Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Buhari Muhammad Fagge da Abdullahi Bello Diginza

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa Kai-tseye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa, domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Gwamnatin Isra'ila na rashin goyon bayanta kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Ministoci a gwamnatin Isra'ila sun bayyana rashin goyon bayan yiwuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

    Benny Gantz ɗaya daga cikin masu faɗa a ji a majalisar zartaswa ya ce akwai buƙatar kawo ƙarshen gwamnatin Isra'ila idan aka soke shirin kai hari birnin Rafah da ke Kudancin gaza.

    Wakilin BBC ya ce: Mista Netanyahu na son kai wa ragowar ''bataliyar Hamas'' da ke Rafah hari, akwai kuma fargaba cikin Isra'ila game da makomar mutane 130 da Hamas ke ci gaba da garkuwa da su.

    Shugaba Joe Biden da Firaminista Netanyahu sun tattauna ta wayar tarho bayan mai ba da shawara kan harkokin tsaro a fadar White House ya ce Isra'ila ta ba da tabbacin cewa dakarunta ba za su shiga Rafah ba har sai Amurka ta bayyana abinda da take fargaba.

    Kungiyar Hamas ta ce wata tawaga za ta je birnin Alkahira ranar Litinin domin gabatar da martaninta kan ƙudirin tsagaita wuta da Isra'ila ta yi.

  3. An gano gawar mutum guda tare da kuɓutar da mutum 25 a tekun Girka

    .

    Jami'an tsaron gabar teku a Girka sun ce sun gano gawar mutum guda tare da ceto wasu 25 bayan wani kwale-kwalen ɗauke da baƙin haure ya shiga mawuyacin hali a tsibirin Samos na Aegean.

    An miƙa waɗanda suka tsira zuwa tashar jiragen ruwa cikin koshin lafiya. Yayinda ake ci gaba da laluben wasu mutum huɗu da suka yi ɓatan dabo.

    Hukumomin ƙasar sun bayyana yadda ayarin wasu 'yan cirani 20 suka tsallake rijiya da baya a tsibirin Chios.

    Adadin mutanen da suke shiga Girka ba bisa ƙa'ida ba na ƙaruwa, rahotanni sun bayyana cewar kusan baƙin haure 11,000 ne suka isa ƙasar a wannan shekara da muke ciki.

  4. Ƙwararrun sojojin Rasha sun sauka a Chadi

    ..

    Rahotanni daga Chadi sun ce kusan masu horaswa 130 daga ƙungiyar dakarun sa kai ta Rasha sun isa kasar.

    Dakarun na Rasha sun sauka a filin jirgin saman N'Djamena babban birnin kasar a Jirgin Ethiopian Airline .

    Wannan al'amri na zuwa ne a lokacin da sojojin Amurka suke shirin janyewa daga Chadi.

    A watan Janairu ne shugaban ƙasar Mahamat Deby, ya kai wata ziyarar ba-zata a birnin Moscow inda ya tattauna da shugaban ƙasar Volodymir Putin.

    A baya-bayan nan wasu ƙasashen Afirka na ƙulla ƙawance da Rasha bayan yanke alaƙa da ƙasashen Yamma.

    Ko a watan Afrilun da mu ke ciki ma ƙwararrun sojoji daga Rashar sun sauka a jamhuriyar Nijar domin horas da sojojin ƙasar

    Kungiyar Wagner da ke aiki a Afirka ta cauya suna zuwa 'Africa Corps' bayan mutuwar shugabanta Yevgeny Prighzhin a shekarar da ta gabata.

    Me zuwan kwararrun sojin Rasha jamhuriyar Nijar ke nufi?

    Yaƙe-yaƙen Wagner da haƙar man fetur da zinare a ƙasashen duniya

  5. Ƙungiyar bayar da agajin ta WCK ta ce za ta koma aiki a Gaza

    Ƙungiyar bayar da agajin abinci ta WCK ta ce za ta koma aiki a Gaza ranar Litinin, wata guda bayan harin Isra'ila ya kashe jami'an ƙungiyar bakwai.

    Kungiyar ta bayyana cewar tana da motoci sama da 200 da saba'in ɗauke da abincin da za ta shigar Gaza ta mashigar Rafah.

    Harin Isra'ila a watan Afrilu ya fuskanci suka da buƙatar a gudanar da cikakken bincike. Tuni aka sallami manyan kwamandoji biyu daga rundunar tsaron Isra'ila.

  6. Lamari ya tsananta a fagen daga - Babban kwamandan Ukraine

    .

    Babban kwamandan sojin Ukraine ya ce lamari ya tsananta a fagen daga, sakamon ƙaruwar hare-haren Rasha.

    Oleksandr Syrskyi ya ce dakarun Ukraine sun janye daga filin daga a gabashin yankin Donetsk.

    Rasha na fatan amfani da ƙarfin dakarun da makaman atilare da take da shi, kafin dakarun Ukraine su samu tallafin makamai da Amurka ta alƙawarta bai wa ƙasar.

    A makon da ya gabata ne Amurka ta bayar da tallafin makamai da kayan aiki ga sojojin Ukraine na dala biliyan 61 ga ƙasar Ukraine.

    To sai dai har yanzu ba a fara amfani da makaman na Amurka a filin dagar ba, inda dakaru na Ukraine na ƙasa da na sama suka shafe watanni suna fama da rashin makamai

    "Lamura sun dagule mana a fagen daga," in ji janar Syrskyi cikin wani saƙo da ya wallafa zuwa ga sojojin ƙasar a shafin Telegram.

    Ya tabbatar da cewa dakarun Ukraine sun janye daga wasu wuraren da suke a yankin Donetsk, wanda ya ce yankunan na daga cikin wuraren da sojojin ƙasar suka kama tun bayan kwace Avdiivka da Rasha ta yi a watan Fabrairu.

    An gudanar da mafi yawan yaƙin a kusa da Chasiv Yar, da ke ƙarƙashin ikon Ukraine, wanda kuma Rasha ke ƙoƙarin kwacewa bayan Avdiivka.

  7. Tsananin zafin rana: Hukumomin Kano sun shawarci mazauna jihar don kauce wa kamuwa da cutuka

    ..

    Hukumar kula da asibitocin Kano ta shawarci al'ummar jihar su gaggauta ziyartar asibiti mafi kusa da su da zarar sun ji wasu alamu na rashin lafiya a jikinsu.

    Sakataren hukumar, Dr Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar da jami'ar hulɗa da jama'a ta hukumar, Samira Suleiman ta sanya wa hannu.

    Dakta Mansur Mudi Nagoda,ya bayar da shawarar ne don kauce wa cutar ƙyanda da wata cuta da ake samu sakamakon tsananin zafi da jihar ke fuskanta

    Sanarwar ta ce alamomin cutukan sun haɗa da zazzaɓi mai tsanani da ciwon kai da amai da ciwon wuya da bushewar maƙogoro da kasala da sauran alkamomi.

    Dakta Mansur Mudi Nagoda ya ce za a samar da tawagar gaggawa ta musamman da za ta riƙa kula da marasa lafiya a asibitocin jihar.

    Sanarwar ta kuma ce mutanen da ke fama da cutar siga da hawan jini su nemi shawarar likitoci a wannan lokaci da ake fama da tsananin zafi.

    Shugaban hukumar ya kuma shawaraci mutane su yawaita shan ruwa tare da guje wa yawo a cikin rana, da kauce wa kwanciya a ɗakunan da ke cike da cunkoso.

    Birnin Kano da wasu yankunan arewacin Najeriya na fama da tsananin zafi, lamarin da ake fargabar ɓarkewar cutukan da ke da alaƙa da zafin.

  8. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  9. Burkina Faso ta musanta zargin sojojin ƙasar da kisan mutum 223 a ƙauyuka

    ..
    Image caption: Shaidu sun ce fiye da sojoji 100 ne aka tura ƙauyukan

    Burkina Faso ta musanta zargin da ta kira ''marar tushe'' da aka yi wa sojojin ƙasar da kisan mutum 223 a wasu hare-hare da suka kai wasu ƙauyukan ƙasar cikin watan Fabrairu.

    Rahoton ƙungiyar kare haƙƙinj bil-adama ta A Human Rights Watch, ya yi zargin cewa a ranar 25 ga watan Fabariru, sojojin sun kashe mutum 179 a ƙauyen Soro da wasu 44 a ƙauyen Nondin, inda rahotoin ya ce 56 daga ciki ƙananna yara ne.

    Ƙungiyar ta ce wannan na daga ciki ''mafi munin zaluncin da sojojin suka aikata'' a ƙasar a cikin kusan shekara 10.

    Hukumomin Burkina Fason sun ce sun fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano 'gaskiyar lamarin' tare da yin Allah- wadai da rahoton da HRW.

    "Gwamnatin Burkina Faso ta yi fatali tare da yin Allah-wadai kan wanna zargi maras tushe,'' kamar yadda ministan sadarwar na ƙasar Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo ya bayyana cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Asabar.

    Ministan ya bayyana mamakinsa cewa ''yayin da ake cikin bincike don gano gaskiyar abin da ya faru, kuma sai ga WHR ta fitar da nata rahoto tana ɗora alhakin hakan a kan wasu ba'', in ji shi.

    A farkon wannan makon ne gwamnatin mulkin sojin ƙasar ta dakatar da BBC da VOA daga aiki a ƙasar, saboda wallafa rahoton na HRW.

  10. Amsoshin Takardunku

    Video content

    Video caption: Latsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  11. 'Likitoci 58,000 ne suka sabunta lasisinsu cikin 130,000 saboda tafiya ƙasashen waje'

    A

    Mai yin rijistar ƙungiyar likitocin haƙori da sauran likitoci masu neman kwarewa Dr Fatima Kyari ta bayyana cewa likitocin da suka yi rijista ba su wuce 58,000 da suka sake sabunta lasisinsu na aiki a 2023 saboda zirarewar kwararrun lafiya zuwa ƙasashen waje.

    Dr Kyari ta bayyana hakan ne yayin rantsar da sabbin likitocin 20 da aka yi bikinsu a Jami'ar jihar Edo.

    Tana cewa wajibi ne ga dukkan wanda aka rantsar ya yi aiki da ƙa'idoji da kuma tsari na yadda likitoci ke aiki a Najeriya.

    Tace hukumar su na da mutum 130,000 da suka yi rijista ya zuwa yanzu a matsayin likitoci da ke son aiki a Najeriya tun lokacin da ta fara aiki shekara 61 baya.

    "Amma 58,000 ne kacal suka sabunta lasisinsu na shekara-shekara a 2023, wannan na da alaƙa da yadda ake samun ƙaruwar likitocin da suke zirarewa ƙasashen ƙetare."

  12. Dubban mutane sun fito suna rokon Firaiministan Spain ka da ya yi murabus

    A

    Dubban mutane da ke goyon bayan Firaiministan Spain Pedro Sanchez ne suka yi taro a kan titinan Madris a wani yunkuri na jan hankalinsa kada ya yi murabus.

    Shugaban jam'iyyar masu sassaucin ra'ayin ya girgizar ƙasar a ranar Laraba ta hanyar sanar da cewa zai sok duk wasu ayyukansa a hukumance domin ya mayar da hankali kan gobensa.

    Ya ɗauki wannan mataki ne bayan kotu ta sanar da kafa wani kwamiti da zai yi bincike kan matarsa dangane da zargin cin hanci da rashawa.

    Magoya bayan jam'iyyarsa un shigo motoci daga sassa daban-daban na ƙasar domin su halarci wannan zanga-zanga a wajen hedikwatar ofishin jam'iyyarsa da ke Madrid, suna waƙa suna cewa 'Pedro ka da ka sare' kuma 'Ba kai daya ba ne.'

  13. Arteta ya nemi shawarar Arsene Wenger kan yadda zai lashe Premier

    A

    Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ya nemi shawara dafa tsohon kocin Gunners Arsene Wnger kan yadda zai iya lashe gasar Premier gabanin wasan hamayyar arewacin Landan da Tottenham Hotspur.

    Kungiyar ta Arteta na saon kawo ƙarshen shekaru 20 da suka kawashe ba tare da cin wannan kofin ba, kofin ƙarshe da Arsenal ta ci shi ne na 2003-04 da Wenger ya ɗauka cikin uku da ya ci wa ƙungiyar.

    Za su je wasan Tottenham ne da maki ɗaya tsakaninsu da Manchester City da ke matsayi na biyu a gasar.

    "Na tattauna da shi na wasu lokuta kaɗan," in ji Arteta, wanda ya yi wasa na shekara biyar ƙarƙashin Wenger lokacin da yake daf da ajiye takalmansa.

    "Akwai wasu maudu'ai kan yadda suka lashe gasar a baya kuma daga baya suka ƙara."

    Arsenal na da damar ba da maki hudu tsakaninta da City da za ta fafata da Notthengham Forest an jima da maraice.

  14. An yi zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a gaban Shugaba Biden

    A

    Dubban magoya bayan Falasdinawa na zanga-zanga a wajen ginin da ake gudanar da wani taron kungiyar 'yan jaridan fadar gwamnatin Amurka a Washington.

    Masu boren na sanye tufafin da aka rubuta sunayen 'yan jaridan Falasdinawa da aka kashe a yakin Gaza.

    A jawabin da ya gabatar cike da barkwanci shugaba Biden ya zolaye kansa da kuma abokin hamayyarsa na Republic Donald Trump a wajen taron.

    "Eh, shekaru za su taka rawa a wannan zabe, gani tsoho ina kuma takara da yaro dan shekara shida," in ji Biden.

    Sannan ya nuna damuwarsa cewa dimokuradiyyar Amurka na cikin hadari a watan Nuwamba.

  15. Ƙyanda ta 'kashe yara 19' a jihar Adamawa

    A

    Rahotanni daga ƙaramar hukumar Mobi ta Arewa sun ce aƙalla yara 19 ne suka mutu sakamakon bullar wata rashin lafiya da ake zargin kyanda ce.

    Kyanda dai wata cuta ce da take yaɗuwa ta yi illa kuma musamman tsakanin yara ƙanana.

    Daga cikin illar da take haifarwa akwai makanta da kumburin kwakwalwa da gudawa da nunfashi da kyar.

    Da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, kwamishinan lafiya na jihar Felix Tangwami ya ce sama da yara 200 yanzu haka sun kamu da cutar a ƙaramar hukumar.

    Ya ce a ranar Asabar ma an samu bullar cutar a Yola babban birnin jihar, abin da ya janyo aike wa da magunguna da kuma ma'aikatan lafiya ga kauyukan da abin da ya shafa.

    Ya yi alƙawarin za a yi maza a garzaya da yaran da suka kamu zuwa asibitoci.

    Kwamishinan ya ce za a aika da jami'an lafiya ƙaramar hukumar Mubi da Gombi inda aka ƙara samun bullar cutar.

  16. Shugabannin Somalia da Tanzania sun tattauna kan alaƙar diflomasiyya

    f

    Shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud ya tattauna da shugabar Tanzania Ms. Samia Suluhu Hassan a fadar Dares Salaam kan abubuwan da suka shafi alaƙar diflomasiyya.

    Shugabannin biyu sun tattauna yadda za su ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu da fuskar siyasa da tsaro da tattalin arziki da abubuwn ci gaban al'umma da dai wasu abubuwa da suka shafi ci gaban yankin.

    Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya je Tanzania ne bayan katin gayyata da ya samu daga shugaba Samia Suluhu Hassan ta Tanzania.

    Ba tare da ɓata lokacin ba Shugaban Somalia ya karɓi wannan gayyata tare da kai mata ziyara.

    a
  17. An buɗe gidan wasan daɓe da raye-raye na farko a Saudiyya

    a

    An buɗe gidan wasan daɓe da raye-raye a birnin Riyadh, an kuma gabatar da wasan farko a cikinsa.

    Wannan dai na cikin shirin Yarima Mohammed bin Salman na mayar da masarautar ta daban ta fuskar jin dadi da kuma tattalin arziki.

    Labarin da aka yi sunansa Zarqa Al Yamama na wasa shugaban wata ƙabila ta masu koren idanu, wata kyauta da aka yi musu tun gabanin zuwan addinin Musulunci cikin Larabawa.

    A

    Hasashen da ta yi na wani haɗari da za su fuskanta bai samu karbuwa ba a wajen al'umarta - wani labari da zai ja hankalin duniya kamar yadda Ivan Vukcevic shugaban gidan ya bayyana.

    A

    An samu wani kamfani daga Switzerland domin taimakawa wajen gudanar da wasan farkon da koyar da kiɗe-kiɗen Gabas ta Tsakiya na shekarun baya.

    Lokacin da aka gabatar wa da Mista Vukcevic da kamfaninsa cewa za a buɗe wajen shekara biyu da suka gabata, ya yi matuƙar kaduwa tare da nuna shakkun ko hakan zai iya faruwa ta dadin rai.

    A

    Sun una mamaki kan yadda za a iya aiki da rubutun Larabci wajen kida, yaren da ake fara rubutu daga dama zuwa hagu a kiɗan da aka ƙirgira a tsakanin ƙasashen yamma d suke rubutu daga hagu zuwa dama. Amma daga baya an shawo kan wannan matsalar.

  18. Majalisar Iraƙi ta ɗauki mataki mai tsauri kan masu auren jinsi

    g

    Majalisar Iraki ta amince da wani kudirin doka dake hukunci mai tsanani kan masu sha'awar mu'amala da jinsu guda.

    Majalisar ta yi haramci tare da amincewa da daurin shekara 15 kan duk wanda aka samu da soyayya ko auren jinsi guda, sannan duk wanda kuma aka samu da laifin goyon-baya ko karfafa wannan dabi'a zai sha daurin shekara bakwai a gidan yari.

    Sannan masu sauya jinsin halitta za su sha daurin shekara daya zuwa uku a gidan kaso, haka zalika duk likitan da aka samu da aikin sauya halitta.

    Dokar ta kuma haramta duk wata dabi'a ko salo na mace ta auri ko mu'amala da sama da namiji guda.

    Tuni dai Amurka ta yi alla-wadai da dokar, haka ma kungiyoyin kare hakki bil adama.

  19. Ya kamata Amurka ta dakile yadda ake shigar da makamai - MDD

    A

    Wakiliyar Sakatare Janar na MDD a Haiti ta bukaci Amurka ta kara kaimi wajen dakile yadda ake shigar da makamai daga Amurka zuwa kasar.

    Maria Isabel Salvador ta shaida wa BBC cewa akwai bukatar daukan matakai na sanya takunkumi kan kungiyoyin daba da suka jefa Haiti a cikin rikici.

    Ta yi watsi da batun a yi sulhu da 'yan daban a kokarin dawo da doka da oda a kasar, Ta ce masu aikata muggan laifuka ne, suna aikata fyade da kisa kan kananan yara da mata a kullum - sannan sun kasaftu rukuni-rukuni sama da 200.

    A ranar Alhamis aka kaddamar da gwamnatin rikin kwarya domin shirya zabe da daidaita harkokin gwamnati.

  20. MDD ta ce yaƙi ya ƙazanta a birnin al-Fashir na Sudan

    A

    Kwamitin tsaro na MDD ya nuna matukar damuwarsa kan kazamin hare-haren da dakarun RSF ke kai wa a birnin al-Fashir na Sudan.

    Al-Fashir shi ne birni mafi girma kuma na karshe a yankin Darfur da sojojin Sudan ke nuna wa RSF fin karfi, dakarun da ake zargi da kai munanan hare-hare kan kabilun da ba larabawa ba.

    Quscondy Abdulshafi na kungiyar Human right watch ya ce mutanen da ke al-Fashir a yanzu ba su da idan za su je ko su tsere saboda fargabar kada a kashe su.

    Kwamitin tsaro ya bukaci bangarorin biyu su kawo karshen karfin sojin da suke nunawa a yankin.