Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Mu tara gobe da safe - idan Allah Ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An zartas da hukuncin kisa kan mutanen da aka samu da laifin ta'addanci a Iraqi

    Zartas da hukuncin kisa

    Hukumomin Iraki sun zartar da hukuncin kisa kan wasu mutane 11 da aka samu da laifin ta'addanci bayan zarginsu da zama 'yan ƙungiyar IS.

    An zartar da hukuncin kisan ne a wani gidan yari da ke birnin Nasiriyya a kudancin ƙasar.

    Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi Alla-wadai da abin da ta kira nuƙu-nuƙu a tsarin shari'ar.

  3. Amurka za ta aika sabon tallafin soji zuwa Ukraine

    Tallafin soji

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya ce ƙasar za ta fara aika sabon tallafin soji zuwa Ukraine cikin sa'o'i bayan ya saka hannu kan wani kudirin doka da majalisar dokokin kasar ta amince da shi.

    Da yake magana a wani taron manema labarai a fadar White House, Mista Biden ya ce tallafin da ya kai dala biliyan 61 zai kara inganta tsaro a Amurka da ma duniya baki ɗaya.

    Ya ce cikin kayan aikin da za a aika Ukraine har da na matakan tsaron hare-hare daga sama da bindigogi da na rokoki da kuma motoci masu sulke.

    Biden ya ce tallafin ba na tsaron Ukraine ba ne kadai, amma na tsaron nahiyar Turai.

  4. Sojoji sun yi fata-fata da maɓoyar 'yan ta'adda a Borno

    Sojoji

    Dakarun sojin Najeriya sun ce yi wa maɓoyar 'yan ta'adda lugudan wuta bayan kai hare-hare ta sama a ƙananan hukumomin Damasak da Mobbar na jihar Borno.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ya fitar, ta ce an kai wa 'yan ta'ddan hari ne ranar Talata 23 ga watan Afrilu.

    Samamen na haɗin gwiwa tsakanin rundunar Operation Haɗin Kai da sojin saman Najeriya da kuma dakarun MNJTF, ya ragargaji sansanonin 'yan ta'ddan abin da ya tilasta wa da dama tserewa.

    Sai dai Gabkwet ya ce 'yan ta’addan sun yi yunkurin far wa sojojin sashe na 4 na MNJTF a garin Lada da ke kan iyakar jamhuriyar Nijar da Najeriya.

    "Mun bi bayan 'yan ta’addan da suka tsere a kan babura 8, inda muka gano su a wurare biyu da ke kauyen Zarri, mai tazarar kilomita 28 daga gabashin Damasak da Mala Alide a karamar hukumar Mobbar ta Jihar Borno," in ji Gabkwet.

    Ya ce an gano wani wuri da 'yan ta'addan suke ɓoye wa tare da baburansu a cikin Kauyen, karkashin bishiyoyi.

    Ba ya ga wannan, dakarun Operation Haɗin Kai sun kuma kai hare-hare ta sama karkashin jagorancin jiragen leƙen asiri na ƙasar Nijar (ISR) a wuraren da 'yan ta'addan suke.

    Hotunan sashen leƙen asirin sun tabbatar da cewa an kashe 'yan ta'adda da dama tare da lalata sansanoninsu.

    Sojojin sun ce ƙoƙarin haɗin gwiwa da suke yi na haifar da sakamako mai kyau a iyakar ƙasar.

    Sun ce hakan ya janyo raguwar ayyukan ta'addanci da sauran laifukan da masu keta iyakokin ƙasar domin guje wa shari'a ke aikata wa.

  5. An dakatar da limamin cocin da ya jagoranci taron tunawa da Alexei Navalny

    Shugaban Cocin gargajiya na Rasha ya dakatar da limamin cocin da ya jagoranci taron tunawa da ɗan adawar Kremlin, Alexei Navalny.

    An dakatar da Dmitry Safronov daga aiki na tsawon shekara uku tare da rage masa muƙami kuma an canza shi zuwa wani coci a Moscow.

    Cocin ba ta bayyana dalilin yanke shawarar ba, amma shugaban cocin Patriarch Kirill ya kasance babban magoyin bayan shugaba Putin.

    Alexei Navalny ya mutu ba za to ba tsammani a gidan yari a watan Fabrairu.

    A lokacin, magoya bayansa sun yi ƙorafin cewa ba su samu wata coci da za ta shirya gudanar da jana'izar sa ba.

  6. Jaririyar da aka ciro daga ciki bayan mutuwar uwarta a Gaza

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

    Wata jaririya ta yi nisan kwana bayan likitoci sun yi nasarar ciro ta da rai bayan wani harin Isra'ila ya kashe mahaifiyarta a Zirin Gaza.

    Likitocin sun yi wasu 'yan dabaru wajen tabbatar da cewa Sabreen ta ci gaba da nimfashi bayan ciro ta daga ciki ta hanyar tattaɓa jikinta da kuma saka ta cikin kwalabar reno.

    An saka mata sunan mahaifiyarta Sabreen ne don girmama mahaifiyar tata.

  7. Ƴan bindiga sun kashe mutum uku, sun yi garkuwa da takwas a Kaduna

    'Yan bindiga

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu takwas a wani hari da suka kai kauyen Hayan Habuja a Kakangi da ke karamar hukumar Birnin-Gwari na jihar Kaduna.

    Sabon harin na zuwa ne kwanaki biyar bayan da ‘yan bindiga suka kashe wasu mutum 23 a anguwan Danko kusa da Dogon Dawa na karamar hukumar.

    Sakataren wata kungiya ta Birnin-Gwari BEPU, Abdulrrashid Abarshi ya fada wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun far wa garin ne da misalin karfe 3 na ranar Talata.

    Ya ce an harbe mutum biyu nan take yayin da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da wasu mutum huɗu.

    "Lokacin da ‘yan bindigar suka zo fita kauyen Hayan Abuja, sun kashe wani mutum wanda ya fita neman itace da kuma yin garkuwa da mutane hudu,” in ji Abarshi.

    Ƙungiyar ta BEPU ta yi kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen daukar matakai na shawo kan matsalar tsaro a yankin.

  8. Ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita Nairobi

    ..

    Ma'aikatan agajin gaggawa na kwashe iyalai daga yankunan Nairobi babban birnin ƙasar Kenya sakamakon ambaliyar ruwa da ta mamaye yankin.

    Ƙasar ta fuskanci ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na makonni da dama kuma ruwan laka ya mamaye unguwannin da ke birnin.

    Ɗan majalisar dattawa mai wakiltar ƙaramar hukumar Nairobi, Edwin Sifuna, ya ce ambaliyar ta yi kamari, kuma lamarin ya fi ƙarfin hukumomin yankin inda hakan ya yi sanadiyyar dakatar da sufurin jiragen ƙasa a Nairobi.

    A makon da ya gabata Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla mutane 32 ne suka rasa rayukansu sannan aka raba sama da 40,000 da muhallansu.

  9. Hukumomi a Kano sun ba da shawarwarin zama da tsananin zafi mai kashe mutane

    ..

    Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun fitar da wasu jerin shawarwari ga al'umma kan yadda za su kare kansu daga yanayin da ake ciki na tsanani zafi.

    Wannan na zuwa ne bayan an samu rahoton ƙaruwar zazzaɓi mai zafi da hukumomin lafiya a jihar suka danganta da ƙaruwar yanayin da kaɗawar busasshiyar iska.

    Bayanai na cewa irin wannan yanayi da aka shiga ya haifar da mutuwar mutum fiye da 40 sannan da dama suna cikin mawuyacin hali.

    Kwamishinan Lafiya Dr Abubakar Labaran Yusuf ya ce jami'an da suka tura don gudanar da bincike sun gano cewa tsananin zafin da ake fama da shi ne ya haddasa zazzaɓi mai zafi.

    A cewarsa, babu mamaki zazzaɓin ne ya jawo mace-macen da aka gani a wasu garuruwa kamar Gundutse a ƙaramar hukumar Kura a makon jiya.

    Dr Labaran ya ce rahotannin da suka samu sun nuna cewa an fara ganin ƙaruwar zazzabin mai zafi da kuma mace-mace ne tun fa arkon watan jiya.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Zahraddeen Lawan daga Kano:

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama don sauraron rahoton:
  10. Yadda dawakin soja suka tsinke a birnin Landan

    Wasu dawaki guda biyar sun lalata abubuwa da dama a birnin Landan bayan zubar da mahayansu a ƙasa.

    Bayan faruwar lamarin, dawakin sun tsere a tsakiyar birnin.

    Sun yi arangama da motoci da dama yayin da suke gudu.

    Dawaki
    Landan
    Landan
    Landan
  11. Tinubu ya ƙaddamar da tsarin karɓar kaya bashi ga ƴan Najeriya

    ..

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar.

    Bayanin hakan na ƙunshe cikin sanarwar da mai bai wa shugaban shawara kan yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar.

    Tsarin zai bai wa al'umma damar inganta rayuwarsu ta hanyar samun bashin kayyaki inda za su riƙa biya sannu a hankali tsawon lokaci.

    Da tsarin, jama'a na iya sayen gidaje da motoci da samun ilimi da kiwon lafiya ta hanyar bashi, inda za su biya daga baya.

    Shugaba Tinubu na ganin ya kamata duk wani ɗan Najeriya ya samu damar more rayuwa ta tsarin karɓar bashi da zai taka rawa sosai wajen cimma wannan ƙudurin.

    Tsarin wanda haɗin gwiwa ne tsakanin cibiyoyin hada-hadar kuɗi da ƙungiyoyin tsumi da tanadi a faɗin duniya, zai faɗaɗa damarmakin mai saye na samun kaya a kan bashi.

  12. Ministan sufuri ya ba da umarnin dakatar da kamfanin Dana

    ...

    Ministan sufuri a Najeriya, Festus Keyamo ya umarci hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama, NCAA ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Dana.

    Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da jirgin kamfanin ya zame daga titin jirginsa a tashar jirgin sama ta Murtala Muhammed da ke Legas.

    Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ministan ya kuma umarci a gudanar da bincike kan kamfanin. Binciken zai shafi dukkan matakan kariya da hanyoyin yin gyara domin tabbatar da cewa kamfanin yana bin umarnin ƙa'idojin tafiyar da harkar sufurin jirage.

    Acikin wata sanarwa da aka aikewa darakta janar na NCAA, minsitan ya ce matakin ya zamo wajibi domin tabbatar da cewa kamfanin yana bin ƙa'idojin aiki musamman na matakan kariya.

    Jirgin Dana ɗauke da fasinja 83 da ya taso daga Abuja zuwa Legas ya zame daga kan titinsa ranar Talata.

  13. Zelensky ya nemi a gaggauta kai wa Ukraine taimakon soji

    ..

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya jaddada muhimmancin samun taimakon soji cikin gaggawa, sa'o'i bayan da majalisar dattawan Amurka ta amince da kudirin bayar da agajin dala biliyan sittin da daya da aka dade ana jira.

    A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta, ya ce "duk shugaban da bai bata lokaci ba to mai ceton rayuka ne"

    Ana sa ran a yau ɗin nan Mista Biden zai rattaba hannu kan kudirin dokar, wanda kuma ya hada da tallafin biliyoyin daloli ga Isra'ila da Taiwan

    Jami'in bincike a Cibiyar Nazarin Dabarun Ukraine ta kasa, mai ba da shawara ga gwamnatin Ukraine game da harkokin soja, Mykola Bielieskov ya ce wannan tallafin zai taimaka wa Kyiv wurin kare kanta daga mamayar Rasha.

    Ya ce Cikin wadannan makudan kudade kashi daya bisa uku ne kawai zai je ga samar da makamai. Don haka, ba wai duka biliyan sittin din ne za a yi amfani da su wurin jigilar makamai ba, shi ya sa ya kamata mutane su takaita burinsu.

  14. Amurka ta ƙaƙaba takunkumi kan jagororin masu iƙirarin jihadi

    Amurka ta ƙaƙaba wa wasu jagorori da mambobin ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke Afrika ta Yamma takunkumi kan garkuwa da ƴan ƙasarta.

    An ɗauki takunkumin kan jagororin ƙungiya mai alaƙa da al-Qaeda ta Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin da kuma al-Murabitoun ta ƙasar Mali.

    "JNIM na amfani da garkuwa da kuma tsare farar hula wajen samun abin da suke so da kuma saka tsoro inda suke sa mutanen da suka tsare da iyalansu cikin baƙin ciki da tashin hankali", a cewar Jami'in kula da baitul mali Brian E. Nelson a wata sanarwa.

    Ya ƙara da cewa " baitul mali zai ci gaba da amfani da ikonmu wajen tabbatar da masu garkuwa da ƴan ƙasarmu sun fuskanci hukunci".

    A sanarwar ya ce mutanen da aka ƙaƙabawa takunkumin sun taimaka da ɗaukar nauyi da kuma ba da goyon baya a garkuwa da tsare ƴan Amurka a Yammacin Afrika.

    Baitul malin Amurka da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar da suka saka takunkumin sun ce "duka kadarorin da kuma kuɗin ruwan da ake biya a kan kadarorin na ƙungiyoyin da ke Amurka an hana su taba su".

    An hana ƴan Amurka yin mu'amala da mutanen da aka ƙaƙaba wa takunkumin waɗanda ƴan asalin Mali ne da Aljeriya da Burkina Faso da Mauritania.

    Takunkumin yazo ne yayin da yankin Sahel na Afrika ta yamma ke yaƙi da ta'addanci daga ƙungiyoyin masu alaƙa da ƙungiyar IS da al-Qaeda.

  15. Ofishin kare haƙƙin bil'adama na MDD na nuna shakku kan azabtarwa

    Shugaban ofishin kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya na yankin Falasdinu ya ce ba shi da ƙwaƙƙwarar shaida da ke nuna cewa an ɗaure hannayen gawarwakin da aka gano a katafaren kabari a harabar wani asibiti a Gaza.

    Ajith Sunghay ya shaida wa BBC cewa duk da dai ya ga hotunan gawarwakin da aka daure masu hannu, amma wannan kadai bai cika mizanin hujjojin da Majalisar Dinkin Duniya ke bukata ba.

    Hukumar tsaro ta Civil defence a Gaza ta ce ta gano gawarwaki sama da dari uku a karkashin harabar asibitin Nasser da ke Khan Younis.

    A farkon makon nan ne ofishin hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva ya bayyana cewa an ɗaure hannayen wasu gawarwakin, lamarin da ke nuni da babban take hakki a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

  16. An kama iyalin da ake zargi da cin zarafin matashiya kan zuwa coci a Uganda

    Hukumomi sun kama mutum bakwai musulmai ƴan gida ɗaya a gabashin Uganda saboda zarginsu da cin zarafin wata matashiya ƴar shekara 18 da ta halarci taron addu'a a coci.

    Rahotanni sun ce kawun matashiyar ya yi mata bulala 100 da sanda yayin da kawunnanta biyar suka danne ta a ƙasa, kamar yadda shafin labarai na Nile Post ya wallafa.

    Bidiyo ya nuna ana dukan matashiyar da kara wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta abin da ya janyo suka daga ƴan Uganda.

    Zuwa yanzu, iyalin ba su ce komai ba kan batun.

    An kama kawunnan matashiyar tare da goggonta wadda a hannunta take zama, in ji ƴan sanda.

    Za su ci gaba da zama a tsare har zuwa lokacin kammala bincike, in ji kakakin ƴan sanda na riƙo a yankin, Samuel Semewo.

    Babu bayani kan tuhumar da za a yi masu amma mista Semewo ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Nile Post cewa abin da ake zargin su da aikatawa cin zarafi ne.

    Wani wakilin hukumar da ke kula da harkokin musulmai a ƙasar ya ce abin da ake zargin iyalin da aikatawa cin zarafi ne kuma ya saɓa da ƙa'idar addini, kamar yadda Daily Monitor ta ruwaito.

  17. An rufe rassan bankin UBA shida a Kaduna

    ..

    Hukumar tattara kuɗin shiga a jihar Kaduna ta rufe rassa shida na bankin UBA saboda zargin kaucewa biyan harajin naira miliyan 14.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kai samamen ne bayan da hukumar gudanar bankin ta gaza mutunta takardun da aka aike masu.

    Tawagar hukumar, bisa jagorancin sakataren hukumar gudanarwa da mai bai wa hukumar shawara kan shari'a, Barista Aysha Muhammad, ta rufe rassan bankin tare da tallafin jami'an tsaro.

    Barista Aysha ta ce "bisa sashe na 104 na dokar haraji, hukumar ta samu izinin kotu ta ƙwace tare da gano naira miliyan 14 da ɗoriya na kuɗin haraji da ba a biya ba tsakanin 2019 zuwa 2021 daga bankin da ke tafiyar da harkokinsa a Kaduna."

    Zuwa yanzu dai bankin bai ce komai ba game da rufe wasu sassan nasa sannan hukumar bankin a Kaduna ba ta ce komai ba da aka tuntuɓe ta.