Fashewar abubuwa a Beirut: Jama'a sun bukaci gwamnati ta yi bayani

Bayanan bidiyo,

Bidiyon yadda bam ɗin ya fashe a birnin Beirut

Mutane a birnin Buirut sun nuna fushinsu ga gwamnati kan cewa sakacinta ne ya janyo fashewar sinadirai a ranar Talata.

Shugaba Michel Aoun ya ce ton 2,750 na sinadarin ammonium nirate da aka ajiye ba tare da bin tsarin kariya ba.

Fashewar ta janyo mutuwar mutum akalla 135 tare da jikkata fiye da 4,000 kuma yanzu haka dokar tabaci na makonni biyu a kasar.

Ammonium nitrate sinadirai ne da ake amfani da su wajen yin takin zamani domin noma sannan ana amfani da su wajen kera abubuwan fashewa.

Shugaban zai jagoranci wani taron ministoci a ranar Laraba, sannan ya kaddamar da dokar ta baci na tsawon makonni biyu.

Za a shafe kwanaki uku ana zaman makoki a fadin kasar tun daga ranar Laraba.

Beirut's destroyed port with smoke rising

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Abin fashewar ya lalata kusan dukkan tashar jirgin ruwan birnin

Ministan harkokin cikin gidan na ƙasar ya ce binciken farko ya nuna cewa wani sinadari ne da aka ajiye a cikin tashar jirgin ruwan ya fashe.

Firai minista Hassan Diab ya ce za a hukunta waɗanda suka yi sakacin aukuwar wannan iftila'in:

"Ba za a kyale wannan lamarin ya wuce ba a dauki mataki ba. Dukkan wadanda suke da alhakin wannan iftila'in za su ɗanɗana kuɗarsu. Wannan alkawari ne na ɗauka ga waɗanda suka sadaukar da rayukansu, da waɗanda aka jikkata, kuma wannan ya kasance alƙawari da ƙasar nan ta ɗauka."

Shugaban ƙasar Lebanon Michel Aoun ya kira wani taron gaggawa na kwamitin tsaron ƙasar, inda shi kuma firai ministan ya ayyana Laraba a matsayin ranar da ƙasar za ta yi zaman makoki.

Ya kuma yi magana kan abin da ya kira "wani ɗakin ajiye kaya da aka tara sinadarai a ciki tun 2014", amma ya ce zai bari shari'a ta dauki mataki kan batun.

Kafofin watsa labarai na ƙasar sun nuna hotunan mutane a ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana ƙarar fashewar ta farko a matsayin mai gigitarwa, kuma hotunan bidiyo sun nuna yadda fashewar ta lalata motoci da gine-gine masu yawa.

An kuma ji ƙarar fashewar a tsibirin Cyprus mai nisan kilomita 240 a can cikin gabashin tekun Rum.

Lebanon
Bayanan hoto,

Lamarin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 100

Wanan iftila'in ya zo wa Lebanon a lokacin da ta ke cikin mawuyacin hali, kamar matsananciyar matsalar tattalin arziki da ta rarraba kawunan 'yan kasar, da kuma zaman ɗar-ɗar da ake yi kan yanke hukuncin da wata kotu za ta yi wa wadanda suka kashe tsohon firai ministan kasar Rafik Hariri a 2005.

Wata kotun Majalisar Ɗinkiun Duniya ce ke shirin yanke hukunci game da shari'ar, wadda ake zargin wasu mutum huɗu da aikata kisan ta hanyar tashin wani bam a mota.

Dukkanin mutum huɗun 'yan ƙungiyar Hezbollah ne wadda ke samun goyon bayan Iran, wadda kuma ta sha musanta zargin hannunta a ciki. Ranar Juma'a za a yanke hukuncin.

A hotel's windows shattered

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Fashewar ta yi barna a wurare da dama