnati ya ce an yi musu azarɓaɓi wajen ba da rahotannin inda ya ce gwamnati ta kafa kwamiti da zai yi bincike da gano gaskiyar abin da ya faru.

  17. Jagororin ƙasashen Afirka na halartar taron ƙoli na Bankin Duniya

    ..

    Shugabannin ƙasashen Afirka da dama na haɗuwa a Nairobi, babban birnin Kenya domin halartar taron yini biyu na ƙungiyar raya ƙasashe ta duniya, IDA ƙarƙashin bankin duniya.

    Taron zai magance matsalolin ci gaba da nahiyar Afirka ke fama da su tare da yin aiki wajen samar da hanyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen.

    IDA wani ɓangare ne na bankin duniya da ke taimaka wa ƙasashen duniya mafiya talauci 75, 39 cikinsu na nahiyar Afirka.

    Cikin shugabannin da za su halarci taron akwai Andry Rajoelina daga Madagascar sai Julius Maada Bio daga Saliyo da Lazarus Chakwera daga Malawi akwai kuma Samia Suluhu Hassan ta Tanzaniya da Hassan Sheikh Mohamud na Somaliya.

    Sauran sune Évariste Ndayishimiye daga Burundi da Mohamed Ould Ghazouani na Mauritaniya da Azali Assoumani daga Cosmoros.

  18. Yadda matsalar man fetur ta 'rincaɓe' a sassan Najeriya

    ..

    Al'umma na ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin mai a faɗin Najeriya abin da ya sa masu sayar da man a kasuwar bayan fage ke cin karensu babu babbaka inda har suke sayar da shi kan N1,200 duk lita ɗaya a wasu yankunan.

    Tun makon da ya gabata ake ganin dogayen layuka na ababen hawa a gidajen man da ke sayarwa, yayin da wasu kuma suke kulle saboda ba sa sayarwa.

    Lamarin na zuwa ne yayin da a baya-bayan nan kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ce ya magance matsalar da ke janyo ƙarancin man.

    Ita ma ƙungiyar dillalan man fetur da Iskar Gas ta arewacin Najeriya, AROGMA, ta ce akwai wasu tarin matsalolin da suka assasa yanayi da ake ciki, kuma ya zama dole a lalubon bakin zarensu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a Abuja, babban birnin Najeriya da wasu jihohi, gidajen mai sun ƙara kuɗi inda suke sayar da shi tsakanin N750 da N800 kowace lita ɗaya.

    A gidajen man NNPCL da suke sayar da shi kan N617 kowace lita ɗaya, sai dai akwai dogayen layukan ababen hawa.

    A jihar Jigawa kuma, an rufe gidajen mai da dama inda ƴan bumburutu ke sayar da man a kan N1,100 kowace lita ɗaya.

    A wasu yankunan jihar Legas kuwa, masu sayar da man a kasuwar bayen fage na saida lita biyar ta mai a kan N5,500.

    Akasarin gidajen mai a Alimosho da Ojo da ƙaramar hukumar Badagry a rufe suke sannan akwai dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai.

    A Jos, babban birnin Filato, an ga dogayen layuka a tsirarun gidajen man da ke sayar da man kuma bayanai na cewa suna sayarwa kan N800.

  19. Sanƙarau ta halaka mutum 85 a Yobe

    ..

    Gwamnatin jihar Yobe ta ce sanƙarau ta kashe mutum 85 tsakanin Janairu da Afrilu sakamakon ɓarkewar cutar a jihar.

    Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana ne ya tabbatar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Damaturu.

    Ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke cewa cutar ta yi ajalin sama da yara 200 cikin mako biyu inda ya ce haƙiƙanin adadin shi ne 85.

    Ya kuma ce fiye da marasa lafiya 2,510 da suka kamu da cutar a jihar sun samu sauƙi kuma an sallame su daga asibiti.

    Dakta Gana ya kuma ce an tura jami'an lafiya na sa kai sama da 200 zuwa sassan ƙananan hukumomin Poyiskum da Fika a wani ɓangare na ƙoƙarin da ma'aikatar take na daƙile cutar.

    Ya ce ma'aikatan lafiya sun bi gida-gida domin ganowa tare da tura mutanen da ke da cutar asibiti.

    Yankunan arewacin Najeriya na fama da matsanancin zafi a tsukin nan - yanayin da ke haddasa cutar ta sanƙarau.