Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Haruna Kakangi, A'isha Babangida da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Ƙarshen labarai

    Da wannan muka kawo ƙarshen labarai a wannan shafi.

    Sai da safenku.

  2. Daftarin tsagaita wuta ya raba kan Falasɗinawa da Isra'ilawa

    Rafah

    Bayan shafe watanni ana kikikaka, an kai wani muhimmin mataki na neman zaman lafiya a Zirin Gaza.

    Babban Sakataren MDD Antonio Guterres ya ce lokaci ne "yankan shakku ga Falasɗinawa, da Isra'ilawa, da ma yankin baki ɗaya".

    Da alama an samu wata matsya tsakanin akasarin ɓangarori game da abubuwa kamar: za a tsagaita wuta don sakin fursunonin ɓangaren biyu.

    Sai dai akwai rashin jituwa game da cikakken bayanin da abin da zai faru, da lokacin da zai faru, da kuma yanayin da zai faru. Jami'an Isra'ila na cewa ya kamata a sako sojojinta mata da wuri ba kamar yadda aka nema ba.

    Sun kuma ce ya kamata a fayyace kalaman yarjejeniyar ta yadda za a ce mutum 33 da za a fara sakowa dole ne su kasance a raye, sannan sun nuna damuwa kan rashin damar zaɓen irin Falasɗinawan da za a sako daga gidan yari.

    Waɗannan ne abubuwan da za su ci gaba da mamaye tattaunawar da tuni aka fara yin ta a birnin Alƙahira.

    Tun farko Isra'ila ta soki yarjejeniyar da Hamas ta amince da ita, kuma ta afka wa yankin Rafah ta ƙasa tare da tura wakilai wajen tattaunawar.

    Yanzu dai an zuba ido don ganin abin da za a cimma, yayin da Hamas ɗin ta jaddada cewa ba za ta sake sauka daga wani matsayinta ba kuma "wannan ce dama ta ƙarshe da Isra'ila ta samu don dawo da mutanenta gida".

  3. TikTok ya maka gwamnatin Amurka a kotu

    TikTok

    Kamfanin TikTok ya maka gwamnatin Amurka a kotu kan wata doka da za ta hana amfani da shahararriyar manhajar a Amurka har sai dai an sayar da ita ga wani kamfani.

    Dokar da Shugaba Biden ya sanya wa hannu a watan da ya gabata ta zo ne sakamakon fargabar cewa China za ta iya amfani da TikTok don yin kutse a bayanan Amurkawa masu amfani da ita, da kuma amfani da ita wajen yaɗa farfaganda.

    Wakilin BBC ya ce yayin da mutum biliyan ɗaya suke amfani da ita a fadin duniya, Tiktok da kamfanin da ya mallake ta wato ByteDance sun samu kasuwa musamman a tsakanin matasa.

    Haka nan, sun sauya dandalin daga manhajar nishaɗi zalla zuwa inda miliyoyin mutane ke samun labaransu.

  4. Tawagar Hamas ta isa Alƙahira don ci gaba da tattaunawa kan zaman lafiya

    Saleh al-Arour
    Image caption: Saleh al-Arouri na cikin manyan jagororin tattaunawa na Hamas kafin harin Isra'ila ya kashe shi a watan Janairun 2024

    Wata sanarwa da ƙungiyar Hamas ta fitar ta ce tawagarta ƙarƙashin Khalil al-Hayya ta isa birnin Alƙahira na Masar a yammacin yau.

    Tawagar ta isa Masar ne da zimmar "dorawa kan tattaunawa da 'yan'uwa na Masar da Qatar suka fara, da kuma ƙoƙarin cimma yarjejeniyar dakatar da hari a kan mutanenmu a Zirin Gaza", a cewar sanarwar.

    Tun a makon da ya gabata ne tawagar ta Hamas ta fice daga Alƙahira tana mai cewa tattaunaar ta ƙare, kafin daga baya ta bai wa duniya mamakin amincewa da daftarin tsagaita wuta wanda Masar da Qatar suka gabatar.

    Zuwa yanzu Isra'ila ta yi watsi da daftarin amma ta tura tawagarta don lalubo matsaya don cimma yarjejeniyar.

  5. Za mu zafafa hare-hare a Rafah har sai an sako mutanenmu - Isra'ila

    Isra'ila ta ce za ta zafafa hare-hare a Rafah da ke kudancin Gaza har sai ta fatattaki Hamas, ko kuma an sako wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.

    Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce kodayake sabon daftarin tsagaita wuta da Hamas ta amince da shi bai biya bukatun gwamnatinsa ba, za ta ci gaba da tattaunawa.

    "Isra'ila ba za ta iya amincewa da yarjejeniyar da ke barazana ga tsaron 'yan kasarmu ba. Don haka, na umurci tawagarmu da ta je Alkahira cewa su ci gaba da tsayawa tsayin-daka kan sharuɗɗan da suka wajaba wajen sako mutanen da aka yi garkuwa da su," in ji shi.

    Tun bayan da sojojinta suka kutsa Rafah a jiya Litinin, Isra'ila ta ce ta gano hanyoyin ƙarƙashin ƙasa uku tare da kashe mutum sama da 30 da ta yi iƙirarin cewa mayaƙan Hamas ne.

  6. Isra'ila ta faɗa mana farmakinta a Rafah ƙayyadajje ne - Amurka

    John Kirby

    Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka John Kirby ya faɗa wa manema labarai cewa Isra'ila ta tabbatar wa Amurka cewa hare-harenta a Rafah za su mayar da hankali ne kan lalata makaman Hamas.

    Yayin wani taron manema labarai a yau, Mista Kirby ya ce Isra'ilar ta ce za kuma tabbatar ta katse duk wani tallafi da ƙungiyar ke samu.

    Amurka ta sha nuna adawarta kan farmakin Isra'ila a Rafah, inda ta bayyana fargabar rasa rayukan fararen hula da za a samu bayan mutum sama da miliyan ɗaya sun nemi mafaka a yankin.

    Tuni sojojin Isra'ilar suka kutsa, har ma suka ce su ne ke iko da yankin a yanzu.

  7. 'Yanbindiga sun yi garkuwa da mutum bakwai a bayan kashe guda a jihar Ogun

    'Yansandan Najeriya

    Mutum ɗaya ya mutu a jihar Ogun da ke kudancin Najeriya yayin da 'yanbindiga suka yi garkuwa da mutum bakwai, a cewar rundunar 'yansanda a jihar.

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi a kan babban titin Sagamu-Ijebu-Ode.

    Maharan da suka kai kusan bakwai, sun isa wurin ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47, in ji sanarwar da kakakin 'yansanda Omolola Odutola ya fitar a yau Talata.

    Ya ƙara da cewa sun bayyana lamarin a matsayin fashi da makami, da kisan kai, da kuma garkuwa da mutane.

  8. Ƙarin jami'an sojin Rasha sun isa Nijar

    Sojojin Nijar

    Wasu ƙarin jami'an soji masu horaswa na kasar Rasha sun isa Nijar a ranar 4 ga watan Mayu, makonni bayan ƙasar ta karɓi dakaru 100 na rundunar sojin Afirka da na tsaro ta jiragen sama, kamar yadda shafin jaridar ActuNiger ya ruwaito.

    Wannan na zuwa ne daidai lokacin da dangantaka ke kara ƙulluwa tsakanin shugabannin sojojin Nijar da fadar Kremlin ta Rasha.

    A cewar ActuNiger, jirgin sama na sojan Rasha na uku ya sauka a Yamai babban birnin kasar ɗauke da wani gungun jami'an soji masu horaswa, da kayan aiki, da kuma kayan agaji.

    "Sojoji masu horaswa" da Moscow ta aiko ƙarkashin yarjejeniyar hadin-gwiwa ta tsaro za su taimaka wajen horar da jami'an tsaron Nijar don fuskantar "rikitattun kalubale" da dabarun yaki.

    Nijar ta soke yarjejeniyar soji da ta kulla da Amurka, sannan ta kuma kori dakarun Faransa daga kasar.

  9. Rayuwar Falasɗinawa ta ƙara tsada saboda rufe mashigar Rafah

    Falasɗinawa

    Rufe mashigar Rafah ta fara shafar rayuwar mazauna Zirin Gaza bayan Isra'ila ta ce ita ke iko da yankin a yanzu.

    Raed Asfou, wani Bafalasɗine da aka raba da muhallinsa a Khan Younis ya ce farashin kayayyaki sun fara tashi. Ya ce iyakar Rafah ce "ruhin" Zirin Gaza.

    "Ta nan ake shigar da agaji, ta nan ne kayan abinci ke shiga. Ta nan ake shigo mana da komai," a cewarsa.

    "Jim kaɗan bayan sun bayyana rufe iyakar, farashin sikari ya tashi...rayuwa ta ƙara tsada. Tana ƙara tsada. Me za mu yi yanzu?"

  10. Yarjejeniyar da muka amince ce dama ta ƙarshe ga Isra'ila - Hamas

    ..

    Wani babban jami'i a ƙungiyar Hamas ya ce zuwan da wakilansu za su yi birnin Alƙahira domin tattaunawa kan yarjejeniyar tsagaita wuta ita ce dama ta ƙarshe ga Isra'ila wajen sakin mutanenta da Hamas din ta yi garkuwa da su.

    Da yake magana ga kamfanin dillancin labari na AFP, jami'in ya ce masu sasantawa na Hamas da farko sun soke tafiya zuwa Alƙahira daga Qatar.

    Jami'in na Hamas ya ce nan gaba kaɗan za su tafi zuwa Alƙahira.

    Harwayau, jami'in na Hamas ya ce ƙudirin firaiministan isra'ila, Benjamin Netanyahu na shiga Rafah ya nuna cewa Netanyahu da sojojin Isra'ila suna son waɗanda ake garkuwar da su su mutu.

    "Wannan ita ce damar Netanyahu da iyalan Yahydawa fursunoni ta ƙarshe domin mayar da yaransu gida." In ji jami'in.

    Hamas ta yi garkuwa da mutum 252 lokacin harin da ta kai na ranar 7 ga watan Oktoba, sannan kuma ba a san inda mutum 128 suke ba. Isra'ila ta ce tana kai hare-hare ne "a Rafah da manufar neman mutanen da aka yi garkuwa da su a maɓoyar 'yan ta'adda."

  11. Sanatocin Arewa sun soki jan ƙafar da ake yi wajen aikin hanyar Kano zuwa Maiduguri

    BBC

    Sanatocin arewacin Najeriya sun nemi gwamnatin Najeriya ta farfado da aikin hanyar da ta tashi daga birnin Kano zuwa Maiduguri na jihar Bornon wanda aka bayar da kwangilar aikinsa tun lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo.

    Sanata mai wakiltar mazaɓar Kano ta Kudu, Abdurrahaman Kawu Sumaila ne ya gabatar da kudurin wanda ya nemi a mayar da hankali kan titin da ya tashi daga Gaya zuwa Wudil.

    A lokacin da ya bayar da tasa gudumawar, Sanata Muhammad Danjuma daga jihar Gombe ya nemi a mayar da hankali wajen kammala hanyar musamman ɓangaren da ya tashi daga Benishek zuwa Maiduguri wanda ya ce kusan kullum sai an rasa rayuka a kan titin.

    Sanata Kaka lawan da yake wakiltar Borno ta tsakiya ya ce da rana ido na ganin ido ana iya yin fashi a kan wannan hanyar ta Benishek zuwa maiduguri, shi ya sa ya nemi majalisa ta matsa ƙaimi wajen ganin an kammala aikin.

    Ya ce ita kadai ce hanyar da ta hada arewa maso gabashin Najeriya da yankuna masu yawa, ta kuma ratsa jihohin Bauchi kano Jigawa Yobe da kuma Borno.

    Mataimakin shugaban Majalisar dattijai, Sanata Barau Jibrin ya goyi bayan wannan kuduri yana cewa "ya kamata a sake duba kwangilar da aka bayar".

    Babbar hanyar wadda ta tashi daga Kano zuwa Maiduguri na daga cikin manyan ayyukan gwamnatin tarayyar Najeriya da ake ganin sun daɗe ana jan ƙafa wajen kammala su.

  12. Ƴan sanda na bincike kan bidiyon cin zalin ɗalibar jami'ar jihar Ekiti

    ..

    Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta ce ba ta da masaniya kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna yadda wata dalibar jami’ar ilimi da kimiya da fasaha ta Bamidele Olumilua, Ikere take cin zalin wata ɗaliba ƴar uwarta a wani wuri mai kama da daji.

    Rundunar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin sada zumuntarta na X.

    "Wannan sanarwar na son sanar da ƴan Najeriya da kuma mutanen jihar Ekit cewa rundunar ‘yan sandan jihar ba ta da masaniya kan wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna wata ɗalibar jami'ar jihar, BOUESTI tana cin zalin ɗaliba ƴar uwarta." in ji sanarwar.

    "Rundunar ta bayyana irin wannan cin zalin a matsayin rashin mutuntaka kuma ba za a yarda da shi ba."

    Rundunar ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Ekiti, CP Akinwale Kunle Adeniran ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin domin tuni ya umurci kwamandan yankin Ikere da ya haɗa kai da hukumar gudanarwar jami'ar tare da tabbatar da an gano wadda ta aikata wannan laifin don fuskantar sakamakon shari'a.

    Sanarwar ta kuma yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu kuma su guji daukar doka a hannunsu domin ana daukar matakan da suka dace.

    View more on twitter
  13. Majalisar dokoki ta gayyaci Dangote da BUA kan tsadar siminti

    ..

    An bai wa Dangote da BUA da IBETO da sauran masu ruwa da tsaki wa’adin kwanaki 14 da su gurfana a gaban kwamitin hadin gwiwa na Majalisar dokoki kan tsadar farashin siminti a kasar.

    Hakan ya biyo bayan gazawar da kamfanonin da wasu suka yi wajen gurfana wajen zaman binciken da aka yi ranar Talata.

    An dai kafa kwamitin hadin gwiwar na majalisar dokokin wanda ya kunshi kwamitocin majalisar masu kula da ma’adanai da kasuwanci da masana’antu da kuma ayyuka na musamman domin ‘binciken ƙarin farashin siminti a Najeriya ba bisa ka’ida ba da kamfanonin yin simintin suka yi.

    Majalisar ta kuma gayyaci ministan ma’adanai na kasa, Dele Alake, da ya gurfana gaban kwamitin bayan ya kasa bayyana a ranar Talata.

    Majalisar ta kuma ba da umarnin cewa ministan ya bayyana ranar Talata, 21 ga Mayu yayin kuma da Dangote da BUA da IBETO da dai sauransu su kuma za su bayyana a ranar Litinin, 20 ga Mayu, 2024.

  14. CBN ya buƙaci masu POS su yi rajista da gwamnati

    ....

    Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayar da wa’adin ranar 7 ga Yuli, 2024 ga masu POS su kammala rajista da Hukumar rajistar kamfanoni ta ƙasar (CAC).

    An bayyana hakan ne lokacin da aka yi wata ganawa tsakanin kamfanonin hada-hadar kuɗi na ƙasar da shugaban hukumar ta rajistar kamfanoni, Hussaini Magaji a Abuja ranar Talata.

    Da yake jawabi a wurin taron, shugaban na CAC ya ce wa’adin watanni biyu na yin rajistar ya yi "daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin babban bankin Najeriya".

    Wata sanarwa da CAC ta fitar kuma ta kara da cewa "An ɗauki matakin ne domin kare masu mu'amala da kamfanonin hada-hadar kuɗi tare kuma da ƙarfafa tattalin arziƙi."

  15. Gwamnan Kano ya sanya hannu kan dokar wajabta yin gwaji kafin aure

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
    Image caption: Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar da ta wajabta yin gwaje-gwajen lafiya ga duk masu niyyar yin aure a faɗin jihar.

    Hakan na nufin cewa daga yanzu babu wani aure da za a ɗaura a jihar har sai an gabatar da takardar sakamakon gwajin ƙwayoyin halittun gado, da na cutar hanta (Hepatitis B da C), da na ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki (HIV).

    Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne kimanin mako guda bayan majalisar dokokin jihar ta amince da ita.

    A cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa an bijiro da dokar ne domin rage yawan yaran da ake haihuwa ɗauke da wasu cututtuka da ake iya ɗauka ko kuma gadonsu daga iyaye, kamar cutar sikila da HIV da kuma ciwon hanta.

    Haka nan dokar ta haramta tsangwamar mutane masu fama da cutar HIV ko sikila ko kuma cutar hanta.

    Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 13 ga wannan wata na Mayu, 2024.

  16. Ƙasar Benin ta dakatar da fitar da man fetur ɗin Nijar ta cikinta

    ...

    Kasar Benin ta dauki matakin hana fitar da man da ake fitarwa daga Nijar ta hanyar bututun mai da ya hada rijiyoyin mai na Nijar da tashar ruwan Cotonou.

    Wannan matakin martani ne kai tsaye ga Nijar, wadda ke ci gaba da rufe kan iyakarta da Benin, duk da cewa Ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (Ecowas) ta ɗage takunkumin da ta kakaba wa gwamnatin Nijar.

    Sakamakon haka, ayyukan jiragen ruwa da aka keɓe don jigilar mai a halin yanzu ya tsaya cak.

    An sanar da jakadan kasar China da ke kasar Benin, Peng Jingtao, tare da hukumar kula da bututun mai, Wapco, a hukumance kan wannan takunkumin.

    Ana gudanar da hada-hadar da ta kai na kuɗi sama da CFA biliyan 600 ta hanyar bututun man na Nijar wanda ya ratsa ta cikin ƙasar Benin.

    Gamayyar kamfanonin kasar Sin ne suka samar da bututun man mai tsawon kilomita 2,000 da kuma rijiyoyin mai na kasar Nijar.

    An kammala aikin bututun man fetur ɗin wanda ake sa ran zai rika jigilar ganga 90,000 na mai a kowace rana zuwa tashar fitar da kaya a kasar Benin a farkon wannan shekarar.

    Sai dai kuma rashin jituwar da ke tsakanin ƙasashen biyu bayan juyin mulkin watan Yulin 2023 da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum na iya kawo cikas ga aikin.

  17. Hotunan yadda ƙarin Falasdinawa ke ficewa daga Rafah

    Fararen hula na ci gaba da ficewa daga Rafah bayan da Isra'ila ta umarcesu su ƙaurace daga Kudancin birnin.

    Kimanin Falasɗinawa dubu 100 ne ke mafaka a birnin Rafah.

    Ga wasu sabbin hotuna da ke nuna yadda Falasɗinawan ke ficewa daga Rafah.

    ...
    ...
    ...
  18. An rantsar da Putin a matsayin shugaban Rasha a wa'adi na biyar

    ...

    An rantsar da Vladimir Putin a matsayin shugaban ƙasar Rasha a wa'adi na biyar wanda hakan ya ƙara tsawaita lokacin da ya kwashe yana mulkin ƙasar.

    A cikin jawabinsa, babu wata alamar nadama game da mamayen Ukraine.

    Ya kuma yi wa ƴan ƙasar alƙawarin cewa Rasha za ta fita daga cikin mawuyacin halin da take ciki a yanzu.

    Shugaba Putin ya kuma dage kan cewa a shirye yake ya tattauna da kasashen Yamma, amma bisa yanayi na martaba juna.

  19. Sojoji sun kashe kwamandan IPOB a Imo

    ...

    Bayan yunƙurin ƴan bindiga na kafa sansanoni a jihar Imo, sojojin Najeriya sun gudanar da wani aikin sharan fage a ranar 6 ga Mayun 2024 inda suka tarwatsa wata maɓuyar ƴan bindigar.

    A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta fitar a shafinta na X, jami'anta sun gudanar da ayyukan ne a yankunan Udda da Ihittukwa da kuma Orsumoghu a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo, bayan samun bayanan sirri.

    Sanarwar ta ce ƴan bindigan sun yi amfani da abubuwa masu fashewa a lokacin artabu da sojoji sai dai daga ƙarshe sojojin ne suka yi nasara.

    A lokacin farmakin an kashe mutum huɗu daga ɓangaren ƴan ƙungiyar ta IPOB, ciki har da wani kwamandan kungiyar, Tochukwu wanda aka fi sani da Ojoto.

    An kuma samu nasarar kwace makamai da dama daga maboyar, waɗanda suka hada da bindigogi da bama-bamai da dai sauran su.