Yakin Yemen: 'Yan Houthi sun zartar da hukunci kisa kan mutum tara

A dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Sanaa aka harbe mutanen

Majalisar Dinkin Duniya, da Tarayyar Turai, da Birtaniya da Amurka sun yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kisan da 'yan tawayen Houthi suka yi wa wasu maza tara.

A ranar Lahadi ne aka bude wa mazan wuta a dandalin Tahrir da ke tsakiyar birnin Sanaa, wanda daya daga cikinsu yaro ne a lokacin da aka kama shi.

Kotun 'yan tawayen Houthi ce ta yanke musu hukuncin kisa, kan samunsu da hannu a kisan shugaban 'yan tawayen a shekarar 2018 a harin da aka kai ta sama.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya MDD, ya ce hukuncin ya saba wa dokokin kasa da kasa, yayin da Amurka ta ce abin tashin hankali ne, bayan shafe shekaru ana azabtar da mutanen.

Tun a shekarar 2015 Yemen ke cikin yakin basasa, lokacin da 'yan tawayen kabilar Houthi suka karbe iko da yawancin kasar, yayin da Saudiyya da kawayenta suka kaddamar da farmaki kan 'yan Houthi domin tabbatar da gwamnatin Shugaba Abdrabbuh Mansour Hadi.

Yakin ya daidaita kasar, tare da hallaka sama da mutum 130,000, da haddasa abin da Majalisar Dinkin Duniya ta kira aikin jin kai mafi girma da muni da duniya ta fuskanta, bayan janyo sama da mutane miliyan biyar na fuskantar barazanar fadawa matsananciyar yunwa.

Hotunan da suke wadari a shafukan sada zumunta na hukuncin ranar Lahadin, sun nuna wani sojin Houthi na harbin mutanen tara ta bayansu a dandalin Tahrir.

Suna cikin mutum 16 da aka yanke wa hukunci kan zargin leken asiri da kai rahoton abin da Houthi ke ciki, wanda ya kai da kisan shugaban majalisar kolin Houthi wato Saleh al-Sammad, da wasu mutane shida a harin da aka kai ta sama a birnin Hudaydah shekaru uku da suka wuce.

Sauran mutum bakwai din da 'yan Houthi suka yanke wa hukuncin kisa ba tare da sun halarci kotun ba sun hada da yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya Mohammed bin Salman, da tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

Mai magana da yawun Sakatare Janar na MDD António Guterres, ya ce ya damu matuka da bayyana takaici kan kisan mutanen, tare da yin Allah-wadai ga matakin na 'yan Houthi, inda ya ce sam zaman kotun da sauraren karar zuwa yanke hukuncin sun sabawa ka'ida da dokokin kasa da kasa.

Ya yi kira ga Yemen ta rungumi tsari mai kyau wajen gudanar da shari'a da yanke hukunci, da kaucewa zartar da hukuncin kisa.