Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 6 ga watan Mayu, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, A'isha Babangida, da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan muke rufe wannan shafi da ya wuni yana kawo muku rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Za mu kawo muku wasu sababbi gobe da safe.

    Umar Mikail ne ke fatan za mu kwana lafiya.

  2. Isra'ilawa sun toshe tituna a zanga-zangar neman dakatar da yaƙi a Gaza

    Tel Aviv

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    'Yan'uwan Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Gaza sun toshe titunan birnin Tel Aviv don yin zanga-zangar neman gwamnati ta amince da yarjejeniyar da Hamas ɗin ta amince da ita don karɓo muatnensu.

    Hamas ta ce ta amince da daftarin da Masar da Qatar suka tsara, amma har yanzu babu tabbas game da abin da yarjejeniyar ta ƙunsa.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce daftarin "ya yi nesa da muradan Isra'ila".

    Amma ya ce za su tura wakilai zuwa Alƙahira don tattaunawa kan daftarin.

    Tel Aviv

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Tel Aviv

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

  3. Matsalar jirgi ta hana Kashim Shettima zuwa Amurka, in ji fadar shugaban ƙasa

    kashim Shettima

    Asalin hoton, State House

    Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya fasa zuwa taron tattalin arziki tsakanin Amurka da ƙasashen Afirka da za a yi a birnin Dallas na Amurka kamar yadda aka tsara tun farko, a cewar fadar gwamnatin ƙasar.

    Yanzu Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar ne zai wakilci Shugaba Bola Tinubu, a cewar sanarwar da kakakin ofishin mataimakin shugaban ƙasar ya fitar a yammacin yau.

    Har yanzu Tinubu bai koma gida ba daga ziyarar da ya kai ƙasashen Netherlands da Saudiyya, abin da ya jawo 'yan adawa suka fara nuna damuwa game da wanda zai jagoranci ƙasar idan Shettima ma ya yi tafiya.

    Sai dai fadar shugaban ta ce matsalar jirgi ce ta hana mataimakin shugaban ƙasar tafiya.

    "Ya fasa tafiyar ne bayan tawagar kula da sufurin shugaban ƙasa ta ba shi shawarar yin hakan," in ji sanarwar da Stanley Nwokocha ya fitar. "Yanzu mataimakin shugaban ƙasa zai ci gaba da hidimta wa ƙasa."

  4. Ba za mu dakatar da kai farmaki a Rafah ba, in ji Netanyahu

    Netanyahu

    Asalin hoton, EPA

    Bayan abubuwan da suka faru game da amincewar da Hamas ta yi da wani daftarin tsagaita wuta, da alama hakan ba zai hana farmakin da Isra'ila ke shirin kaiwa yankin Rafah na Zirin Gaza ba.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce majalisar yaƙi ta ƙasar ta amince a ci gaba da shirin kai harin don matsa wa Hamas ɗin ta saki mutanen da take garkuwa da su a Gaza.

    Ya ce duk da cewa daftarin bai ƙunshi dukkan muradan Isra'ila ba, za su tura tawaga don tattaunawa game da ƙudirin.

  5. Kalli yadda Falasɗinawa ke murna da labarin tsagaita wuta

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
  6. Muna duba daftarin tsagaita wutar da Hamas ta amince da shi - Isra'ila

    Muna ci gaba da bin diddigin abubuwan da ke faruwa a kowane ɓangare game da ƙudirin tsagaita wuta a Zirin Gaza da Hamas ta amince da shi.

    Mai magana da yawun Rundunar Sojin Isra'ila Daniel Hagari ya faɗa wa manema labarai yayin taron manema labarai cewa suna duba daftarin abin da Hamas ta saka wa hannu.

    "Muna tantance duk martanin da za mu mayar da kyau kuma muna ci gaba da ƙoƙarinmu wajen tattaunawar dawo da mutanen da ake garkuwa da su," in ji shi.

    "A gefe guda kuma, muna ci gaba da kai hare-hare a Gaza kuma za mu ci gaba da yin hakan."

  7. Yadda mazauna Gaza ke murna da sanarwar tsagaita wuta

    Sanarwar da Hamas ta bayar cewa ta amince da ƙudirin tsagaita wuta a Zirin Gaza ta jefa mazauna zirin cikin murna da shewa.

    Suna murna ne bayan sun shafe sama da wata shida a ƙarƙashi hare-haren Isra'ila tun daga ranar 7 ga watan Oktoba - bayan harin da Hamas ɗin ta kai cikin Isr'aila da ya kashe aƙalla mutum 1,200.

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas ɗin a Gaza ta ce hare-haren ramuwar gayya sun kashe Falasɗinawa sama da 34,700.

    Qatar da Masar ne suka jagoranci tattaunawar tsagaita wutar a wannan lokaci, amma zuwa yanzu Isra'ila ba ta bayyana ko ta amince ba.

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

  8. 'Daftarin tsagaita wuta na ƙunshe da abubuwan da Isra'ila ba za ta yarda da su ba'

    Wani jami'in gwamnatin Isra'ila ya ce daftarin ƙudirin tsagaita wuta da Hamas ta amince da shi "sauƙaƙaƙƙe ne" wanda kuma Isra'ila ba za ta amince da shi ba.

    Kamfanin labarai na Reuters ya kuma ruwaito cewa jami'in ya ce daftarin na ƙunshe da "manyan abubuwa" da Isra'ila ba za ta yarda da su ba.

  9. 'Yan Gaza na murnar tsagaita wuta

    ..

    Asalin hoton, AP

    Hotuna daga Gaza sun nuna yadda al'ummar Gaza da suka haɗa yara da manya maza da mata na ta faman soya da murna bayan samun labarin amincewar Hamas na tsagaita wuta.

    Yara suna ta tsalle tare da kiɗe-kiɗe na tukwane da farantai da kuma rera waƙoƙi.

  10. Sojojin Najeriya sun daƙile yunƙurin sace mutane a Benue

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Dakarun sojin Najeriya da aka tura domin yaƙi da ta'addanci a yankin Arewa ta tsakiya tare da hadin gwiwar jami'an sa-kai, sun yi nasarar dakile wani yunkurin yin garkuwa da mutane tare da ceto wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a jihar Benue.

    Sojojin sun yi gaggawar kai ɗauki bayan amsa kiraye-kiraye daga sansanin ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a kauyen Tsede da ke kan titin Tor Donga Takum a ƙaramar hukumar Katsina Ala, a jihar, inda suka yi artabu da masu garkuwa da mutane, lamarin da ya tilasta musu yin harbi.

    Mutanen da aka ceto waɗanda suka haɗa da wani Cif Sano Kursi da Augustine Sada, ba su samu wani rauni ba, kuma tuni aka hada sada su da iyalansu.

    Sojojin sun kuma ƙwace makamai da alburusai wanda ya nuna jajircewar sojoji wajen kare rayuka da dukiyoyi da kuma muhimmiyar rawar da jami’an tsaro da al’umma ke takawa wajen yaki da miyagun laifuka.

  11. Labarai da dumi-dumi, Hamas ta amince da sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagorancin ƙungiyar Hamas ya ce sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

    A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, Hamas ta shaida wa masu shiga tsakani na ƙasashen Qatar da Egypt dangane da shawarar amincewar.

    Kawo yanzu dai babu cikakken bayani dangane da yarjejeniyar da suka haɗa da tsawon lokacin tsagaita wuta da kuma makomar mutanen da Hamas suka yi garkuwa da su a Gaza.

    Jami'an ƙungiyar ta Hamas na cewa yanzu zaɓi ya ragewa Isra'ila tunda su sun amince da sharuɗɗan yarjejeniyar.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, shugaban Hamas, Isma'il Haniyeh ya kira firaiministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani da kuma ministan bayanan sirri na Egypt, Abbas Kamel inda ya sanar da su dangane da amincewar da Hamas ɗin ta yi gar yarjejeniyar tsagaita wuta.

  12. Ƴan adawa na zargin murɗiya a zaɓen ƙasar Chadi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu masu sa ido na 'yan adawa sun yi tir da abin da suka bayyana a matsayin rashin bin ka'ida a ci gaba da kaɗa kuri'a a zaben shugaban kasar Chadi.

    Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar cewa tsarin zaben ya bai wa shugaban soji Mahamat Deby fifiko.

    A wata rumfar zaɓe da ke gunduma ta bakwai a babban birnin kasar, N’Djamena, wani mai sa ido na jam'iyyar Transformer's Party ya nuna alamar tambaya kan rikodin na yawan katin zabe da kuma yadda aka aka ƙaɗa kuri'un.

    “Mutum 226 ne aka yi wa rijistar katin zaɓe amma ANGE [Hukumar zabe] ta gabatar da katunan zabe 156 ne kawai. Ina sauran katunan zabe 70?”, Gauthier Saldnba ya tambaya inda ya kara da cewa "akwai matsala a nan."

    An kuma nuna damuwa kan yadda jami'an zabe suka hana wasu masu kaɗa ƙuri'a kada ƙuri'unsu.

    An hana masu kaɗa ƙuri'a da suka yi rajista a wasu yankuna daga N'Djamena, su kaɗa ƙuri'a a cibiyoyin zaɓe a babban birnin kasar.

    Jami’an zaɓen dai sun ce suna bin ka’idojin zaɓen.

    Ana sa ran sakamakon zagayen farko na zaɓen a ranar 21 ga watan Mayu.

  13. Amurka ta jaddada adawarta kan farmakin Isra'ila a Rafah

    Rafah

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada ƙin goyon bayan ƙasarsa game da yunƙurin Isra'ila na kai hare-hare ta ƙasa a yankin Rafah da ke Zirin Gaza.

    Fadar White House ta ce shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da ya tattauna ta waya da Firaminista Benjamin Netanyahu a yau Litinin.

    Biden ya jaddada cewa ba shi goyon bayan farmakin ba tare da wani cikakken tsarin taimaka wa fararen hular da ke samun mafaka a yankin ba.

    "Netanyahu ya amince zai tabbatar da cewa za a bar mashigar Kerem Shallom a buɗe don shigar da kayan agaji ga mabuƙata," a cewar sanarwar da ke ɗauke da kalaman tattaunawar tasu.

    Kerem Shallom mashiga ce a kan iyakar Isra'ila da Gaza, kuma a nan ne wani harin roka na Hamas ya kashe sojojin Isra'ila huɗu a ranar Lahadi.

  14. Babu tattaunawa tsakaninmu da Amurka da Faransa kan kafa sansanin soja - Gwamnatin Najeriya

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Gwamnatin Najeriya ta musanta batun cewa tana duba yiwuwar bai wa ƙasashen Amurka da Faransa damar kafa sansanin soja a ƙasar.

    Wata sanarwa da Minista Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya aike wa BBC ta ce wannan batu "ba shi da tushe" kuma "gwamnatin tarayya ƙarƙashin mulkin Bola Tinubu ba ta yin wata tattaunawa da kowace ƙasa game da hakan".

    A ƙarshen makon da ya gabata ne wasu cibiyoyi da manyan mutane a arewacin Najeriya suka rubuta wa gwamnatin wasiƙa suna gargaɗin kada a bai wa ƙasashen damar kafa sansanin soji a Najeriya, bayan korar su da aka yi daga wasu ƙasashen yankin Sahel.

    "Muna neman jama'a su yi watsi da wannan ƙaryar," a cewar sanarwar.

    "Ba mu samu wata buƙata ko tattaunawa da wata ƙasa ba kan wannan batu game da kafa sansanin wata ƙasar waje a Najeriya. Da ma tuni Najeriya na ci gaba da amfana daga aikin haɗin gwiwa wajen daƙile matsalolin tsaro."

    Tuni ƙasashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suka fatattaki sojojin Faransa da na Amurka daga ƙasashensu kuma suka gayyaci na Rasha.

  15. An rage wa 'yan rukunin 'Band A' farashin lantarki a Najeriya

    Lantarki

    Asalin hoton, TCN

    Hukumar kula da samar da lantarki ta Najeriya ta rage farashin wutar lantarki ga waɗanda suka faɗa cikin rukunan 'Band A' masu samun ƙarfin wuta fiye da kowa a ƙasar.

    Da yake tattaunawa da BBC, jam'in hukumar ta NERC, Usman Abba, ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne saboda karyewar darajar dala, inda yanzu farashin ya sauko daga naira 225/kWh zuwa naira 206.80.

    "Daga cikin abubuwan da ake dubawa wajen ƙayyade farashin wuta akwai farashin kuɗaɗen ƙasar waje," in ji shi. "Tun da an samu saukar dala to dole ne farashin mai ma ya sauko."

    Najeriya na samar da lantarki ne ta hanyar amfani da tashoshi masu amfani da ruwa, da man fetur, da kuma iskar gas.

    A makwannin da suka gabata ne hukumar ta ƙara farashin lantarki ga al'ummar ƙasar waɗanda ke samun lantarki na fiye da awa 20 a kowace rana.

    Lamarin ya haifar da koke-koke a faɗin ƙasar, inda masana ke fargabar hakan zai iya jawo ƙarin hauhawar farashi.

  16. Kwamitin bincike kan bangar siyasa a Kano ya fara aiki

    Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, fb/Abba Kabir Yusuf

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf

    A jihar Kano, kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin binciken kan rikice-rikicen siyasa ya fara zamansa na jihar.

    Kwamitin karkashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf, zai yi bincike ne a kan rikice-riciken siyasa da mutanen da suka ɓata da tashin hankalin da aka yi a 2015 da 2019 da kuma 2023.

    A cikin jawabin da ta gabatar a lokacin ƙaddamar da zaman farko na kwamitin, Zuwaira Yusuf ta ce kwamitin zai yi ƙoƙarin zaƙulo waɗanda suka ɗauki nauyi da kuma waɗanda suka aikata laifukan da suka shafi rikicin siyasa da kuma sauran ayyukan assha.

    Haka nan kwamitin zai bayar da shawara kan yadda za a tallafa wa mutanen da rikice-rikicen suka rutsa da su.

  17. Najeriya za ta rage lantarkin da take bai wa Nijar da Benin da Togo

    ...

    Asalin hoton, bbc hausa

    Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta umarci kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasar ya rage lantarkin da yake bai wa ƙasashe maƙwafta domin bunƙasa samar da wutar lantarki a cikin gida.

    A cikin wata takardar umarni da hukumar ta fitar a ranar Juma’ar da ta gabata, ta ce tsarin da kamfanin samar da wutar lantarki ga ƙasashen ƙetare ke bi a halin yanzu ya jawo jefa ‘yan Najeriya cikin wahala.

    Hukumar ta ƙayyade cewa kashi 6 cikin 100 na wutar da ake samarwa ne kawai za a fitar da su ƙasashen ƙetare na tsawon watanni shida masu zuwa, daga ranar 1 ga Mayu.

    Akwai yarjeniyoyi da Najeriya ta ƙulla na samar da wutar lantarki ga ƙasashen Afirka da ke makwabtaka ita.

    Ana yawan samun katsewar wutar lantarki a Najeriya saboda karancin wutar amma abin ya ƙara kamari a 'yan kwanakin nan.

    A baya-bayan nan ne kamfanonin samar da wutar lantarki suka ƙara kuɗin lantarki ga wasu kwastomomin cikin gida da ke samun wutar lantarki na tsawon sa'o'i 20 a kullum.

  18. Anam da Amar: Ma'auratan da ke burin gyara zaman aure ta hanyar TikTok

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  19. Mahaukaciyar guguwa ta kashe mutum uku a Tanzaniya

    ...

    Asalin hoton, EPA

    An bayar da rahoton mutuwar mutane uku tare da ceto wasu fiye da 100 a ƙasashen Kenya da Tanzania sakamakon mahaukaciyar guguwar da ta faɗa wa ƙasashen a karshen mako.

    Ko da yake guguwar ta rage ƙarfi sosai yayin da ta tunkari gaɓar tekun Tanzaniya, ta haddasa ruwan sama da iska mai karfi a yankunan kudancin kasar a ranar Asabar.

    Jiragen ruwa sama da 20 daga Tanzaniya da Zanzibar na daga cikin wadanda aka ceto, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na ƙasar suka ruwaito.

    Jirgi guda daya dauke da masunta 10 ya fito ne daga tsibirin Pemba na Zanzibar sannan daya kuma an ruwaito cewa ya fito ne daga ƙasar Tanzaniya.

    An bayar da rahoton cewa wani matukin jirgin ruwa ɗaya ya mutu.

    A tsibirin Kilwa na kasar Tanzaniya a yankin Lindi kuma, mutane 2 ne suka mutu sannan aka ceto wasu 80 kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Lahadi.

    An samu katsewar wutar lantarki a mafi yawan ƙasar Tanzaniya a ranar Asabar, sakamakon ruwan sama da iska mai karfi.

    Haka kuma, an dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa tsakanin cibiyar kasuwancin Tanzaniya, Dar es Salaam, da Zanzibar yayin da mahaukaciyar guguwa ta tunkari gabar tekun gabashin Afirka.

    Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna gidaje da dama da iska mai karfi ta lalata yayin da itatuwan kwakwa suka fado kan gidaje sakamakon ruwan saman da iskan mai karfi.

  20. Isra'ila ta umurci mutanen Gaza su fice daga yankin Rafah

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta fara bai wa Falasdinawa umarnin ficewa daga sassan gabashin Rafah, gabanin farmakin da take shirin kai wa a kudancin yankin na Gaza.

    Kimanin mutum 100,000 ne aka umurce su da su nufi wani “babban yanki na jin kai” a Khan Younis da al-Mawasi.

    Bayan shafe watanni bakwai ana yaƙi, Isra'ila ta ce dole ne ta ɗauki mataki a Rafah domin fatattakar Hamas.

    Sai dai Majalisar Dinkin Duniya da Amurka sun yi gargaɗin cewa kai hari kan birnin, inda Falasdinawa sama da miliyan daya ke samun mafaka, na iya haifar da mummunan sakamako.

    An bayar da rahoton cewa, harin da jiragen yakin Isra'ila suka kai a Rafah sun kashe Falasdinawa aƙalla 19 a cikin dare, bayan da mayaƙan Hamas suka kashe sojojin Isra'ila uku a kan iyakar Kerem Shalom da ke ƙarƙashin ikon Isra'ila - wata muhimmiyar hanyar shigar da agaji zuwa Gaza.

    Hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da yunkurin tabbatar da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su ya ci tura, ko da yake masu shiga tsakani sun ce suna ci gaba da kokari.