Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran nahiyoyin duniya na 05/05/2024

Takaitacce

  • Jam'iyyar da ke mulki a Togo ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki
  • Shugaban babbar jam'iyya adawa a Burtaniya ya bukaci a gaggauta shirya babban zabe
  • 'An bar Arsenal da addu'a yayin da City ke ta cin wasanninta'
  • Yankin Rio Grande do Sul na Brazil ya shiga cikin masifar ambaliya
  • An rufe yaƙin neman zaɓe a Chadi
  • 'Ya kai wata bakwai Amurka da Faransa suna rokon kafa sansanin soji a Najeriya'
  • Ana fuskantar matsananciyar yunwa a arewacin Gaza - MDD
  • A yau ake saran cigaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza
  • Bellingham ne ya ƙarfafawa Madrid gwiwa ta lashe La Liga

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Asai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da akwo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Al jazeera ta zargi Isra'ila na yunƙurin ɓoye gaskiyar abin da ke faruwa a Gaza

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafar yaɗa labaran Aljazeera ta bayyana shirin gwamnatin Isra'ila na hana ta gudanar da aiki a ƙasar, a matsayin yunƙurin ɓoye gaskiyar abin da ke faruwa a Gaza.

    Aljazeera - wadda ke da hedikwata a Qatar - ta kasance tashar kasar waje guda ɗaya tilo da ke fitar da rahotannin yadda ake fafata yaƙin a filin daga.

    Mahukuntan Isra'ila dai sun zargi tashar da zama kakakin Hamas.

    Shugaban Ofishin Aljazeera a Isra'ila ya ce ''wannan mataki ne mai hatsari, Isra'ila na ikirarin dimukuradiyya amma kuma a lokaci guda ta hana yan jarida yin aiki yadda ya kamata''.

    Tun daga lokacin da firaiminista Benjamen Netanyahu ya sanar da ɗaukar matakin hana Aljazeera aiki, yan sandan Isra'ila suka yiwa ofishin ƙawanya a birnin Qudus.

    Tuni dai kamfanonin tauraron ɗan Adam da ke baza shirye-shiryen Aljazeera suka dakatar da yaɗa ayyukanta a Isra'ila nan take.

  3. Hamas ta kai hari Kerem Shalom da ke tsakanin Isra'ila da Gaza

    Sashen kula da makamai na Kungiyar Hamas ya ce ya kai hari Kerem Shalom da ke tsakanin Isra'ila da Gaza, har wasu yan Isra'ila sun jikkata.

    Isra'ila ta ce ta rufe wa matocin dakon kayan agaji hanya bayan hari da makamai masu dogon zango daga birnin Rafah da ke Kudancin Gaza.

    Hamas ta ƙara da cewa sansanin sojojin Isra'ila ta yi niyyar kai wa harin.

    Firaiministan Isra'ila Benjamen Netanyahu ya ce ko an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ko ba a cimma ta a, sai sojin Isra'ila sun kai hari birnin Rafah, inda miliyoyin Falasɗinawa da yaƙi ya raba da muhallansu suka fake.

  4. Kotu ta ɗaure tsohon manajan banki shekara 121 saboda zambar kuɗi

    .

    Asalin hoton, EFCC

    Wata kotu a Anambra ta yanke wa tsohon manajan bankin FCMB, Nwachukwu Placidus, hukuncin ɗaurin shekara 121 saboda samunsa da laifin zambar kuɗaɗe.

    Kotun ta samu tsohon manajan da laifin karkatar da wasu kuɗi kimanin naira miliyan 112.1 da wani kwastoma ya kawo da nufin sanya masa a asusunsa.

    Cikin wata sanarwar da Hukumar Yaƙi da cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC), ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, ta ce an gurfanar da mista Placidus a gaban kotun ne ranar 27 ga watan Maris ɗin 2018.

    An tuhume shi da laifuka 16 da suka haɗa da sata da yin ƙarya a furucinsa da kuma a takardu.

    Sanarwar ta ce a lokacin da Placidus ke aiki a matsayin manajan bankin FCMB reshen birnin Onitsha, ya karɓi kuɗi daga wani kwastoman bankin da nufin sanya masa kudin asusun ajiyarsa, amma sai mista Placidus ya karkatar da su.

    Bayan gudanar da bincike ne, EFCC ta gano cewa Placidus ya karkatar da kuɗin domin amfanin kansa, inda kuma ya gabatar da takarda ta ƙarya da ke nuna shaidar saka kuɗin a asusun kwastoman, kan hakan ne kuma kotun ta ɗaure a gidan gyaran hali.

  5. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga a Neja da Borno

    .

    Asalin hoton, NAF

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakarunta sun samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama a jihohin Borno da Neja.

    Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar, Edward Gabkwet ya ce cikin jerin wasu hare-hare ta sama da dakarun rundonin Hadin Kai da Whirl Punch suka ƙaddamar a jihohin biyu ya samu narasar lalata wasu shirye-shiryen 'yan bindigar.

    Edward Gabkwet ya ce a ranar 3 ga watan Mayu dakarun ƙasar sun kai hari a garin Chinene da ke yankin tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno.

    Ya ce dakarun sojin ƙasar sun ga 'yan bindigar na wani taro da ake kyautata zaton tattaunawa suke yi a lokacin da jirgin sojin ya kai musu hari tare da kashe su.

    “Haka kuma a garin sojojinmu sun hangi wasu motocin yaƙi bakwai da ake zaton na 'yan bindigar ne a ƙarƙashin wata bishiya, nan take su ma aka kai musu hari tare da lalata su'', in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa “bayanan da muka samu bayan hare-haren sun nuna cewa an samu nasara, domin kuwa hare-haren sun halaka 'yan bindigar da damarsu tare da lalata kayayyakinsu.''

    Haka kuma sojojin sun ce sun kuma samu nasarar kai hari a ƙauyen Allawa da ke kusa da Shiroro a jihar Neja, inda aka kashe 'yan bindiga masu yawa.

    Gabkwet ya ce sojojin sun kai harin ne bayan samun bayanan sirri kan ƙaura da 'yan bindigar ke yi zuwa ƙauyen, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyen da dama tururuwar ficewa daga yankin sakamakon fargabar da suke yi.

  6. Shugaban China na ziyara a Faransa

    Shugaban ƙasar China Xi Jinping ya isa Faransa a ziyararsa ta farko ga wata ƙasar EU cikin shekara biyar.

    Ziyarar na zuwa ne lokacin da ake tsaka da rashin jituwar kasuwanci, Tarayyar Turai na duba yiwuwar ƙara wa motocin China masu amfani da lantarki kuɗin haraji, ita ma Beijing ta yi irin wannan kan kayayyakin da za a shigar mata.

    Ana sa ran za a shawo kan wasu daga cikin matsalolin rikicin duniya idan Mista Xi ya tattauna da shugaba Macron da Usula von der Leyen a ranar Litinin.

    Faransa na son China ta matsawa Rasha ta dakatar da yaƙin da take yi da Ukraine - wani yanayi da masu sharhi ke kanin akwai lauje cikin naɗi kansa.

  7. Karin sojojin Rasha da kayan aiki sun isa Nijar

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafafen yaɗa labaran Nijar sun ce ƙarin jiragen dakon kaya ɗauke da kayan aikin soji sun isa Yamai babban birnin ƙasar.

    Rahotanni sun ce wannan yana cikin wasa sabuwar yarjejeniyar tsaro da aka cimma tsakanin Nijar da Moscow.

    Kazalika jirgin ya kawo abinci ga rukunin farko na sojin Rasha da suka je kasar a watan jiya- wadanda ake kira 'yan sanda Afrika.

    Alaƙar da ke tsakanin Amurka da Faransa ta yi tsami ne tun bayan juyin mulkin da aka hambarar da gwamnatin farar hula a bara.

    Amurka ta amince za ta fara janye dakarunta dubu daya daga sansaninsu da ke cikin Nijar, mafi yawansu suna arewacin kasar.

    Nijar da wasu ƙasashen yankin Sahel na fama da matsalar masu ikirarin jihadi na tsawon shekaru.

  8. Isra’ila za ta rufe ofishin Al Jazeera daga kasarta

    A

    Asalin hoton, Reuters

    Majalisar Isra'ila ta yanke shawarar rufe duk wasu ayyukan gidan talabijin na Al Jazeera daga ƙasarta kan dalilin cewa tana barazana ga lamuran tsaronta.

    Matakin zai haɗa da rufe ofishin gidajn talabijin ɗin da ke Isra'ila, da kwace kayan aikin yaɗa labaranta, da yanke duk wasu wayoyin tashar daga tauraron ɗan adam ɗinta sannan ta toshe shafin tashar na Intanet.

    Manajan tashar ya bayyana matakin a matsayin mai cike da haɗari, inda ya ce tawagar tashar ta ɓangaren shari'a na shirya matakin da za ta ɗauka.

    Tun tuni hukumomin Al jazeera suna sukar tashar wadda ke samun goyon bayan Qatar da nuna kin jinin Isra'ila.

    Wakilan Al Jazeera na daga cikin 'yan jarida ƙalilan da ke cikin Gaza suke kawo rahoton yakin da ake yi.

  9. Bellingham ne ya ƙarfafa wa Madrid gwiwa ta lashe La Liga

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid ta zama gwarzuwar La Liga ta wannan shekarar a ranar Asabar, bayan ta doke Cadiz da ci 3-0 a Bernabeu kafin daga bisani Barcelona ta sha kashi da ci 4-2 a hannun Girona.

    Wannan shekara ce mafi birgewa ga kungiyar Carlo Ancelotti, wadanda suka yi rashin nasara daya a duka kakar bana - a hannun abokan hamayyarsu Atletico Madrid a watan Satumba - kuma daga nan babu wanda ya sake cinsu a wasannin 28 da suka buga.

    BBC ta duba labarin nasararsu wadda za zata iya ƙarewa da lashe Champions shi ma.

    Amma mai karatu watakila ya yarda da cewa nasarar tana bayan kokarin da Jude Bellingham yake yi ne a ƙungiyar.

    Tun a ranar wasansa na farko ya ci kwallo, ya ci kwallon da ta bai wa Madrid nasara, sau biyu yana cin kwallo a mintinan ƙarshen wasannin El Clasico wanda hakan ya sa ya zama ɗan wasan La Liga na wannan shekarar, wani abu da babu mai ja.

    Shekararsa ta farko a Spain cike take da nasara.

  10. A yau ake saran cigaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza

    r

    Asalin hoton, Reuters

    A yau ake saran cigaba da tattaunawar tsagaita wuta a Gaza da sakin fursunonin Isra'ila, bayan masu shiga tsakani a jiya Asabar sun gaza cimma daidaito a birnin Alkahira na Masar.

    Wakilan Hamas na cewa ba za su amince da duk wata yarjejeniya da ba za ta kawo karshen yakin Gaza ba.

    Yayinda Jami'in gwamnatin Isra'ila ya shaida wa 'yan jarida cewa ba za su bayar da tabbacin hakan ba.

    Isra'ila har yanzu dai ba ta tura wakilanta wajen tattaunawar Alhakira ba, tana mai cewa har sai ta fahimci inda Hamas ta dosa a kan tayin da suka gabatar.

  11. Ana fuskantar matsananciyar yunwa a arewacin Gaza - MDD

    A

    Shugabar hukumar abinci ta MDD ta ce ana fuskantar matsananciyar yunwa a arewacin Gaza.

    Cindy McCacain ta shaida hakan ne a lokacin tattaunawa da wata tashar Amurka, inda ta kara da cewa matsalar da ake ciki na yaɗuwa har zuwa kudanci.

    Ms McCain ta ce hukumarsu na cigaba da rokon a tsagaita wuta domin a samu damar kai agaji ta dukkanin hanyoyin ruwa da kasa.

    Wani mazaunin Gaza ya ce tabbas suna fuskantar karancin taimako, sannan duk abin da suke samu baya isansu, sun fi wata biyu ba sa samun ganyayyaki.

    Kafin wannan lokaci dama dai MDD ta yi gargardin cewa sama da kashi 70 cikin 100 na al'ummar Gaza za su fada cikin yanayi na bala'in yunwa a watan Mayu.

  12. 'Ya kai wata bakwai Amurka da Faransa suna rokon kafa sansanin soji a Najeriya'

    A

    Asalin hoton, Facebook

    Wasu mutanen Arewacin Najeriya da ke nuna kishin ƙasar sun nuna fargabarsu kan rokon da Amurka da Faransa ke yi na neman kafa sansanin soji a Najeriya.

    Cikin wata tattaunawa da BBC Farfesa Jibirn Ibrahin wanda shi ne mai magana da tawagar wadannan mutane ya ce akwai tashin hankali bai wa waɗannan kasashe wurin zama a Najeriya.

    "Yanzu yakai wata bakwai muna jin ƙishin-ƙishin ɗin cewa Amurka da Faransa na ta rokon a basu wuri su kafa sansanin sojinsu. To yanzu maganar ta ƙara ƙarfi shi yasa muka fito muke ba da shawara ka da a sake a yi hakan.

    " Wannan haɗari ne ga ƙasarmu bai kamata sojojin Faransa da na Amurka su kafa sansani ba a ƙasarmu," in ji Farfesa Jibrin.

    Yace an fatattaki sojojin ƙasashen biyu daga Nijar da Mali da Burkina Faso saboda gazawa suka koma Chadi nan ma aka kore su to yanzu suna neman inda za su zauna ne su riƙa sanya idanu kan wadannan kasashe.

    Ya ce gwamnatocin ƙasashen da suka kori sojojin Faransan da Amurkan, sun ce sun gaza ne a kan cimma manufar da aka girkesu a kai ta yaki da masu iƙirarin jihadi a don haka suka sallame su.

    To ko Najeriya suka zo "ba za su taimakawa matsalar tsaro ba sai dai ta sake taɓarɓarewa," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa cikin yarjejeniyar da suka ambata suke so a cimma akwai maganar cewa "babu mai bincikar abin da suka shigo da shi Najeriya. Duk wani laifi da suka yi wa 'yan Najeriya babu mai tuhumarsu.

    "Babu wanda zai iya shiga sansaninsu. Kawai ƙasa suke so su kafa a cikin ƙasarmu. Kuma mu ƙasa ce mai cikakken 'yanci," in ji Farfesa.

  13. An rufe yaƙin neman zaɓe a Chadi

    B

    An rufe gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da ake yi a Chadi, kwana guda gabanin fara babban zaɓen ƙasar.

    Za a gudanar da zaɓen ne a gobe Litinin, wata rana da aka dade ana jira domin mayar da ƙasar kan turbar dimokradiyya.

    A
    A

    Kimanin makonni uku kenan da 'yan takarar shugaban ƙasar su 10 ke ta yawon neman zaɓe a fadin kasar, domin shaidawa magoya bayan shirinsu na ciyar da ƙasar gaba ta fuskar rayuwa da siyasa da kuma tattalin arziki.

    Da yake rufe nasa yaƙin neman zaɓen a N'Djamena, jagorar mayar da ƙasar ga gwamnatin farar hula Mahamt Deby ya shaida wa magoya baya da jam'iyyun kawance cewa akwai kwarin gwiwa kan sakamakon zaɓen.

    A
    A

    "Zan iya cewa akwai gamsuwar nasararmu a ranar 6 ga watan Mayu tabbatacciya ce," in ji Janar Mahamat Deby.

    Ya kuma jaddada sabonta ƙawancensu da ƙasashen da mutunta Chadi a matsayin ƙasa mai cikakken 'yanci.

    L
    A
    A
  14. Yankin Rio Grande do Sul na Brazil ya shiga cikin masifar ambaliya

    A

    Gwamnan jihar Rio Grande do Sul ya ce ana cikin yanayin fuskantar ambaliyar da ba a taba ganin irinta ba a yankin na Brazil.

    Kusan mutum 60 aka tabbatar sun mutu sannan dubbai sun rasa matsugunansu bayan kogi tayi ambaliya da daidaita birnin, Porto Alegre.

    Yanzu an umarci illahirin al'ummar yanki su fice.

    Wani mazaunin yankin ya nuna matukar damuwa kan yada ambaliyar a koda yaushe ke karuwa da sake jefa su a cikin barazana.

    Gwamna Eduardo Leite, ya ce dole ne a kaddamar da gagarumin shirin sake gina jihohin kasar da dama.

    Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva, zai ziyarci yankunan da ambaliyar ta shafa a wannan Lahadin.

  15. 'An bar Arsenal da addu'a yayin da City ke ta cin wasanninta'

    B

    Asalin hoton, BBC Sport

    Mun kusa kammala wasannin gasar Premier kakar bana.

    Kamar yadda kocin Manchester City Pep Guardiola yake yawan faɗa: "mako ɗaya ne ya rage, wasanni uku suka yi saura. Maki tara muke buƙata mu lashe gasar. duk abin da ya yi kasa da tara, bakwai ko shida ko ƙasa da haka Arsenal za ta ci Premier.

    Guardiola ba shi da kwarin gwiwa kan Manchester United wadda Arsenal za ta ziyara a ranar 12 ga watan Mayu, ya fi sa ran Gunners za ta cinye ta.

    Amma dama bai kamata a ce ya yi tsammanin United za ta zamarwa Arsenal matsala ba.

    Idan City ta lashe duka wasanninta uku na ƙarshe za ta shiga wani littafin tarihi, Ƙungiya ta farko da ta lashe Premier sau hudu a jere a tarihi.

    A wasan da ta buga na karshe ta doke Wolves ne inda Haaland ya ci kwallo hudu rigis.

    Yaznu kuma za ta Fullham, kungiyar da City ta ci sau 15 a jere ba tare da wata matsala ba.

    Ta doke West Ham a gida. Kuma rabon da City ta ko canjaras da Hammers a Etihad tun 2016 da Guardiola ya zo.

  16. Shugaban babbar jam'iyya adawa a Burtaniya ya bukaci a gaggauta shirya babban zabe

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban babbar jam'iyya adawa a Burtaniya ya bukaci firaminista Rishi Sunak ya gaggauta shirya babban zabe cikin hanzari bayan masu kada kuri'a sun juyuwa Conservatives baya a zaben kananan hukumomin da aka gudanar.

    Keir Starmer ya ce mutane sun gaji da mulkin 'yan conservatives inda a yanzu suke son ganin sauyi.

    Ya ce sakon da ke bayyane a wannan zabe ba boyayye abu ba ne, wanda shi ne na karshe kafin babban zabe, na nufin babu abin da zai sauya kuma an gaji.

    Jam'iyyarsa ta Labour tayi nasarar lashe kujeru 10 cikin 11 na magadan gari a ranar Alhamis, da suka hada da na birnin Landan da West Midlands, sannan sun samu kujerun kansiloli kusan 200.

    Mista Sunak ya ce babu shaka basu ji dadin wannan sakamako ba, sai dai ba zasu karaya ba za su cigaba da gwagwarmaya da Labour.

  17. Jam'iyyar da ke mulki a Togo ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki

    A

    Asalin hoton, .

    Jam'iyyar da ke mulki a Togo ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki da gagarumin nasara, wanda hakan zai bai wa shugaba Faure Gnassingbe damar cigaba da zama a mulki.

    Sakamakon wucin-gadi da aka fitar ya nuna jam'iyyar UNIR ta samu kujeru 108 cikin 113 da ake da su a majalisa.

    Kuma dama dokokin sabon kudin tsarin mulkin kasar da aka yiwa kwaskwarima a watan daya gabata, majalisa ce ke da hurumin zaben shugaban gwamnati, sauyin da masu adawa suka yi alla-wadai da shi, tare da bayyana cewa wani salo ne na bai wa iyalan Gnassingbe damar cigaba da mulki na har abada.

  18. Barka da hantsi

    Masu bibiyar wannan shafi Buhari Muhammad Fagge ke fatan mun wayi gari lafiya.

    Ku kasance da mu a wannan yini domin kawo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya har ma da nahiyar Afrika baki daya.