Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi mai albarka.

    Mu haɗu da ku gobe Juma'a da safe don samun wasu cikakku da suka shafi rayuwarku.

    Umar Mikail ne ke muku fatan mu zama lafiya.

  2. Ukraine ba ta makara ba wajen kare kan ta daga Rasha - Jens Stoltenberg

    Jens Stoltenberg

    Shugaban ƙawancen tsaro na Nato ya ce Ukraine ba ta makara ba wajen samun galaba a kan Rasha ba, yayin da yake maraba da sabon shirin tallafin soji da Amurka za ta bai wa Kyiv.

    Jens Stoltenberg ya amince da cewa mambobin Nato sun kwashe watanni da dama ba tare da sun bai wa Ukraine goyon bayan da suka yi alkawari ba.

    Ya ce jinkirin da aka samu ya sa Rasha ta samu nasarar mamaye wasu yankuna.

    Fadar White House ta ce wasu kayan agajin sojin Amurka za su isa Kyiv nan da ƴan kwanaki.

  3. Mun shawo kan matsalar da ta jawo layuka a gidajen mai - NNPCL

    Layin man fetur

    Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya ce ya shawo kan matsalar da ta jawo dogayen layuka a gidajen mai da ke faɗin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin yau Alhamis, NNPCL ya ce an samu matsalar ne saboda "ɗawainiyar wajen jigilar man".

    "NNPCL na tabbatar da cewa wahalar da ake sha wajen samun man fetur a wasu sassan Najeriya ta faru ne saboda matsalar da aka samu wajen jigilar man kuma yanzu an kawo ƙarshen ta," in ji sanarwar.

    Kamfanin ya ƙara da cewa ba shi da niyyar sauya farashin man, wanda tuni 'yan kasuwa suka ƙara farashinsa a jihohi.

    Lita ɗaya ta man ta zarta N750 a Abuja babban birnin ƙasar.

    Tun daga farkon makon nan aka fara ganin layuka a gidajen mai a Abuja, inda matsalar ta bazu zuwa jihohi daga baya.

  4. Kamfanin mai na Saudiyya Aramco ne zai ɗauki nauyin Kofin Duniya na 2026

    Giani Infantino

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta sanar da ƙulla yarjejeniyar da za ta bai wa kamfanin mai na Saudiyya, Aramco, damar ɗaukar nauyin gasar Kofin Duniya na 2026.

    Kazalika yarjejeniyar da za ta ƙare a 2027, ta ƙunshi ɗaukar nauyin Kofin Duniya na Mata a shekarar.

    Da ma kamfanin yana da haƙƙin ɗaukar nauyin wasan tseren mota na Formula 1, kuma abokin hulɗar hukumar ƙwallon Cricket ne.

    "Aramco na da tarihi mai kyau wajen tallafa wa wasanni masu nagarta, amma zai mayar da hankali wajen haɓaka wasanni tun daga tushe," a cewar Shugaban Fifa Gianni Infantino.

    Yarjejeniyar na ƙara fito da yadda Saudiyya ke faɗaɗa tasirinta a harkokin wasanni na duniya.

    Wani rahoto da aka wallafa a watan Nuwamban 2023 ya bayyana cewa Saudiyya ta ƙulla yarjejeniya 312 a harkokin wasanni 21.

  5. Kotun Ƙoli za ta ji bahasi kan ko Trump na da kariya daga tuhuma

    ..

    Kotun kolin Amurka za ta saurari bahasi kan ko tsohon shugaban kasar Donald Trump na da kariya daga tuhumar da ake masa kan abubuwan da ya aikata a lokacin da yake kan karagar mulki.

    Sakamakon dai zai tabbatar da ko zai fuskanci shari'a kan zargin da ake masa na yunkurin juya kayin da ya sha zaben shugaban kasa na 2020.

    Mista Trump ya ce ba zai iya fuskantar tuhuma kan laifukan da ya yi a lokacin da yake kan karagar mulki ba.

    Ana tsammanin yanke hukunci kan batuna watan Yuni.

    Hukuncin da za a yanke kan wannan batu ba zai shafi shari'ar da ake tuhumar sa da aikata laifi ba a halin yanzu a New York , inda ake tuhumarsa da laifin biyan kudi ga tauraruwar fina-finan batsa Stormy Daniels.

  6. Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram uku a Kamaru

    Sojojin Kamaru

    Dakarun haɗin gwiwa a yankin arewa mai nisa na Kamaru sun ce sun yi nasarar kashe wasu mutum uku da suke zargin 'yan ƙungiyar Boko Haram ne.

    Dakarun sun yi musu kwanton-ɓauna ne a birnin Mora, wurin da suke ta kai hare-hare a baya-bayanan.

    Lamarin ya faru ne a lokacin da hukumomi a Kamaru ke murnar mayar dawowar harkokin kasuwanci da zirga-zirgar jama’a tsakanin Kamaru da Najeriya.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton da Mohaman Babalala ya aiko mana daga Yaounde:

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton:
  7. EU na fuskantar gagarumin haɗari nan da shekara 10 – Macron

    Macron

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi gargaɗin cewa Tarayyar Turai na fuskantar haɗari sosai a cikin shekara 10 masu zuwa a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankuli a duniya.

    Mista Macron ya ce akwai buƙatar yin watsi da abin da ya kira rashin wayewa kan tsaro da kasuwanci inda yake ba da shawarar a bunƙasa hanyoyin dogaro da kai.

    Ya ce samar da makamai a Turai na tafiyar hawainiya, kuma tsarin tattalin arzikinta ba mai ɗorewa ba ne.

    Ya ce "Babban haɗarin da ke tattare da tsaron Turai a yanzu shi ne yaƙin da ake yi a Ukraine, abin da ke damun mu shi ne kar a bar Rasha ta yi nasara a wannan yaƙi na ta’addanci da take yi da Ukraine.

  8. Ƴansanda sun kashe 'ƴanbindiga' takwas a Bauchi

    ..
    Image caption: CP Auwal Musa Muhammad, kwamishinan ƴan sanda na jihar Bauchi

    Ƴan sanda tare da haɗin gwiwar ƙungiyar mahauta a Bauchi sun kashe mutum takwas da ake zargin masu garkuwa da mutane ne yayin musayar wuta a kusa da iyakar jihar da Filato.

    Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta jihar Bauchi SP Ahmed Wakil ya bayyana wa ƴan jarida a jihar a ranar Alhamis cewa ƴan sanda sun samu nasarar ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su don karɓar kuɗin fansa.

    Sanarwa da mai magana da yawun hukumar ya fitar ta bayyana cewa "Jami'an na ƴan sanda da aka kawo daga offisoshin ƴan sanda na Gumau da Tilde da Tulu sun haɗu da masu garkuwa da mutane tare da makamansu yayin da suke bakin aikinsu na tabbatar da tsaro inda suka yi musayar wuta da ya yi sanadiyyar kashe masu garkuwar huɗu.

    "Biyu daga cikin waɗanda ake zargin da suka mutu daga bisani sun amsa laifin garkuwa da mutane da dama a Bauchi da Filato da ya haɗa da mummunan kisan gillar da aka yi wa maigarin Ruruwai a garin Lame dake ƙaramar hukumar Toro.

    "Yayin musayar bindiga tsakanin jami'an da sauran masu garkuwar da ke gadin mutanen da aka yi garkuwa da su aka sake kashe mutum huɗu cikinsu sannan aka samu ƙwato mutum ukun da ke hannunsu ba tare da biyan kuɗin fansa ba".

    SP Wakil ya yi kira ga al'umomin garuruwan Bauchi da su ba da haɗin kai da jami'an tsaron ta hanyar samar musu da bayanan sirri da za su taimaka wajen shawo kan matsalolin tsaro kafin ma su faru wanda faruwar tasu kan iya samar da mummunan lahani a kan rayuka da kuma dukiyoyi.

  9. Yaƙin Gaza: 'Yansanda sun kama ƙarin ɗaruruwan ɗalibai a Amurka

    Ɗalibai a Amurka

    'Yansanda sun sake kama ɗaruruwan masu zanga-zangar ƙin jinin hare-haren Isra'ila a Zirin Gaza a faɗin jami'o'in Amurka.

    An kama aƙalla mutum 108 a kwalejin Emerson da ke Boston, kamar yadda 'yansanda suka shaida wa kafar talabijin ta CBS.

    Tun da farko, an tsare mutum 93 a jami'ar University of Southern California (USC) da ke Los Angeles bisa zargin aikata laifi.

    Kazalika, masu zanga-zanga sun yi arangama da jami'an tsaro a jami'ar Texas da ke Austin, inda hukumomi suka ce an kama mutum 34 a can ma.

    Ɗalibai
  10. Tsananin zafi ya tilasta rufe makarantu ga yara miliyan 33 a Bangladesh

    ..

    Matsanancin zafi ya tilasta wa yara miliyan 33 daina zuwa makaranta a Bangladesh inda yanayin ya kai maki 42 a ma'aunin salshiyos.

    Makarantu za su ci gaba da zama a rufe har zuwa 27 ga watan Afrilu. Wannan ce shekara ta biyu a jere da hukumomi suka ɗauki irin wannan matakin saboda zafin.

    Philippines da Indiya ma a baya sun ɗauki irin wannan matakin yayin da ake fama da yanayin zafi a nahiyar Asiya.

    "Yara a Bangladesh na cikin ƙasashe mafiya talauci a duniya kuma rufe makarantu saboda matsanancin zafi ya kamata ya zama abin fargaba," in ji Shumon Sengupta, daraktan ƙungiyar Save the Children.

    Bangladesh ɗaya ce cikin ƙasashe mafiya rauni ta fuskar sauyin yanayi.

    A cewar ƙungiyar da ke fafutuka kan sauyin yanayi ta ce tumbasar teku na iya ɗaiɗaita mutum miliyan 35 daga lardunan da ke kusa da teku - kimanin kashi ɗaya bisa huɗu na al'ummar duniya.

  11. Sojin Najeriya sun kashe jagoran 'yan fashin daji a jihar Sokoto

    'Yan bindiga

    Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta kashe wani jagoran 'yan fashin daji a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    Wata sanarwa da ta fitar a shafukanta na intanet ta ce dakarun rundunar da aka tura don yaƙi da ta'addanci ne suka yi nasarar kashe jagoran, wanda ba ta bayyana sunansa ba, a ranar Laraba.

    "Bayan samun bayanan sirri, dakaru sun yi wa gungun 'yanta'addan kwanton-ɓauna a wata mashiga da ke ƙauyen Sarma a ƙaramar hukumar Tangaza, inda suka yi nasarar kashe jagoransu tare da ƙwato bindigar AK-47 da kuma babur," in ji sanarwar.

    A jihar Kaduna kuma, dakarun sojin sun yi nasarar katse hanzarin masu garkuwa da mutane a garin Kafanchan na ƙaramar hukumar Jema'a, sannan suka kama biyu daga cikinsu tare da ƙwato bindiga ɗaya, da harsasai, da kuma babur.

    Kazalika, wani ɗan fashi ya gamu da ajalinsa a wurin duba ababen hawa na Kaskara da ke ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato, lokacin da dakarun suka amsa kiran neman agaji game da gungun 'yanfashi a yankin.

  12. An karrama ƴan asalin Kano da suka yi zarra a gasar Hikayata ta BBC

    ..

    Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta karrama gwarazan gasar ƙagaggun rubutattun labarai ta Hikayata ta BBC Hausa.

    A bikin da aka yi ranar Alhamis, an karrama waɗanda suka yi nasara a gasar ƴan asalin jihar Kano tun daga lokacin da aka fara gasar a 2016 zuwa 2023.

    Hukumar ta kuma karrama sashen Hausa na BBC da ya ɓullo da gasar da ke haɓaka harshen Hausa.

    Ga wasu hotuna na yadda taron ya kasance.

    ..
    ..
    Image caption: Shaidar karramawar da hukumar tace fina-finai ta yi wa BBC
    ..
    ..
    ..
    ..
    ..
    Image caption: Lokacin da ake karrama sashen Hausa na BBC saboda samar da gasar Hikayata ta mata zalla
    ..
    ..
    ..
  13. 'An kashe gomman farar hula a harin ramuwar gayya na sojin Burkina Faso'

    ..

    Sama da farar hula 220 ciki har da yara 56 sojojin Burkina Faso suka yi wa kisan gilla a rana ɗaya a wannan shekarar a cewar ƙungiyar kare haƙƙin bil'dama ta Human Right Watch.

    A hare-haren da sojojin suka kai ranar 25 ga watan Fabarairu, an kashe mutane 179 a ƙauyen Soro da kuma wasu 44 a ƙauyen Nondin da ke maƙwabtaka a cewar wani bincike da ƙungiyar ta yi.

    HRW ta kira kisan kiyashin "ɗaya daga cikin cin zarafi mafi muni da sojoji "suka aikata a ƙasar a gomman shekaru.

    Mahukuntan Burkina Faso ba su ce komai ba kan rahoton.

    A watan da ya gabata lauyan gwamnati Aly Benjamin Coulibaly ya buƙaci shedu domin gano wanɗanɗa ke da hannu a kisan kiyashin inda ya bayyana cewa mutanen da suka mutu sun kai 170.

    Sauran ƴan garin da suka rayu bayan harin sun shaida wa ƙungiyar cewa motoci ɗauke da sojoji kusan sama da 100 sun je ƙauyen Nondin minti 30 bayan masu ikirarin jihadi sun wuce ta kusa da ƙauyen.

    Sojojin sun bi gida-gida suna fito da mutane daga gidajensu.

    "Sai suka haɗa ƴan garin waje ɗaya kafin buɗe musu wuta", a cewar rahoton tare da nuni da bayanai daga shedu da waɗanda suka rayu.

    Ƴan garin da suka yi saura sun ƙara da cewa sojojin sun tsaya kilomita 5, bayan sa'a ɗaya suka fara haɗuwa suna harbin su.

    Sojojin sun harbi waɗanda suka yi ƙoƙarin guduwa ko ɓuya yayin harin a duka ƙauyukan biyu a cewar ƴan garin.

    Kisan kiyashin ana tunanin kamar ramuwar gayya ne daga sojojin bayan sun zargi mutanen garuruwan da taimaka wa masu ikirarin jihadin.

    Hare-haren sun faru bayan wani hari da masu ikirarin jihadi suka kai kusa da sansanin sojoji da ke arewacin yankin Yatenga.

    "Kisan kiyashin farar hula a garin Nondin da Soro ne na baya-bayan nan da sojojin Burkina Faso suka yi a ƙoƙarinsu na daƙile ta'addanci", a cewar Tirana Hassan, shugaban ƙungiyar ta HRW.

    Ƙasar ta sahel na ƙarƙashin mulkin soja bayan sun ƙwace mulki a 2022 inda suka yi alƙawarin kawo ƙarshen ta'addanci.

    Duk da haka ta'addancin ya ci gaba da ƙaruwa inda sama da kashi uku na Burkina Faso ke hannun masu ikirarin jihadin.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da na ƙasa-ƙasa da suka haɗa da Tarayyar Turai da Majalisar ɗinkin duniya sun zargi Burkina Faso da laifin cin zarafin bil'adama a yaƙin da suke yi da ta'addanci ciki har da kisa da ɓatan fararen hula da dama.

  14. Yadda gobara ta tilasta sauya aƙalar jirage a filin jirgin saman Legas

    Hukumar kula da tashoshin jiragen sama a Najeriya, FAAN ta sauya aƙalar harkokin sufurin jirage daga sashe na ɗaya zuwa wani sashe na filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas sakamakon tashin wata gobara.

    A cewar jaridar Leadership, lamarin ya faru ne bayan tashin hayaƙi a matattakalar jirgi a ɓangaren sufurin cikin gida na tashar jirgin.

    Cikin wata sanarwa da daraktar yaɗa labaran hukumar Obiageli Orah ta fitar, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau Alhamis.

    A cewar sanarwar da jaridar ta ruwaito, an samu kashe wutar bayan da jami'an kashe gobarar suka yi hanzarin kai ɗauki.

    FAAN ta ƙara da cewa ana gudanar a bincike domin gano abin da ya haddasa tashin gobarar.

  15. Yadda aka kama masu ƙwacen waya takwas a Kano

    ..

    Rundunar ƴan sanda a jihar Kano ta cafke mutum huɗu da ake zargin sun shahara wajen yi wa mutane ƙwacen waya.

    Wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce an kama mutanen nan take kan titin Airport Road inda kuma aka same su da wayoyin hannu guda bakwai da ankwa.

    Mutanen da ake zargi sun bayyana cewa suna amfani da babur mai ƙafa uku wajen yi wa jama'a ƙwacen waya.

    Rundunar ta ce wani Aminu Sulaiman ya shigar da ƙorafi cewa an sace wayarsa cikin motarsa a wani gidan mai da ke jihar inda bayan samun rahoton, wata tawagar ƴan sanda ta kama mutane uku da ake zargi. An gano wayar da aka sace da kuma babur mai ƙafa uku da suke amfani da shi wajen aikata ta'asar.

    A cewar rundunar a ranar 23 ga watan Afrilu, sun samu kiran waya inda aka sanar da su wasu ɓatagari a kan babur mai ƙafa uku suna far wa fasinja tare da sace wayarsa. An kuma aika tawagar ƴan sanda inda suka fara bincike sannan suka kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi tare da gano wayar da wuƙa mai kaifi daga wajensa.

    Rundunar ta ce ana gudanar da bincike kan mutanen da ake zargi a sashen binciken manyan laifuka sannan daga bisani za a gabatar da su gaban kotu.

    ..
    ..
  16. Mutumin da zai takara da Nicolas Maduro na son inganta lafiya da ilimi a Venezueala

    .

    Dan takarar da jami'iyun adawa a Venezuella ke goyan baya, wanda zai ƙalubalanci shugaban ƙasar mai ci Nicolas Maduro a zaɓen watan Yuli, ya yi kira da a yi zaɓe cikin kwanciyar hankali kamar yadda dimokradiyya ta tanada.

    Edmundo Gonzalez ya ce zai dauki matakan da suka dace wajen magance talauci da tsadar rayuwa.

    Ya ƙara da cewa zai kuma inganta bangaren lafiya da ilimi.

    Wakiliyar BBC ta ce ɗantakarar zai mayar da hankali wajen ba fursinonin siyasa ƴanci tare da bai wa wadanda ke gudun hijira damar komawa gida.

  17. Fafaroma ya bayyana yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza da "ta'addanci"

    ..

    Fafaroma Francis ya ce yana buga wa cocin Katolika da ke Gaza waya kullum domin sanin halin da mutanen yankin ke ciki.

    A cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na CBS, Fafaroma ya ce daruruwan Falasdinawa da ke gudun hijira na fama da rashin abinci.

    Fafaroma ya ce a lokacin da aka kashe Uwa da ƴarta a harabar cocin, rikicin ya tashi daga yaƙi ya koma ta'addanci.

    Manyan mutane da ƙungiyoyi da dama dai na sukar yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza.

  18. Anthony Blinken ya nemi haɗin kan China ga Amurka

    ..

    A yayin da Sakataren harkokin wajen Amurka , Anthony Blinken ya shiga rana ta uku a ziyarar da ya kai China, ya ce kamata yayi Amurka da Chinar su kawo karshen banbance- banbancen da ke tsakaninsu.

    Mista Blinken ya bayyana haka ne a Shanhai, inda ya ce akwai buƙatar a mayar da hankalin kan hakan, yana mai cewa dole ne Amurka da China su hada kai wajen shawo kan matsalar.

    Ya ce muna da nauyin al'ummarmu da duniya akanmu, na ganin mun daidaita alaƙar ƙasashenmu cikin sanin ya kamata.

  19. Labarai da dumi-dumiFursunoni 118 sun tsere daga gidan yarin Suleja

    ..

    Aƙalla fursunoni 118 ne suka tsere daga gidan yarin Suleja da ke jihar Naija mai maƙwabtaka da birnin Abuja, sakamakon ruwan sama mai kama da bakin ƙwarya da ya ruguza wani ɓangaren ginin gidan ranar Laraba.

    Mai magana da yawun hukumar gyaran hali ta birnin Tarayya, Adamu Duza, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis ya ce "sakamakon ruwa kamar da baƙin ƙwarya da ya kwashe awa 24 yana zuba ya lalata wasu sassan gidan yarin inda fursunoni 118 suka tsere."

    To sai dai wani jami'in gidan yarin da BBC ta tattauna da shi ya ce kawo yanzu an samu damar kama fursunonin 10 daga cikin 118 ɗin da suka tsere, inda kuma suke ci gaba da baza komar neman mutum 108.