Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, Umar Mikail da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    To jama'a a nan za mu dakata da kawo muku rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Fatan kun ji daɗin kasancewa da mu tun daga sanyin safiya zuwa yanzu.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. 'Muna yin kira na ganin an ƙara kai wa Gaza agaji'

    Babban jami'in kula da ayyukan jin kai na ƙungiyar Tarayyar Turai yana kira ga masu ba da tallafi na kasa da kasa da su agazawa hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Kiran da Janez Lenarcic ya yi ya biyo bayan fitar da rahoton wani kwamiti mai zaman kansa na hukumar wanda ya yi nazari kan iƙirarin Isra’ila na cewa ɗaruruwan ma’aikatanta da ke Gaza ƴan ta’adda ne.

    Wannan ikirari ya sa ƙasashe da dama sun dakatar da tallafin da suke bai wa hukumar.

    Binciken ya kammala da cewa ko da yake hukumar na da wasu tambayoyi a kan ta bisa ga batun nuna ɓangaranci, Isra'ila ba ta ba da wata shaida da ke tabbatar da zargin ba.

  3. Ana nuna damuwa kan ƙaruwar safarar mutane a Najeriya

    Safarar mutane

    Ana ci gaba da bayyana damuwa game da ƙaruwar mutanen da ake safararsu zuwa ƙasashen ketare don yin aikatau daga Najeriya.

    Wannan na zuwa ne bayan da hukumar yaki da fataucin bil'adama ta NAPTIP ta sanar da cewa sun kuɓutar da mutum 51 waɗanda aka yi yunkurin fita da su daga Najeriya ta jihar Kano.

    Bayanai na cewa a baya-bayan nan ɗimɓin mutane suna fita ketare ba bisa ka'ida ba don neman aiki, inda kuma idan aka yi rashin sa'a suke faɗa wa ayyukan bauta.

    Bayanan da wakilinmu Zahraddeen Lawan ya tattaro na cewa hukumar ta NAPTIP ta kama mutum biyu waɗanda suke da hannu wajen yunkurin safarar mutum 51 zuwa kasar Ivory Coast.

    Tun da farko hukumar Hisba ce ta kama mutanen wadanda suka kunshi mata 49 da maza biyu sannan suka mika su ga hukumar ta NAPTIP.

    Rahotanni na cewa matsalar safarar mutane na karuwa a sassan Najeriya.

    Kwamared Hafizu Sanka mukaddashin kodinatan hukumar kare hakkin ɗan Adam ta duniya a jihar Kano, ya ce irin waɗannan mutane idan aka yi rashin dace suna tsintar kansu a mummunan hali.

    Hukumar kare hakkin ɗan adam ta Najeriya reshen Kano ta ce ba iya wannan matar bace ta fuskanci irin wannan wahala, akwai waɗanda sai da aka kai musu ɗauki.

    Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam da kuma masu yaƙi da fataucin bil'adama sun jaddada cewa tilas sai hukumomi a matakai daban-daban sun tashi tsaye don magance wannan matsala ta hanyar haɗin gwiwa da jami'an tsaro da kuma hukumomin shige da fice.

    Sun kuma ce ya kamata gwamnati ta samar da kyakkyawan yanayin da zai sa mutane su daina fice wa daga ƙasar da kuma tabbatar da hukunta masu safarar mutane don ya zama izina ga masu niyyar aikata laifin.

  4. Isra'ila ta yi watsi da zargin binne gawawwakin Falasɗinawa a harabar wani asibiti a Gaza

    Sojojin Isra'ila sun yi watsi da zargin da ake musu na cewa dakarunsu sun binne gawarwakin Falasdinawa a harabar wani asibiti da ke Gaza.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar IDF ta bayyana zargin Falasdinawa a matsayin mara tushe balle makama.

    Sojojin Isra’ila sun ce sun binciki gawawwakin Falasdinawan domin su tabbatar da cewa ba ƴan Isra'ila da aka yi garkuwa da su ba ne, amma daga baya sun sake binne su a inda suka same su.

    IDF ta kara da cewa daidaitaccen hari ne aka kai wa mayakan Hamas a yankin.

  5. EFCC ta kama tsohon ministan sufurin jirage Hadi Sirika

    Hadi Sirika

    Hukumar yaƙi da cinhanci da rashawa a Najeriya EFCC ta kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika bisa zargin almundaha.

    Mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya faɗa wa BBC cewa suna tsare da ministan ne bisa zargin aikata ba daidai ba a lokacin da yake minista.

    "Ina tabbatar muku da cewa muna tsare da shi...amma ba zan iya faɗa muku adadin kuɗin da ake zargi ba har sai an kammala bincike," kamar yadda ya bayyana ta waya.

    Wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya na cewa hukumar na zargin Sirika ne da almundahanar kuɗin da suka kai naira biliyan takwas.

    Hadi Sirika ya riƙe muƙamin ministan sufurin jirgin sama kusan shekara takwas - farko a matsayin ƙaramin minista kafin daga baya ya zama babban minista.

    Tsohon ministan ya tayar da ƙura lokacin da ya ƙaddamar da kamfanin sufurin jirgin sama na Nigeria Air 'yan kwanaki kafin ƙarewar wa'adin gwamnatinsu a watan Mayu, wanda har yanzu bai fara aiki ba.

  6. 'Abin tashin hankali ne yadda aka lalata cibiyoyin lafiya a Gaza'

    Babban jami'in kare hakkin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya ce abin tashin hankali ne yadda aka lalata cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza da kuma gawawaki fiye da dari biyu da aka gano a wani katafaren kabari.

    An ba da rahoton cewa an kashe wasu a kai tsaye ba tare da wata shari’a ba- wasu kuma an sake binne su ne bayan an tono su daga wata makabarta da aka kaddamar a lokacin da Isra'ila ta yi wa yankin kawanya.

    Ravin Shamdasani ita ce mai magana da yawun Mr Turk:

    Kowane minti goma ana kashewa ko kuma raunata yaro. Zan bari ku yi lissafin yara nawa ne aka kashe ko aka raunata tun lokacin da aka fara wannan bitar a yau, an ba su kariya a karkashin dokokin yaki, amma duk da haka su ne wadanda ke fuskantar munin wannan lamarin.

    Mista Turk ya kuma yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ta kai yankin a baya-bayan nan, wanda ya ce ya yi sanadiyar mutuwar mata da kananan yara.

  7. Mun rufe asusun banki 300 kan canjin kuɗin ƙasashen waje - EFCC

    Ola Olukoyede

    Shugaban hukumar yaƙi da cinhanci ta EFFC a Najeriya ya ce sun yi nasarar gano wani sabon dandalin canjin kuɗin ƙetare "da ya fi dandalin Binance muni".

    Ola Olukoyede ya ƙara da cewa hakan ya sa suka rufe asusun banki 300 bisa umarnin kotu da ke da alaƙa da dandalin, wanda ya ce sunansa "P to P" - ko kuma peer- peer.

    "Abin da muka gano shi ne ɗaya daga cikin waɗannan asusun ya yi kasuwancin kuɗi sama da dala biliyan 50 cikin shekara ɗaya ba tare da bankuna sun sani ba, kuma babu wanda ya sani," in ji shi yayin taron manema labarai a yau Talata.

    Ya ƙara da cewa sun gano "akwai mutanen da suke aikata ɓarnar da ta fi ta Binance".

    Game da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, Mista Olukoyede ya ce "ba don sun kai zuciya nesa ba da sun yi musayar wuta da jami'an tsaronsa" lokacin da suka je kama shi a Abuja.

  8. Ɓarkewar sabon faɗa a Habasha ya raba mutum 50,000 da muhallansu - MDD

    Habasha

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sabon faɗan da ya ɓarke a wani yanki da ake takaddama a kai a arewacin Habasha, ya raba mutane sama da 50,000 da muhallansu.

    Dakarun da ke hamayya da juna daga yankunan Tigray da Amhara sun fara fafatawa ne mako guda da ya gabata a gundumar Raya Alamata da dukkansu ke iƙirarin mallaka.

    Yankin ya kasance na al'ummomin Tigray har zuwa karshen shekarar 2020 lokacin da yaƙin basasa ya ɓarke tsakanin ƴan tawayen Tigray da gwamnatin Habasha.

    Daga baya dakarun Amhara suka ƙwace yankin suna masu ikirarin cewa asalin yankin nasu ne.

    Fiye da mutane miliyan huɗu ne ke gudun hijira a ƙasar Habasha, akasarinsu sakamakon tashe-tashen hankula.

  9. Ɓata-gari sun lalata turakun wutar lantarki, sun saka Gombe da Yola da Jalingo cikin duhu

    Wutar lantarki

    An jefa al'ummomin garuruwan Gombe, Yola da kuma Jalingo cikin duhu bayan da wasu bata-gari suka lalata turakun wutar lantarki guda huɗu a kan hanyar Jos zuwa Gombe mai karfin mega watt 330.

    Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, kamar yadda babbar manajan kamfanin rarraba lantarki ta kasa (TCN), Ndidi Mbah ta bayyana a ranar Talata.

    Ta ce hakan ya janyo katsewar wutar lantarkin da tashoshin Gombe, Yola, da kuma Jalingo ke bayar wa.

    "Lalata turakun wutar ya kuma shafi yawan wutar lantarkin da kamfanonin rarraba wuta ke bayar wa a sassan Yola da Jos," in ji Ndidi.

    Ta ce TCN na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an mayar da wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa.

    'Muna kuma yin ƙoƙari domin sake gyara turakun wutar lantarku guda huɗu da aka lalata," in ji sanarwar da hukumar ta fitar.

  10. 'Mutum miliyan 50 za su fuskanci ƙarancin abinci a yammacin Afrika da Sahel'

    Masana ilmin yanayi sun yi gargaɗin cewa fiye da mutum miliyan 50 ne za su iya fuskantar karancin abinci a yankin kasashen yammacin Afirka da na Sahel.

    Masanan sun ce za a iya fuskantar wannan lamari a tsakanin watannin Yuni da Oktoba, inda suka ta’allaka hakan da kalubalen tsaro da koma baya a sha’anin noma da kuma rashin saukar damina da wuri.

    Ku latsa ƙasa don sauraron tattaunawar da Zubairu Ahmad ya yi da Farfesa Almustapha Dankani, na Sashen Nazarin Ilmin Kasa da Yanayi a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto.

    Video content

    Video caption: Latsa sama don sauraron tattaunawar
  11. Yaƙin Gaza: Sojojin Isra'ila sun yi lugudan wutar da ba a taɓa gani ba tun fara yaƙi

    Gaza

    Sojojin Isra'ila sun yi lugudan wuta mai zafi a Gaza, kwanaki 200 da fara yaƙi.

    Yawancin lugudan wutar ta afku ne a yankin arewacin Gaza.

    Mai magana da yawun sojojin Isra'ila ya ce an kai harin kan wurare 25, ciki har da shingayen sa ido na sojoji da ke kudancin yankin.

    Hezbollah - wadda ta ƙara yawan hare-haren roka da take kai wa Isra'ila - ta sanar da mutuwar mambobinta guda biyu, inda Isra'ila ta kashe ɗaya daga ciki a wani harin sama da ta kai kusa da birnin Tyre na Lebanon.

    A ɗaya gefen, Qatar - wadda ke shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wuta - ta musanta rahotanni da ke cewa ta faɗa wa Hamas ta mayar da hedkwatar siyasarta zuwa Dubai.

  12. Majalisar dokokin Burtaniya ta amince da kai masu neman mafaka Rwanda

    Majalisar dokokin Birtaniya ta amince da wani kudurin doka da ya dade ana ta jinkiri a kansa, na neman tura masu neman mafaka a Birtaniya zuwa Rwanda.

    Wakilin BBC ya ce an dauki tsawon lokaci ba a cimma wannan matsaya ba saboda yadda aka samu tirjiyar wasu daga cikin ƴan majalisar na ƙin amincewa da ƙudurin.

    Kudirin ya bayyana Rwanda a matsayin kasa mai aminci bayan da kotun koli ta yanke hukunci a watan Nuwamba cewa matakin gwamnatin ya saɓa doka.

    Firaiministan Burtaniya dai, Rishi Sunan ya kafe kai da fata kan ganin wannan ƙudiri ya kai ga gaci.

  13. Mutum 16 sun mutu a kifewar kwale-kwale a tekun Dijobouti

    Kifewar kwale-kwale

    Hukumar kula da ƴan ci-rani ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutane 16 sun mutu sannan 28 kuma sun ɓata bayan da wani kwale-kwale ya kife a tekun ƙasar Djibouti.

    IOM ta ce yawancin mutane da ke cikin kwale-kwalen sun kasance yara.

    Aƙalla mutum 38 ne suka mutu a wani hatsarin kwale-kwale a tekun makonni biyu da suka wuce.

    Jami'ai sun ce a tsawon shekara goma da suka gabata, kusan dubban mutane ne suka mutu ko kuma suka ɓata a bulaguro ta hanyar jirgin ruwa.

    Tekun dai ya kasance hanyar da ƴan ci-rani daga kusurwar Afrika ke amfani da shi wajen zuwa Yemen, don neman aiki a Saudiyya ko sauran ƙasashen Larabawa.

  14. Tunisia da Algeria da Libya na ƙoƙarin haɗa ƙawance

    ..

    Tunisiya ta gudanar da taron koli da kasashen Aljeriya da Libya a kokarin da suke na samar da wani sabon ƙawancen yankin.

    Babbar abokiyar hamayyar Algeria - Maroko - ba ta halarci taron ba kamar yadda Mauritania ma ba ta halarta ba.

    Ƙasashen biyar dai su ne suka haƊu suka hada ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta Maghreb wadda aka kafa tun 1989, sai dai ta kwashe shekaru ƙungiyar ba ta aiki saboda takun saƙar da ke tsakanin wasu daga cikin ƙasashen.

    Taron ya amince da yin ƙawance wajen yaƙar kwararar baƙin haure da samar da wutar lantarki da kuma shigi da fici na kaya da na ƴan kasashen.

  15. Matar da ke fafutukar taya mutane su kashe kansu ta mutu

    ..

    Matar nan ƴar ƙasar Peru - mai fafautukar taimaka wa mutane wajen kashe kansu, wadda ke tsananin jin jiki a asibiti, ta rasu.

    Ana Estrada ta mutu ne bayan da likitanta ya ba ta maganin da ta fiye da ƙima.

    Wakiliyar BBC ta ce a cikin wata sanarwa da lauyanta ya fitar, ya ce ta rasu ne ta hanyar da take fata, domin dai tana ta ƙoƙarin ganin ta kashe kanta tsawon shekaru takwas.

    Ana Estrada dai ƙwarararriya ce a ɓangaren sanin hallayar dan adam ta kuma yi fama da jinya ta tsawon shekaru.

  16. Unai Emery ya tsawaita kwantiragi a Aston Villa zuwa 2027

    Unai Emery

    Kocin Aston Villa Unai Emery ya amince ya tsawaita kwantiraginsa a ƙungiyar har zuwa 2027.

    Emery ya karɓi ragamar Villa ne a hannun Steven Gerrard a watan Nuwamban 2022, lokacin da ƙungiyar ke mataki na 16 a teburin Premier kuma suna dab da faɗa wa gasar ƴan dagaji.

    A kakarsa ta farko a Villa, ya taimaka mata karewa a mataki na 7 a gasar Premier da kuma samun damar zuwa gasar Europa wanda rabon ta je tun kakar 2010/2011.

    A wannan kakar kuwa, suna matsayi na huɗu a teburin Premier, inda suke da burin zuwa gasar Champions League.

    Suna da maki shida a gaban Tottenham, wadda ke da kwanten wasanni biyu.

    Tagomashin Unai Emery za taƙaru matuka idan har ya taimakawa ƙungiyarsa ta ɗauki kofin Conference, inda za su fafata da Olympiakos a wasan kusa da na karshe.

  17. Zanga-zangar ɗalibai ta goyon bayan Falasɗinawa na bazuwa a Amurka

    ..

    Zanga-zangar da daliban jami'o'i ke yi ta nuna adawa da yaƙin da ake a Gaza ta bazu zuwa yankin Columbia da Yel {Yale} da wasu jami'o'in.

    Wannan dai na zuwa ne bayan da hukumomi suka yi yunƙurin kawo karshen zanga-zangar.

    A daren jiya Litinin ne 'yansanda sun far wa masu zanga-zangar a birnin New York, tare da kama da dama.

    Jami'ar ta ce ta samu rahotannin da ke nuna masu zanga-zangar na rera wakokin nuna ƙyama ga Yahudawa.

  18. Ƴan sanda za su yi bincike kan makarantar Lead British

    ..

    Rundunar ƴan sanda a Abuja, babban birnin Najeriya ta ce ta aika tawagar ƙwararrun jami'anta zuwa makarantar Lead British bayan bidiyon yadda wata ɗaliba ke cin zalin ƴar ajinsu ya bazu a shafukan sada zumunta.

    Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta ce rundunar ta san da abin da ya faru kuma tana ɗaukan mataki a kai.

    A cewar kakakin, ƴan sandan da aka tura za su gudanar da bincike tare da hana karya doka da oda.

    A ranar Litinin ne bidiyon da ke nuna yadda ake cin zalin wata ɗaliba ya karaɗe shafukan sada zumunta lamarin da ya fusata al'ummar Najeriya.

    Tuni dai hukumar makarantar ta fitar da sanarwa inda ta nemi yafiyar al'umma da kuma iyayen ɗaliban makarantar sannan ta ce ta soma bincike kan lamarin.

  19. An kama matasa uku kan zargin garkuwa da mutane a Nasarawa

    ..

    Rundunar ƴan sanda a jihar Nasarawa ta cafke wasu matasa uku kan zarginsu da haɗa baki don yunƙurin yin garkuwa da kawun ɗaya daga cikinsu.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Rahman Nansel ya sanyawa hannu, waɗanda ake zargi sun yi barazanar sace mutumin idan ya ƙi biyansu kuɗin fansa.

    Sanarwar ta ce fargabar kada a sace shi ta sa mutumin ya tanadi kuɗin da matasan suka buƙaci ya ba su, inda ya ajiye shi a wurin da suka nema daga nan kuma suka kwashi kuɗin tare da rabawa a tsakaninsu.

    Waɗanda ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da yi sannan sanarwar ta ce ana ƙoƙarin bankaɗo wanda ya tsere.