Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, Umar Mikail da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    To jama'a a nan za mu dakata da kawo muku rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Fatan kun ji daɗin kasancewa da mu tun daga sanyin safiya zuwa yanzu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. An kama masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa 40 a Amurka

    Sama da masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa 40 ne aka kama a jami'ar Yale da ke jihar Connecticut ta Amurka.

    'Yan sanda sun cean gargaɗi masuzanga-zangarhar saubiyu a kan su dakatar da ita, bayan fara ta ranar juma’ar da ta gabata.

    Shugaban jami’ar ya yi gargaɗin cewa za a ɗauki matakin ladabtarwa kan waɗanda aka samu da aikata laifukan da suka keta dokokin tsaro da suka haɗa da kafa tantuna ba bisa ka’ida badakuma yawo a harabar makaranta bayan lokacin da aka kayyade.

    Kamen da aka yi a Yale ya biyo bayan irin wannan zanga-zangar da aka yi a jami'ar Colombia da ke New York, inda a makon da ya gabata akakamamasu zanga-zanga fiye da ɗari.

  3. Majalisar wakilai ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan samar da ‘yan sandan jihohi

    NATIONAL ASSEMBLY

    Majalisar wakilan Najeriya ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan maganar samar da ‘yan sandan jihohi a faɗin ƙasar.

    An jima ana tafka muhawara kan batun samar da ‘yan sandan jihohi a Najeriya, sai dai a wannan karon majalisar ta fito karara domin sanya zancen a bainar jama’a.

    Masu ruwa da tsaki da dama ne suka halarci taron a yau Litinin, ciki har da wasutsofaffin shugabannin ƙasar da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da sauran su.

    Latsa hoton ƙasa don sauraron rahoton Abdou Hallou.

    Video content

    Video caption: Latsa sama don sauraron rahoton
  4. Za mu bayyana shaidu da ke nuna Trump yana da laifi - Masu gabatar da ƙara

    Donald Trump

    Masu gabatar da kara a shari’ar Donald Trump, sun shaida wa kotu da ke birnin New York cewa tsohon shugaban Amurkar ya kitsa makarkashiya da yin rufa-rufa, kuma shaidu za su nuna wa masu taya alkali yanke hukunci cewa yana da laifi.

    Mista Trump ya musanta shirya karya a bayanan kasuwancinsa don ɓoye kuɗaɗen da aka biya wata ‘yar fim ɗin batsa Stormy Daniels, domin kar bayanan alaƙarsu ta fito fili gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2016.

    Bayanin da masu gabatar da ƙarar suka yiwa masutaya alkali yanke hukunci na cewa wannan batu ne namakarkashiya.

    Kafin a fara shari'ar, Mista Trump ya yi Allah-wadai da lamarin a matsayin katsalanda cikin hakar zaɓeda aka tsara domin daƙile yunkurinsa na sake tsayawa takara a watan Nuwamba.

  5. Mutum takwas sun mutu a hatsarin mota a Kogi

    Hatsarin mota

    Mutum takwas ne suka rasa ransu a wani hatsarin mota a yankin Aloma a karamar hukumar Ofu na jihar Kogi.

    Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kogi Samuel Oyedeji ya tabbatar da faruwar lamarin a Lokoja, babban birnin jihar.

    Ya ce hatsarin ya afku ne ranar Lahadi kuma ya shafi fasinjoji 21.

    Oyedeji ya ce wasu mutum 13 kuma sun samu raunuka daban-daban a gobarar da ta tashi sakamakon hatsarin.

    Wani ganau ya faɗa wa gidan talabijin na Channels cewa wata motar Sienna ce da ke hanyar zuwa Abuja daga Fatakwal, ta yi taho-mu-gama da motar bas, abin da ya janyo tashin gobara da kuma ya yi sanadiyar mutuwar wasu fasinjoji.

    Ganau ɗin ya ɗora laifin afkuwar hatsarin kan gudu fiye da kima da kuma rashin kyawun hanya, inda ya ce sun shafe sa'o'i uku kafin su sami damar cire direban ɗaya daga cikin motocin daga motarsa.

  6. An kori sojojin Najeriya bayan an tuhume su da sata a kamfanin Dangote

    Sojoji

    Rundunar sojin Najeriya ta sanar da korar wasu jami'anta biyu waɗanda aka samu da laifin satar wayoyin wutar lantarki a matatar Dangote da ke jihar Legas.

    Tun da farko dai, a baya-bayan nan ne wasu jami’ai na kamfanin tsaro mai zaman kansa da kuma wasu sojoji suka kama waɗanda ake zargin, Kofur Innocent Joseph da Lance Kofur Jacob Gani bisa laifin sata.

    Wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na rundunar sojin Najeriya, Manjo-janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ranar Litinin, ya ce an samu mutanen biyu da laifin barin wurin aikinsu yayin binciken da aka gudanar.

    Nwachukwu ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun gaza yin aikinsu yadda ya kamata da kuma saɓa wa dokokin aikin soja kamar yadda yake a sashe na 57.

    Ya ce bayan kammala bincike ne, rundunar ta ɗauki matakin sallamar jami'an biyu tare da miƙa su ga hukumomin da suka dace domin gurfanar da su gaban kotu, domin hakan ya zama izina ga sauran jami’an tsaro da ke shirin aikata irin wannan laifin.

    "Muna da zimmar ganin mun ci gaba da jajircewa a kan aikinmu na kare ƴan ƙasa. Muna kira ga al'umma da su ci gaba da ba mu goyon baya a ƙoƙarin mu na samar da tsaro da kuma ɗabbaka zaman lafiya a faɗin ƙasa," in ji sanarwar.

  7. An kama mutum uku da zargin yi wa China leƙen asiri

    China

    Masu gabatar da ƙara a Jamus sun ce an kama wasu ƴan ƙasar Jamus guda uku, waɗanda ake zargi da yi wa China leƙen asiri.

    Mutum biyu cikin waɗanda ake zargin sun kasance ma'aurata da suka mallaki kamfani a birnin Dusseldorf.

    An kwatanta na ukun kuma a matsayin ma'aikaci a hukumar kula da harkokin tsaron cikin gida a ƙasar China.

    An zarge shi da karɓar bayanai kan sabuwar fasaha da za a yi amfani da ita a fasahar sojoji.

  8. Mutum 13 sun mutu a hatsarin mota a Tanzaniya

    Hatsarin mota

    Wasu mutum 13 sun mutu a wani hatsarin mota a Tanzaniya.

    Lamarin ya faru ne lokacin da wata motar bas da ta fito daga yankin Somanga zuwa Kilwa Kivinje, a lardin Lindi, ta yi taho-mu-gama da wata motar dakon mai.

    Kwamandan ƴan sandan lardin, John Imori ya tabbatar da faruwar al'amarin, inda ya ce wasu mutum shida kuma sun samu raunuka.

    Ana ci gaba da bincike domin gano abin da ya janyoi hatsarin.

  9. Najeriya za ta haɗa gwiwa da Libya don daƙile yaɗuwar ƙananan makamai

    Badaru

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta haɗa gwiwa da Libya domin daƙile yaɗuwar ƙananan makamai.

    Ministan tsaron ƙasar, Muhammad Badaru Abubakar shi ya bayyana haka ranar Lahadi, yayin wata tattaunawa da wakilin gwamnatin ƙasar Libya, a wani ɓangare na karfafa matakan tsaro, rage tu'ammali da ƙwayoyi da kuma ɗorewar ƙasashen biyu.

    Badaru ya tabbatar da cewa Najeriya a shirye take wajen ci gaba da aiki da sauran ƙasashen Afrika da kuma karfafa haɗin gwiwa a matakin yanki da kuma na ƙasa da ƙasa.

    A cewarsa, safarar ƙananan makamai ba ta san kan iyaka ba kuma ba ta mutunta dokoki, inda ya ce ya zama tilas a haɗa kai don aiki tare.

    Tun da farko, shugaban tawaga kuma wakilin hukumar tsaro ta ƙasar Libya, Janar Mohammed M.M Azain, ya bayyana cewa sun kawo ziyara Najeriya ne don tattauna matsalolin rashin tsaro da ke addabar ƙasashen da kuma samar da hanya ta daƙile yaɗuwar ƙananan makamai.

    Ƙasashen biyu sun yi alkawarin ci gaba da ɓullo da hanyoyin daƙile yaɗuwar ƙananan makamai da kuma safarar ƙwayoyi daga Libya zuwa Najeriya, saboda ɗorewar ƙasashen biyu da kuma kare jama'arsu.

  10. Sojojin Najeriya sun gano gidan gasa burodi na mayaƙan ISWAP a Borno

    ..

    Dakarun sojin Najeriya sun ruwaito gano gidan gasa burodi da ƙungiyar masu tayar da kayar-baya ta ISWAP ke amfani da shi a garin Maisani, da ke karamar hukumar Damboa na jihar Borno.

    A cewar wasu bayanan sirri da wani masani kan ƙungiyoyin ta'addanci, Zagazola Makama ya fitar ranar Litinin, ya ce haɗin gwiwar dakarun bataliya ta 199 da kuma rundunar tsaro ta JTF ne suka gano wurin gasa burodin yayin wani samame da suka kai maɓoyar ƴan ta'addan ranar Lahadi.

    "Majiyoyi sun ce an lalata gidan burodin tare da ƙwato kayayyaki da suka kunshi manyan injunan bayar da hasken wutar lantarki guda biyu, wani abin gasa burodi da kuma wasu kayan haɗi da ake yin burodi da dama," kamar yadda Makama ya ruwaito.

    A cewar rahoton, gano wurin na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji suka kai wani samame na tsawon mako ɗaya da zimmar kakkaɓe ƴan ta'dda daga yankunan da suka fi karfi a dajin Timbuktu Triangle, da sauran yankuna da suka haɗa da Talala, Ajigin, Dusula, Abulam da kuma Gorgi - waɗanda suka kasance wurare masu haɗari da ƙungiyoyi masu tsattsaurar ra'ayi ke zama.

    "Waɗannan ƙungiyoyin ƴan ta'dda yawanci su ke da alhakin kai hare-hare, kwantan-ɓauna, binne abubuwan fashewa a kan hanyoyin Damboa, da Damaturu-Maiduguri, kai hare-hare garuruwan Askira, Buratai, Buni Yadi, da kuma lalata layukan wutar lantarki da ke haɗa Borno da Yoba," in ji Makama.

    Ya ce sojojin Najeriya na ci gaba da aikin fatattakar ƴan ta'ddan babu kakkautawa, duk da irin haɗari da wasu yankuna ke da shi, musamman ganin sansanonin ƴan ta'addan na cikin manyan dazuka da kuma binne abubuwan fashewa da suke yi kan hanyoyi da za su kai wurinsu.

  11. Masu iƙirarin jihadi sun yi garkuwa da farar hula 100 a Mali – Rahotanni

    Taswira

    Wasu rahotanni daga Mali sun ce aƙalla farar hula 100 ne suka tsinci kansu a hannun wasu da ake zargi masu iƙirarin jihadi ne bayan da suka yi garkuwa da su a makon da ya gabata.

    Wasu al'umma sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutanen na tafiya ne cikin motocin bas uku lokacin da maharan suka tilasta masu sauya aƙalarsu zuwa daji da ke tsakanin Bandiagara da Bankass.

    Kusan mako ɗaya da sace su, har yanzu ba a ji ɗuriyarsu ba.

    Yankin Mopti a Mali ya fuskanci hare-hare lokuta da dama daga masu ikirarin jihadi.

    Jama'a na ci gaba da nuna ɓacin rai biyo bayan kai hare-hare da aka kai yankin a baya-bayan nan.

    Ƙungiyoyin fararen hula a Bandiagara sun gudanar da zanga-zangar nuna fushinsu kan hare-haren ganin cewa sun ɗaiɗaita mutane da dama, inda suka yi kira da a kafa sansanin sojoji a yankin domin kare al'ummomi.

    Biyo bayan juyin mulki a shekara ta 2021, shugabannin mulkin sojin Mali sun umarci dubban dakarun ƙasashen waje da su fice daga ƙasar, abin da ya janyo take ci gaba da fuskantar barazanar hare-hare.

    Masu iƙirarin jihadi sun fara kai hare-hare a arewacin Mali sama da shekaru goma da suka gabata, kuma sun yaɗu zuwa tsakiyar ƙasar da kuma makwabtanta Burkina Faso da Nijar.

    Wannan ya janyo juyin mulki a waɗannan kasashe guda uku.

  12. Ƴan sandan Kenya sun cafke shugaban Binance da ya tsere daga Najeriya

    ..

    Rudunar ƴan sanda a Kenya ta kama jami'in kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla yayin da hukumar ƴan sanda ta duniya, Interpol ke neman tisa ƙeyarsa zuwa Najeriya a wannan makon.

    Majiyoyi daga gwamnati da suka san da shari'ar waɗanda suka nemi a sakaya sunansu saboda ba su da izinin yin magana kan batun sun tabbatar da labarin ga ƴan jarida.

    Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce ƴan sandan Kenya sun kama shugaban kamfanin Binance, Nadeem Anjarwalla kuma Interpol za a tisa ƙeyarsa zuwa Najeriya a makon nan.

    Wata majiyar ta ƙara tabbatar da kama Anjarwalla a Kenya.

    Bayanai na cewa gwamnatin Najeriya ta gano Anjarwalla a Kenya sakamakon tserewar da ya yi daga inda aka tsare shi a Najeriya.

    Hukumar EFCC da Interpol da rundunar ƴan sandan Kenya sun zurfafa tattaunawa domin hanzarta tisa ƙeyar Anjarwalla zuwa Najeriya.

  13. Tinubu na son a kafa rundunar bai-ɗaya domin yaƙar ta'addanci a Afirka

    ..

    Nijeriya ta bayyana buƙatar gaggawa ta ganin Cibiyar murƙushe ta'addanci a Afirka ta kama aiki gadan-gadan a ƙoƙarin dukkan masu ruwa da tsaki a nahiyar na kawar da ta'addanci.

    Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce lallai bai kamata ƙasashen Afirka su yi biris da tunanin kafa wata rundunar ko-ta-kwana a nahiyar ba, wadda ayyukanta za su haɗar da tunkarar ta'addanci.

    Ya bayyana haka ne yayin buɗe wani babban taron wuni biyu don ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe Afirka da bunƙasa cibiyoyin gwamnati, don shawo kan matsalolin ta'addanci.

    Kasashen Afirka dai musamman na yammaci na fama da matsalar tsaro da ke haddasa rasa dubban rayuka da tilasta miliyoyi barin muhallansu.

    Masana fannin tsaro na yi wa taron na Abuja kallon wani ɗan-ba da za a dasa wanda ka iya samar da bakin zare ga matsalar da ke ci wa yankin tuwo a kwarya.

  14. Ƙaruwar fursunoni ma su dakon shari'a na janyo cunkoso a gidajen yarin Kano

    Gidajen yari

    Hukumar da ke lura da gidajen gyaran hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta nuna damuwa kan ƙaruwar masu zaman jiran shari'a a gidajen yari da ke faɗin jihar.

    Wata sanarwa da kakakin hukumar reshen jihar Musbahu Lawan ya fitar, ta ce ƙaruwar mutanen da ke jiran a yanke masu hukunci na kawo wa hukumar cikas wajen gudanar da ayyukanta a jihar, inda ya ce yawan fursunoni masu jiran shari'a ya ninƙa har sau uku idan aka kwatanta da waɗanda aka yanke wa hukunci a jihar.

    "Fursunoni ma su zaman shari'a ya kai kashi 70 na ɗaukacin fursunoni da ake da su a faɗin jihar, ana tsare da yawancinsu duk da cewa kotu ba ta kammala yanke hukunci kan shari'o'insu ba," in ji Musbahu.

    Kofar Nasarawa ya ce idan da a ce an yanke wa mutanen da ke zaman jiran shari'a hukunci, to da hukumar ba za ta yi ƙorafi kan cikar gidajen yarin ba, saboda doka ta ba su damar sauya wa fursunonin da aka yanke wa hukunci wurin zama zuwa ko'ina a faɗin ƙasar.

    Ya ƙara da cewa an fi samun sauƙin kula da fursunonin da aka yanke wa hukunci saboda ana saka su cikin shirye-shiryen gyaran hali, wani abu da waɗanda ke zaman jiran shari'a ba su da damar morar sa.

    Mai magana da yawun gidajen gyaran halin, ya ce wasu fursunoni 38 waɗanda aka yanke wa hukunci sun zana jarrabawar kammala sakandare ta NECO, kuma suna neman gurbin karatu a Jami'ar karatu daga gida (NOUN).

    Musbahu ya ce duba da ƙaruwar fursunonin da suka nuna sha'awar karatu, hukumar na aiki da Jami'ar ta NOUN domin kafa ƙarin cibiyoyin karatu a gidajen yari a faɗin jihar.

    Ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa ɓullo da matakai na yi wa fursunoni afuwa domin shawo kan matsalar cunkoso a gidan gyaran hali.

  15. Rishi Sunak ya tsaya kai da fata kan mayar da masu neman mafaka Rwanda

    ..

    Firaministan Biritaniya, Rishi Sunak, ya yi alƙawarin cewa jiragen sama da za su fara jigilar wasu masu neman mafaka zuwa Rwanda za su tashi cikin makonni goma zuwa goma sha biyu masu zuwa.

    Mista Sunak ya ce yana da cikakken tabbacin cewa kudirin dokar zai sami goyon bayan majalisa ba tare da wata tantama ba.

    Ya ce "ya isa, babu sauran bata lokaci, majalisa za ta zauna yau, za ta kuma kaɗa ƙuri’a komin daren daɗewa, ko ta halin ƙaƙa waɗannan jiragen sai sun tafi Rwanda".

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa mutane da dama na goyon bayan ƙudurin amma masu suka na ganin manufar ba ta dace ba kuma mataki ne mai tsadar gaske.

  16. Ana zargin Narendra Modi da yin kalaman nuna ƙiyayya ga Musulmi

    ..

    Jam'iyyun adawa a Indiya sun zargi Firaminista, Narendra Modi, da yin kalaman nuna ƙyamar Musulunci a wajen wani gangamin zaɓe.

    A cikin jawabin nasa, Mista Modi ya yi zargin cewa idan aka zaɓi jam'iyyar adawa ta Congress za ta raba dukiyar al'ummar ƙasar ga masu kutse da kuma waɗanda ke da ƴaƴa da dama -- kalaman da ake yi wa kallon suna nuni ne ga tsirarun al'ummar Musulmi.

    Wakilin BBC ya ce ,masu fafutuka sun yi kira ga hukumar zabe ta kasar da ta gudanar da bincike kan ko kalaman Mista Modi sun saɓawa dokokin zaɓen ƙasar.

    Shugaban jam'iyyar Congress ya bayyana kalaman Mista Modi a matsayin kalaman tayar da zaune tsaye da kuma nuna ƙyama. Jam’iyyar BJP mai mulki na fatan lashe zaɓen ƙasar a karo na uku a jere.

  17. Hukumar 'yan gudun hijra a Gaza ba ta goyan baya kowane ɓangare - Guterres

    ..

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya amince da shawarwarin da ke da nufin tabbatar da cewa hukumar kula da 'yan gudun hijirar Falasdinawa ba ta goyi bayan ko wane bangare ba.

    A yau litinin ne za a saki rahoton wani kwamiti mai zaman kansa na hukumar - ƙarƙashin jagorancin tsohuwar ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna.

    A farkon wannan shekara wani rahoton hukumar leken asirin Isra'ila ya yi ikirarin cewa jami'an hukumar goma sha biyu na da hannu a harin da Hamas ta kai wa Isra’ila a ranar bakwai ga watan Oktoba.

    Duk da cewa a lokacin an kori waɗanda ake zargi, amma ƙasashe da dama sun daina bai wa hukumar tallafin kuɗaɗe.

  18. An samo gawarwaki fiye da 200 daga wani kabari a Khan Younis

    Hukumar tsaro ta Civil defence a Gaza ta ce yanzu haka an tsamo gawarwaki fiye da dari biyu daga wani katafaren kabari da ke harabar asibitin Nasser da ke Khan Younis.

    Hukumar - wadda ke ƙarƙashin ikon Hamas ta ce gawawwakin na karkashin harabar asibitin.

    Hukumar ta bayyana cewa wasu a cikin su an kashe su nan take ba tare da yi masu shari'a ba, yayin da wasu kuma an haƙo su ne daga wata maƙabarta ta hukuma da aka yi lokacin mamayar Isra'ila, sannan aka sake binne su.

    Isra'ila dai ta ce tana nazari kan rahotannin. Sojojin Isra'ila sun janye daga Khan Younis makonni biyu da suka wuce bayan tsanantar yaƙi a harabar asibitin.