Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir da A'isha Babangida

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Buhari Muhammad Fagge ke cewa sai da safe.

  2. Dole ne Isra'ila ta daina gangancin da take yi - Iran

    A

    Ministan harkokin wajen Iran Hossein Amirabdollahian ya bayyana cewa ba za su sake kai hari kan Isra'ila ba kuma harin da suka kai mata a baya ba na fararn hula ba ne, na neman fansa ne kan sasanin sojojinta.

    Da yake magana kan harin da Isra'ila ta kai wa ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, Mista Amirabdollahian ya ce dole ne Isra'ila ta daina rawar kan da take ko kuma Iran ta sake kai mata wani mummunan harin.

    Ya kuma ci gaba da cewa gwamnatin Isra'ila ta "yan ta'adda ce" kuma ya kira wannan ƙasar da cewa wuri ne da aka mamaye da ƙarfi".

  3. Tinubu na sane ya bai wa 'yan arewa manyan muƙamai - Ribadu

    A

    Mai bai wa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribaɗu, a ranar Alhamis ya ce Shugaba Tinubu yana sane ya naɗa 'yan arewa manyan muƙamai.

    Ribaɗu ya bayyana haka ne a Sokoto yana cewa shugaba Tinubu ya ɗauki 'yan arewa ya sa a wasu mukamai masu muhimmanci saboda yana son a kawo karshen rikicin yankin.

    Da yake gabatar da wata maƙala kan "shawo kan matsalolin tsaro da arewa ke fuskanta a Najeriya" wanda wani bangre ne na yaye ɗaliban aji na 38, 39, 40 da kuma 41 na Jami'ar Danfodiyo da ke Sokoto, ya nuna bacin rai kan matsalolin da arewa ke fuskanta kama daga matsalar tsaro zuwa yaran da ba sa zuwa makaranta da dai sauransu.

    Ya kuma ƙara da cewa talaucin da yankin ke ciki na ƙara ta'azzara a kullum.

    "Yayin da Tinubu yake kada gwamnatinsa, ya sanya Arewa a tsakiyar zuciyarsa kuma yana shirin yin komai domin ceto yankin daga halin da yake ciki.

  4. Spain na son a bai wa Falasɗinawa cikakken wakilci a MDD

    A

    Bayan bayanin da ministan harkokin wajen Iran a yayin taron kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, wakilin Spain a Majalisar ya ce yayin da ake ganin Isra'ila na da 'yancin kare kanta, tare da wasu ƙasashe 139, suna goyon bayan a bai wa Falasɗinawa cikakken wakilci a MDD.

    Ambasadan Isra'ila ya yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai wa Isra'ila a ranar Asabar, da kuma harin 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai, wanda ya kashe Isra'ilawa 1,200, ya ce matsayar ƙasarsa ita ce, samar da 'ƙasar Falasɗinawa yancinsu ne da kuma ganin damarsu, kuma babu shakka zai iya zama mafita ga rikicin yankin.

    Tattaunawar da kwamitin sulhun ya fara a safiyar Alhamis ta mayar da hankali wajen shawo matsalolin Gabas ta Tsakiya da kuma ɗaga likafar Falasɗinawa zuwa zama cikakkiyar mambar MDD.

  5. Da yiwuwar mu sake sawa Iran takunkumi - Amurka

    A

    Cikin wata sanarwa da take nuna yiwuwar sanyawa sabbin takunkumai ga Iran saboda harin makami mai linzami da na jirage marasa matuƙa da ta kai wa Isra'ila.

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce Amurka da ƙawayenta da suka dade tare za su ci gaba da kare Iran tare da riƙe Iran a matsayin wadda ba ta gaskiya.

    Wannan tsohuwar alaƙar za ta janyo mu sanya sabbin takunkumai da koma neman yadda za mu karbe iko da wajen.

    Sanarwar ta ce sabbin takunkuman an ce za su mayar da hankali ne kan shugabannin da cibiyoyin da suke da alaƙa da Dakarun Juyin Juya hali. ma'aikatar tsaro da sauran wasu cibiyoyi, in ji Biden.

    "Yayin da na yi magana da shugabanin G7 a safiyar bayan harin, mun amince ba ki ɗaya mu ƙara matsawa Iran lamba ta fuskar tattalin arziki, kuma ƙawayenmu da abokan hulɗarmu za su sake ɗaukar matakan tattalin arziki,".

  6. Raisi ya ce Iran ba ta bar teburin tattaunawa ba

    D

    Shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi ya ce ƙasarsa ta shirya tattaunawar sulhu.

    Mista Raisi ya ce "idan kai mai yawan surutu ne da ɓaɓatu, to mu ba haka muke ba, kuma ba mu bar teburin sulhu ba."

    A lokaci guda kuma, ya ce "yaren da ake amfani da shi domin tunzura Iran ba zai karya mana gwiwa ba."

    Ebrahim Raisi ya kwatanta manufofin harkokin wajen ƙasar da na lokacin Hassan Rouhani yana cewa lokacin da mutum zai nemi cinikayya kan makamanmu, kuma a yi shi yadda ya ga dama."

    "Jiya, wasu mutane sun ce, ba za mu iya rubuta taken mutuwar Isra'ila ba da makamai, wanda zai janyo zaman ɗarɗar ga makiyanmu, amma yau makaman rokarmu za su iya sauka a tsakiyar birnin maƙiyanmu domin su fahinci laifukan da suke yi da kuma kisan kiyashin da suke yi."

  7. Labarai da dumi-dumiEFCC na neman tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo

    Hukumar yaƙi da cinhanci a Najeriya EFCC ta ayyana tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

    Matakin hukumar na zuwa ne 'yan awanni bayan kotu ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar ta shigar saboda wanda take zargin bai halarci zaman kotun ba.

    Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC mai suna Kemi Phinro ya faɗa mata cewa "wani mutum da ke da kariya daga tuhuma ne ke bai wa tsohon gwamnan mafaka".

    "EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 80.2," in ji hukumar cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na zumunta ɗauke da hoton tsohon gwamnan.

    Tun a jiya Laraba rahotonni suka ce gwamnan Kogi na yanzu Usman Ododo ne ya fice da Yahaya Bello a motarsa lokacin da jami'an EFCC suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.

    Gwamnatin Kogi ba ta ce komai ba game da zargin zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

    Lauyan hukumar ya kuma ce suna duba yiwuwar neman taimakon rundunar sojin Najeriya wajen kamawa tare da gurfanar da shi a gaban kotun.

    A watan Janairun shekarar nan ne Yahaya Bello ya miƙa ragamar mulkin jihar ta Kogi da ke tsakiyar Najeriya ga Usman Adodo, bayan ya shekara takwas a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

  8. Muna duba yiwuwar neman taimakon sojoji don kama Yahaya Bello - EFCC

    Ola Olukoyede

    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar yaƙi da cinhanci ta EFCC ta shigar kan tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello.

    Mai Shari'a Emeka Nwite ya ɗage ƙarar zuwa 23 ga watan Afrilu ne bayan lauyan EFCC, Kemi Phinro, ya faɗa wa kotun cewa wanda ake zargin bai halarci zaman ba saboda "wani wanda yake da kariya na ba shi mafaka", kamar yadda kafar talabijin ta Channels ta ruwaito.

    Lauyan ya ƙara da cewa hukumar na duba yiwuwar haɗa kai da dakarun soja don ganin sun kama tsohon gwamnan.

    Tun a jiya Laraba rahotonni suka ce gwamnan Kogi na yanzu Usman Adodo ne ya fice da Yahaya a motarsa lokacin da jami'an hukumar suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.

    EFCC na tuhumar Yahaya Bello da zargin halasta kuɗin haram da suka kai naira biliyan 8.2 a lokacin da yake gwamnan jihar da ke tsakiyar Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar.

  9. Jamus ta tsare mutum biyu kan zargin yi mata leƙen asiri

    Jamus

    Ma'aikatar Harkokin Waje ta Jamus ta gayyaci jakadan Rasha bayan kama mutum biyu da ake zargi da yin leƙen asiri da shirya zagon-ƙasa a wuraren da sojoji suke.

    Masu gabatar da ƙara na Jamus sun zargi mutanen biyu - wadanda aka bayyana a matsayin 'yan asalin Jamus da Rasha - da yunkurin kitsa hari, da kuma tuntubar hukumar leken asirin Rasha.

    Wakilin BBC ya ce ana zargin su da ɗaukar hotuna da kuma bidiyon wuraren da Amurka da Jamus ke ajiye makamai a Baveria.

  10. Kotu ta jingine dakatarwar da aka yi wa Ganduje daga APC

    ..

    Wata babbar kotun tarayya a Kano ta dakatar da shugabannin jam'iyyar APC a mazaɓar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa daga ɗaukan ƙarin mataki a kan dakatar da shugaban jam'iyyar ta ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.

    A wata takardar kotu mai ɗauke da sa hannun magatakardan kotun, Usama Ibrahim Isah, mai shari'ar Abdullahi Muhammad Liman ne ya bayar da umarnin inda ya buƙaci mutanen da ake ƙara da su guji aiwatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje har zuwa lokacin da za a saurari ƙarar da shugaban APC ya shigar a kotu.

    Umarnin kotun ya zo ne sa'oi bayan da babbar kotu a Kano ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Ganduje saboda zarginsa da rashawa.

    Kotun ta kuma umarci ɓangarorin da su tsaya kan matsayin da ake kafin taron manyan jam'iyyun APC na mazaɓar ta Ganduje wanda bayansa ne aka dakatar da shugaban jam'iyyar a mazaɓar.

    Mai shari'a Liman ya sa ranar 30 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a saurari shari'ar.

    Waɗanda ake ƙara sune Haladu Gwanjo da Nalami Mai AC da Muhammadu Baiti da Danmalam Gata da Musa Lado da Laminu Sani Barguna da Umar Sanda da Auwalu Galadima da Abubakar Daudu.

  11. 'Ɗaukar matakan shari'a da gangan ne ke ɓata sha'anin jagoranci a PDP'

    ..

    Majalisar Amintattu ta jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa akwai wasu mambobin jam'iyyar da ke yi wa kundin tsarin mulkin jam'iyyar zagon ƙasa ta hanyar ɗaukar matakan shari'a ga shugaba da sakataren jam'iyyar.

    Shugaban kwmaitin, Sanata Adolphus Wabara ne ya bayyana hakan yayin buɗe taron majalisar gudanarwar jam'iyyar da ake yi a Abuja.

    Sanata Wabara ya ƙara da cewa ɗya daga cikin abubuwan da ke damun 'yan jam'iyyar shi ne " halin da shugabancin jam'iyyar ke ciki a yanzu haka."

    Batun jagorancin jam'iyyar ne dai yake kokarin raba kan jama'a, inda ko a ranar Laraba sai da wani ɓangare na 'yan jam'iyyar suka gudanar da zanga-zanga a sakatariyar jam'iyyar.

  12. Mutum biyar sun mutu bayan haɗarin jirgin helikwafta na dakarun Kenya

    Wani jirgi mai saukar ungulu na rundunar sojin Kenya ya yi haɗari jim kaɗan bayan da ya tashi.

    Kafar yaɗa labarai ta NTV ta ruwaito kakakin ƴan sanda na tabbatar da mutuwar mutane biyar da ke cikin jirgin.

    Ya kuma ce akwai mutum uku da suka tsira kamar yadda ƴan sandan suka shaida.

    Kakakin gwamnatin Kenya Isaac Mwaura ya nemi ƴan Kenya da su kwantar da hankalinsu su kuma guji yaɗa jta-jita.

    Saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, ya zo bayan labarin haɗarin da jirgi sami saukar ungulun ya yi inda bayanai ke cewa akwai manyan jami'ai a ciki.

    "Kakakin gwamnatin ya ce za a fitar da sanarwa game da haɗarin nan kusa.

  13. Korar jami'an diflomasiyyarmu daga Burkina Faso ba shi da tushe – Faransa

    Gwamnatin Faransa ta ce matakin Burkina Faso na korar jami'an diflomasiyyarta uku ba shi da tushe bare makama.

    Tun farko ma'aikatar harkokin wajen Burkina Faso ya ce an umarci jami'an uku a ofishin jakadancin Faransa da su fice daga ƙasar saboda abin da ta kira yin maƙarƙashiya ga gwamnati.

    Wasu rahotanni sun nuna cewa jami'an suna haɗuwa da masu fafutuka daga ƙungiyoyin farar hula.

    Tun hawansu kan mulki bayan kifar da gwamnati a 2022, sojojin Burkina Faso sun nesanta kansu daga Faransa wadda ta mulke su a baya.

    Sun tilasta wa sojojin Faransa ficewa daga ƙasar tare da dakatar da kafar yaɗa labaran ƙasar da neman Faransar ta yi wa jakadanta kiranye.

  14. Jam'iyyar PDP na gudanar da taron majalisar zartaswa

    ..

    A yau ne babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ke gudanar da taron majalisar zartaswarta na ƙasa karo na 98.

    An soma taron ne da na kwamitin amintattu na jam'iyyar kafin a ɗora da na majalisar zartaswar a hedikawatar jam'iyyar da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

    Taron na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke fuskantar rikicin cikin gida.

    Ƙusoshin jam'iyyar daga sassa daban-daban na Najeriya ne ke halartar taron.

    Ga wasu hotuna da muka samu daga wurin taron.

    ..
    ..
    ..
  15. Muna sayen dala daga gwamnati kan naira 980 – Shugaban ƴan canji

    ..

    Ƙungiyar ƴan canji ta Najeriya ta ce ƴan canji sun fara sayan dala ɗaya a kan naira 980 a kasuwar bayan fage sannan su sayar kan naira 1,020.

    Shugaban ƙungiyar ta ƙasa, Aminu Gwadabe ne ya tabbatar da haka a hirarsa da gidan talabijin na Channels inda ya ambaci cewa darajar naira ta ƙaru a lokaci kaɗan da ba a taɓa tsammani ba.

    Gwadabe ya jinjinawa gwamnati da kuma babban bankin ƙasar kan ƙoƙarinsu inda ya ce wannan ne karon farko cikin shekara 15 da farashin dala a kasuwar ƴan chanji ke ƙasa da farashin da ake saidawa a hukumance.

    Ya shaida cewa yanzu babu raɗe-raɗin da ake yawan yi da ke zuzuta farashin dala.

    Gwadabe ya ƙara da cewa "a halin yanzu muna siya daga gwamnati a kan naira 980 sannan mu sayar a kan naira 1,020".

  16. Burkina Faso ta kori jami'an diflomasiyyar Faransa

    ..

    Burkina Faso ta kori jami'an diflomasiyya uku saboda neman yi wa gwamnati maƙarƙashiya, kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta shaida cikin sanarwar da ta aike wa Faransa.

    Sanarwar na ɗauke da kwanan watan 16 ga watan Afrilu sai dai ba ta yi cikakken bayani kan ayyukan da jami'an suka yi ba.

    An buƙaci jami'an diflomasiyyar da suka haɗa da mashawarta kan harkokin siyasa biyu a ofishin jakadancin Faransa a Ouagadougou, su fice daga Burkina Faso cikin sa'a 48," in ji sanarwar.

    Alaƙa tsakanin Burkina Faso da Faransa - ƙasar da ta mulke ta a baya ta yi tsami tun da Kyaftin Ibrahim Traore ya ƙwace mulki a juyin mulkin da aka yi a Satumbar 2022.

    Shugaban sojin da ke mulki ya karkatar da alaƙar Burkina Faso ga Rasha tare da kawo ƙarshen kusancinsu da Faransa.

    A ƙarƙashin mulkinsa, an kori jami'an diflomasiyyar Faransa da dama kuma an rufe sansanin sojojin Faransa da ke ƙasar.

  17. An gurfanar da mutum 104 a kotu kan zargin ayyukan daba a Kano

    ..

    Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da mutum 104 da ake zargi ƴan daba ne a gaban wasu kotuna da ke unguwar Nomandsland.

    An kama mutanen a wuraren hawan sallah da masarautun Kano ke yi duk shekara a bukukuwan sallah.

    Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Fesbuk inda ya ce ana zargin mutanen da laifukan daba da riƙe makamai da kuma ta'amali da miyagun ƙwayoyi.

    Kiyawa ya ce an samu kama mutanen ne bayan binciken da aka yi a sashen binciken manyan laifuka na rundunar kamar yadda kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel ya umarta.

    A baya-bayan nan ma rundunar ƴan sandan ta Kano ta kama wasu da ta ce ƴan daba ne waɗanda kuma suke addabar unguwar Ɗorayi.

    ..
  18. An kulle fitaccen ɗan jarida a Tunisia saboda ɓata suna

    ..

    Wa kotu a Tunisiya ta yanke wa fitaccen ɗan jarida hukuncin wata shida a gidan gyaran hali saboda ɓata sunan wata ma'aikaciyar gwamnati, kamar yadda lauyansa ya bayyana.

    Ƙanin Mohammed Boughalleb da lauyansa sun ce ɗan jaridar ya fuskanci tuhume-tuhumen cin zarafin ma'aikaciyar gwamnati.

    A watan da ya gabata, an tsare shi a Tunis, babban birnin ƙasar sakamakon ƙorafin da ma'aikaciyar da ke aiki a ma'aikatar harkokin addini ta shigar.

    Rahotanni sun ce ma'aikaciyar ta zargi Boughalleb da lalata ƙimarta da kuma sunanta a saƙonnin da ta wallafa a shafinta na fesbuk da kuma kafafen yada labarai.

    Mista Boughalleb, wanda yake aiki a gidan rediyo, an san shi da yawan sukar Shugaba Kais Saied.

    Shugaban ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasar, Zied Dabbar ya ce lamarin shi ne yunƙuri na baya-bayan nan na gwamnati don tsoratar da ƴan jarida.

    Ƙungiyar ƴan jarida ta duniya - Reporters Without Borders, ta yi gargaɗi kan ƙaruwar takunkumin da ake yi wa ƴan jarida a Tunisiya.

  19. Za mu iya mayar wa maniyyata rarar kuɗi saboda karyewar dala - NAHCON

    ..

    Shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyata rarar kuɗin da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka.

    Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da kafar sadarwa ta DCL da ke intanet wadda kuma hukumar alhazan Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis.

    "Idan misali ranar da muka yi shela dala tana naira 1,000, sai ya zamana kai ranar da ka saka kuɗinka ka saka ne ranar da take naira 900, to ai ka ga akwai rarar naira 100. Wannan naira 100 ya kamata mu mai da maka. Ba mu jira tana ta yin ƙasa ba. To idan kuma ta ƙara yin sama fa?" In ji Jalal Arabi.

    Ya ƙara da cewa "indai da rai da lafiya kuma idan dai mu ne a kan kujerar to ba za mu zauna a kan haƙƙin kowa ba da izinin Allah. Za mu tabbatar mun biya wannan rarar."

    To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan na Najeriya bai faɗi lokacin da za a mayar wa da maniyyatan rarar kuɗaɗen nasu ba.

    A mafi yawancin lokuta dai hukumar ta Alhazai kan mayar wa alhazai rarar kudaɗen ne bayan kammala aikin Hajji.

    A yanzu haka dai naira na ci gaba da samun tagomashi a kan dalar Amurka inda bayanai ke nuna farashin dala a kasuwar bayan fage na tsakanin naira dubu ɗaya da ƙasa da haka.

  20. An sake kuɓutar da ƴar Chibok da ƴaƴanta daga hannun Boko Haram

    ..

    Sojoji ƙarƙashin rundunar kakkaɓe dazuka daga ƴan ta'adda a yankin arewa maso gabas sun kuɓutar da ƙarin ƴar makarantar Chibok, Lydia Smith.

    Rahotanni daga jaridun Najeriya na cewa sojojin runduna ta 82 a ƙaramar hukumar Gwoza sun kuɓutar da Lydia ne tare da ƴaƴanta uku a ranar Laraba.

    Jaridun sun ruwaito cewa Lydia ta miƙa wuya ga dakarun a Gwoza. Tana ɗauke da juna biyu da ya kai wata biyar kuma ta yi iƙirarin cewa ta fito daga garin Pemi a Chibok.

    A ranar 14 ga watan Afrilu ne aka cika shekara 10 tun bayan da Boko Haram ta sace ƴan matan su 276 daga makarantarsu da ke Chibok a jihar Borno.

    57 daga cikin ɗaliban sun kuɓuta byan sace su, 16 kuma an kuɓutar da su daga bisani sai wasu 107 da aka sake su a lokuta daban-daban bayan da aka tattauna.

    Gwamnati da sojojin Najeriya sun yi alƙawarin ƙwato ragowar ƴan matan da har yanzu suke hannun mayaƙan na Boko Haram.