Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, A'isha Babangida da Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za dawo domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokani aiki Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  2. Rufewa

    Masu bin shafin Kai tsaye na BBC nan muka kawo ƙarshen labaran shafin namu.

    Sai kuma gopbe idan Allah ya kai mu.

    A madadin sauran Abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya

  3. 'Yan sandan Najeriya na ci gaba da tsare ɗan jaridar FIJ

    Lauyoyin wani dan jarida mai binciken kwakwaf a Najeriya sun ce ya shafe fiye da mako ɗaya a tsare a hannun 'yan sanda ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba, kan zargin da ake masa na saba dokar amfani da intanet.

    Batun kama dan jaridar ya já hankalin masu fafutikar kare hakkin 'yan jarida a Najeriya da wajen ƙasar. Sai dai babu wani bayani daga ɓangaren yan sandan Najeriya.

    Batun kama danjaridar ya já hankalin masu fafutikar kare hakkin 'yan jarida a Najeriya da wajen kasar.

    Sai dai babu wani bayani daga ɓangaren 'yan sandan na Najeriya.

    Kamar FIJ da ke binciken kwakwaf a Najeriya ta yi zargin cewa 'yan sanda sun kama dan jaridarta ne mai suna Daniel Ojukwu kan labarinsa na watan Nuwamba da ya bankaɗo badalaƙar rashawa a gwamnati

    Kafar ta ce tun 1 ga watan Mayu ɗan jaridar ya yi ɓatan dabo, sai daga baya rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da manema labarai a ranar Lahadi cewa tana tsare da ɗan jaridar.

    Kuma yana tsare ne a sashen da ke binciken laifukan intanet ne bayan koken da aka gabatar a kansa.

    Ƙarƙashin dokar Najeriya dai, ya zama tilas a gurfanar da wanda ake zargi cikin sa’a 48 bayan kama shi.

    Kan wannan dalilin ne batun kama shi ya ja hankalin ƙungiyoyin kare hakkin 'yan jarida.

    Kungiyar kare 'yan jarida ta duniya CPJ ta yi kiran gaggauta sakin ɗan jaridar, inda ta ce tsakanin 2015 aƙalla 'yan jarida 25 ne aka tuhuma da aikata laifuka a intanet

    Masu suka da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi zargin cewa ana amfani da dokar domin murƙushe 'yan jarida da faɗin albarkacin baki

    Alƙalumman 2024 sun nuna Najeriya ce kasa ta 112 a jerin kasashe 180 da aka fi ƙuntata wa 'yan jarida

  4. Stormy Daniels ta yi musayar kalamai da lauyoyin Trump

    .
    Image caption: Mista Trump ya sha musanta alaƙa da Stormy Daniels

    Fitacciyar tauraruwar fina-finan batsa ta Amurka, Stormy Daniels ta yi musayar kalamai da tawagar lauyoyin Donald Trump, a lokacin da ta ke bayar da shaida a shari'ar da ake wa tshohon shugaban kasar na aikata laifuka a New York.

    Tsohon shugaban na Amurka ya musanta yin ƙarya a bayanan kasuwanci don ɓoye kuɗin toshiyar baki da aka biya Ms Daniels kan alaƙar da ta shiga tsakaninsu a 2006.

    Donald Triump ya daɗe yana musanta yin lalata da Stormy Daniels, kuma a yau lauyansa ya nemi ya warware duk shaidar da ta bayar inda ya zarge ta kai-tsaye da kitsa labarin ƙanzon kurege.

    Masu gabatar da kara sun ce biyan kuɗaɗen da aka yi ya kasance tamkar maguɗin zaɓe, sakamakon ya zo daf da nasaran da Mista Trump ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2016.

  5. Succes Masra ya zargi wasu mutane da sauya sakamakon zaɓen Chadi

    ..

    Dan takarar shugabancin ƙasar Chadi - wanda kuma shi ne firaministan ƙasar, Succes Masra - ya zargi wasu mutane da bai ambaci sunansu ba da ƙoƙarin sauya sakamakon zaɓen.

    Zargin nasa na zuwa ne a daidai lokacin ake sa ran hukumar zaɓen ƙasar na dab da bayyana wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Litinin.

    Ya ce “Muna sane da wasu mutane da ke yunƙurin cusa wa mutane tunanin cewa wani tsari da ya kwashe gomman shekaru yana mulkar Chadi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen,” in ji Masra.

    Ya ƙara da cewa “suna so mu yadda da wani tsari, suna so su sauya alƙaluma,” sai dai bai bayyana wata ƙwaƙƙwarar hujjar hakan ba.

    Tun da farko a yau, jam'iyyarsa ta wallafa wani saƙo a shafin Facebook da ke cewa kashi 80 na 'yan ƙasar sun zaɓi chanji ne.

    To amma cikin jawabin da ya gabatar Mista Masra ya ce ''Duka mun sani cewa suna son yi mana fashi da nasara'', inda ya yi kira ga magoya bayansa su yi gangamin lumana a daidai lokacin da ake dakon sakamakon zaɓen.

    “Al'ummar Chadi kada ku yarda a sace muku ƙaddarku,” in ji Masra.

    Gabanin kaɗa ƙuri'ar dai, hukumar zaɓen ƙasar ta gargaɗi ɗaiɗaikun mutane da 'yan takara kan wallafa ko yaɗa sakamakon zaɓen a shafin sada zumunta, saboda kauce wa ruɗani.

    A cikin daren yau ne ake sa ran hukumar zaɓen ƙasar za ta bayyana sakamakon zaɓen.

  6. 'Yan sanda sun kama wani mutum kan zargin kisan abokinsa a Kano

    .

    Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu, bisa zargin kisan abokinsa Bello Bukar Adam wanda ma'aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki ta KEDCO ne.

    Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ya ce a ranar 5 ga watan Mayu ne rundunar 'yan sanda ta samu ƙorafin ɓatan Bello Bukar Adam mai shekara 45, wanda aka ce ya bar gida tun ranar 4 ga watan Mayun.

    Sanarwar ta ce a ranar ne kuma 'yan sanda suka samu rahoton tsintar gawar mutumin, wanda aka jefar a ƙauyen Bechi da ke yankin ƙaramar hukumar Kumbotso, inda nan take rundunar 'yan sanda ta tura tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin DPO na ƙaramar hukumar, inda suka ɗauko gawar zuwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

    Inda nan take rundunar 'yan sanda ta ƙaddamar da bincike tare da kama wani mutum mai suna Sadiq Zubairu mai shekara 35 da ke unguwar Hotoron Arewa bisa zargin aikata laifin.

    SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce a lokacin da 'yan sandar ke tuhumar wanda ake zargin, ya amsa cewa ya haɗa baki da wasu mutum biyu wajen fito da Bello - wanda ya kasance abokinsa ne - daga gidansa.

    Sadiq ya shaida wa 'yan sanda cewa da kansa ya ɗaure Bello inda suka rika dukansa da sanduna da ƙarafa masu kaifi a kansa da sauran sassan jikinsa har sai da ya mutu.

    ''Bayan ya mutu ne suka sanya shi jikin but ɗin motarsa, tare da jefar da gawar a kan titin Eastern Bypass, a daidai ƙauyen Bechi, inda suka gudu da motar, ƙirar Toyota Corolla 2015, da kuma wayar marigayin'', kamar yadda sanarwar 'yan sandan ta yi bayani

    Haka kuma wanda ake zargin ya shaida wa 'yan sandan cewa ya karɓi naira miliyan uku a wajen marigariyin da zummar zai sama masa aiki, kuma aikin bai samu ba, daga nan kuma sai ya yi yunƙurin kashe shi tare da yin awun gaba da motarsa inda suka ɓoyeta wani gareji da ke unguwar Hotoro.

    Tuni dai 'yan sanda suka kwato motar.

  7. Yunƙurin wata mahaifiya don shigar da ɗanta Masar ya gamu da cikas

    Wata mahaifiya, wadda ɗanta, Amin ke samun kulawa a asibitin al-Aqsa da ke tsakiyar Gaza - ta shaida wa BBC yadda ya kamata a ce an miƙa ɗan nata Masar ta mashigar Rafah.

    Wannan ƙudirin, a cewarta, a yanzu ya fuskanci tsaiko.

    "Lafiyar ɗana na ƙara taɓarɓarewa," in ji mahaifiyar, inda ya ce farmakin da ake kai wa Rafah ya sa ta kasa tsallakawa mashigar da ɗanta.

    "Ina ta fama tsawon fiye da wata uku a asibitin al-Aqsa, ina zaune a nan inda nake cikin takaici kowace rana saboda yanayin da ɗana ke ciki."

  8. Kai hari ta ƙasa kan Rafah ba zai murƙushe Hamas ba – John Kirby

    ..

    Amurka ta ce Isra'ila na kai farmaki kan birnin Rafah da ke kudancin Gaza ba zai haifar wa Isra'ila ci gaba ba ko ma cimma ƙudurin Amurkar na murƙushe Hamas.

    Mai bai wa fadar White House shawara kan sha'anin tsaro, John Kirby ya ce shugaba Joe Biden bai yadda cewa kai hare-hare a Rafah zai ciyar da wannan ƙudiri gaba.

    Kirby ya ƙara da cewa akwai wasu hanyoyi da suka fi dacewa a bi don murƙushe Hamas a Gaza a maimakon ƙaddamar da samame ta ƙasa.

  9. An tsare wani mutum kan zargin shiga gidan mawaƙi Drake

    ..

    Ƴan sanda a Kanada sun tsare wani mutum saboda zarginsa da yunƙurin shiga gidan mawaƙi Drake a Toronto.

    An kama mutumin bisa dokar lafiyar ƙwaƙwalwa inda kuma aka ba shi kulawa.

    A ranar Talata ne, aka jikkata wani mai gadin gidan sakamakon harbe-harbe.

    Ƴan sanda ba su ce akwai alaƙa tsakanin hare-haren ba.

    A yanzu dai Drake na takun saƙa da abokin hamayyarsa Kendrick Lamar.

    Wani hoton gidan Drake da aka ɗauka ta sama shi ne hoton da aka sa a faifan waƙoƙin Lamar na baya-bayan nan.

    Sai dai ba a danganta tsamin dangantakar tasu ba da abubuwan da ke faruwa a baya-bayan nan.

  10. Majalisar dattawan Najeriya ta amince da hukuncin kisa ga masu safarar ƙwaya

    ..

    Majalisar dattawan Najeriuya ta amince da ƙudurin dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar, bayan ƙudurin ya tsallake karatu na uku a zauren majalisar.

    Majalisar ta amince ta ƙudurin bayan kwamitin majalisar kan ayyukan yaƙi da fataucin miyagun ƙwayyoyi, ƙarƙashin jagorancin Sanata Tahir Munguno ya gabatar da rahotonsa kan sabuwar dokar a zauren majalisar.

    Yayin da take sake nazarin dokar, majalisar ta amince da dokar hukuncin kisan ne domin ƙarfafa ayyukan hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar.

    A lokacin muhuwar, babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Peter Nwebonyi ya nemi majalisar ta amince da dokar hukuncin kisa ga masu safarar miyagun ƙwayoyin, maimakon ɗaurin rai -da-rai.

    A lokacin da aka nemi ra'ayin sauran 'yan majalisar dangane da batun, majalisar ta nuna amincewarta kan dokar ciki har da mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar.

    To sai dai wasu tsirarun 'yan majalisar ba su goyi bayan ƙudurin ba, inda Sanata Adams Oshimole ya kasance cikin masu nuna adawa da dokar.

    To sai dai mataimakin shugaban majalisar dattawan, Sanata Barau Jibril ya yi watsi da buƙatar sanata Oshimolen, yana mai cewa ƙorafin sanatan ya saɓa wa dokar majalisar saboda ƙorafin ya zo ne bayan majalisar ta amince da ƙudurin.

  11. Somaliya ta nemi MDD ta kawo ƙarshen ayyukanta a ƙasar

    Gwamnatin Somaliya ta buƙaci a kawo ƙarshen ayyukan siyasa na Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar inda ta ce ba shi da amfani.

    Wata wasiƙa zuwa ga kwamitin sulhu na MDD ta nemi a gaggauta kawo ƙarshen ayyukan idan wa'adi ya cika a watan Oktoba.

    Ƴan siyasar Somaliya sun zargi jami'an MDD da sa baki a sharkokin cikin gida na ƙasar.

    Buƙatar kawo ƙarshen ayyukan MDD ya yi daidai da sauye-sauyen kundin tsarin mulki da aka samu wanda masu suka suka ce an yi ne domin ƙara wa'adin gwamnati mai ci.

  12. Dakarun Mali sun musanta kai farmaki a Mauritaniya

    .

    Rundunar sojin Mali-FAMa ta musanta zargin kai hare-hare kan mayaƙan sa kai a yankin Mauritaniya yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu.

    Hakan na zuwa ne sakamakon soma atisayen soji da dakarun Mauritaniya suka yi a kan bodar ƙasar da Mali a ƴan kwanakin nan wanda hakan ya yi kama da martani kan zargin kutsen da FAMa da sojojin hayar Rasha na Wagner da ke faɗa da mayaƙan sa kai a yankin suka yi. Kafafen yaɗa labarai na Mali sun fasalta atisayen a matsayin "gargaɗi" ga Mali.

    Shuguban sashen fitar da labarai na FAMa Kanar Manjo Souleymane Dembele a taron manema labarai da aka yi a ranar 7 ga watan Mayu ya musanta zargin.

    "Mun zo wajen nan domin mu faɗi gaskiya. Mun ce ba mu taɓa ƙetare iyakar Mali don shiga Mauritaniya ba. Babu lokacin da dakarun sojin Mali suka tsallaka iyaka don aiwatar da wani aiki a Mauritania", a cewar Dembele.

    Ya ƙara da cewa "A hukumance sojojin Mali ba su taɓa shiga Mauritaniya ba".

    Bayanan sun zo ne bayan rahoton kashe farar hula 13 a garin Mourdiah da ke kusa da iyakar da Mauritaniya yayin wani hari na FAMa da Wagner.

  13. Saudiyya ta bayar da izinin amfani da ƙarfi don gina birni mai dausayi

    ...

    Hukumomin Saudiyya sun ba da izinin yin amfani da ƙarfi don kakkaɓe filaye a wani garin da ake gina birni mai dausayi da ake kira Neom, wanda kamfanoni da dama na ƙasashen Yammacin duniya ke ginawa, kamar yadda wani tsohon jami’in leƙen asiri ya shaida wa BBC.

    Kanal Rabih Alenezi ya ce an umarce shi ya kori mutanen ƙauyen, don ba da hanyar a kafa 'The Line', wani ɓangare na aikin samar da birnin dausayi na Neom.

    Daga bisani an harbe ɗaya daga cikinsu wanda ya nuna rashin amincewa da umarnin.

    Gwamnatin Saudiyya da shugaban Neom ba su ce komai ba game game da rahoton.

    Neom, wani dausayi ne a da Saudiyya za ta kashe dalar Amurka biliyan 500 wajen ginawa, a wani ɓangare na burinta zuwa 2030 don bazakomar tattalin arzikinta daga dogara da man fetur.

  14. Yawan basussukan Masar sun ninka sau huɗu a shekara takwas

    Babban bankin Masar ya ce basussukan da ake bin ƙasar sun ƙaru da ninki huɗu cikin shekaru takwas da suka gabata.

    A yanzu, yawan basussukan ƙasar sun kai rabin arzikin da ƙasar ke samarwa.

    Masar na kashe maƙudan kuɗi kan tsaro da farfaɗo da darajar kuɗin ƙasar da ya durƙushe.

    Ana kuma gina katafaren gini da ya laƙume dala biliyan takwas a gabashin birnin Alƙahira.

    Shi ne ɗaya daga cikin zaɓaɓɓun ayyukan shugaba Abdul Fattah al-Sisi.

    Ya ce zai rage cunkuso a birnin na Alƙahira. Sai dai masu suka na cewa gini ne mai tsada kuma kamata ya yi a mayar da hankali kan yaɗa damarmakin bunƙasa tattalin arziki a sassan ƙasar a don haka babu dole ga mutane su koma Alƙahira.

  15. Muna zargin Biden da ƙaunar Hamas bayan daina samar mana makamai – Isra’ila

    ..

    Ministan harkokin cikin gida na Isra'ila mai ra’ayin riƙau ya yi allah wadai da matakin da shugaba Biden ya ɗauka na ƙin samar da makaman Amurka da za a iya amfani da su a gagarumin farmakin da Isra'ila za ta kai kan birnin Rafah.

    Itamar Ben Gvir ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa Hamas na ƙaunar Biden amma Shugaban kasar Isra'ila, Isaac Herzog, ya bayyana kalaman ministan a matsayin masu nuna rashin dattaku.

    Da yake jawabi yayin bikin tunawa da nasarar da aka samu a kan Jamus a yaƙin duniya na biyu, Mista Herzog ya gode wa shugaba Biden da Amurka kan goyon bayan da ƙasarsa ke samu.

    Wakiliyar BBC ta ce rahotanni daga kafofin yada labaran Isra’ila na nuni da cewa jami’an tsaron ƙasar sun nuna matuƙar damuwa kan shawarar da babbar ƙasa mai samar masu da makamai ta ɗauka domin hakan na iya kawo cikas a ɓangaren tsaron Isra’ila.

  16. Hotunan halin da Falasɗinawa ke ciki a Rafah bayan hare-haren Isra'il

    ..
    Image caption: Wani yaro yana zaune a kan ɓuraguzain gini a wani wuri da aka kai wa hari a Rafah.
    ..
    Image caption: Yara sun zauna kusa da wasu kayayyakin jama'a a daidai lokacin da Falasɗnawa ke ci gaba da tserewa daga Rafah bayan umarnin da aka ba su na su fice.
    ..
    Image caption: Falasɗnawa sun taru a wani gida da aka kai wa hari a Rafah.
    ..
    Image caption: Sojojin Isra'ila sun taru a wani wurin da ba a sani ba kusa da shingen da ke iyakar Zirin Gaza da kudancin Isra'ila.
  17. An aikata kisan ƙare-dangi kan ƙananan ƙabilu a Sudan - HRW

    ...

    Akwai alamun da ke tabbatar da cewa an aikata kisan kiyashi a birnin El Geneina na jihar kudancin Darfur a ci gaba da yaƙin da ake gwabzawa a Sudan, kamar yadda wani rahoton Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ya bayyana.

    Rahoton ya ce kisan kiyashin na daga cikin ayyuka mafi muni da aka aiwatar a yaƙin basarar da ke gudana a Sudan.

    Ya ƙara da cewa dakarun RSF masu faɗa da gwamnati da dangoginsu ne suka aikata kisan ƙare-dangi da laifukan yaƙi a kan mutane ƴan ƙabilar Masalit da kuma sauran ƙabilun da ba Larabawa ba.

    Rahoton ya buƙaci a sanya takunkumi kan waɗanda ake ganin su ne ke da hannu a laifukan, ciki har da jagoran dakarun na RSF, Mohammed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hemeti.

    Majalisar dinkin duniya ta ce akwai yiwuwar an kashe mutum kimanin 15,000 a birnin El Geneina a shekarar da ta gabata kawai.

  18. Majalisar wakilan Najeriya ta umarci CBN ya dakatar da harajin tsaron intanet

    ...

    Mambobin majalisar wakilan Najeriya sun umarci babban bankin ƙasar, CBN ya janye aiwatar da harajin tsaro na intanet da zai cire kashi 0.5 cikin ɗari a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki.

    'Yan majalisar sun bayyana matakin a matsayin abu mai sarƙaƙiya.

    Wannan buƙatar dai na zuwa ne a matsayin martani ga wani kuduri kan bukatar gaggawa na dakatar da gyara aiwatar da harajin tsaron intanet, wanda Kingsley Chinda ya gabatar.

    A cewar ƴan majalisar, CBN ya janye takardar aiwatar da tsarin da ya fitar , sannan kuma ya fayyace tsarin yadda 'yan Najeriya za su fahimta.

    Majalisar ta kuma nuna damuwa kan cewa za a aiwatar da dokar cikin kuskure idan ba a dauki matakin gaggawa ba, don magance matsalolin da ke tattare da fassarar umarnin na CBN da kuma dokar tsaro ta Intanet.

    A ranar 6 ga watan Mayun shekarar 2024 ne babban bankin kasar CBN, ya fitar da wata sanarwa da ta umarci dukkan bankun da masu gudanar da hada-hadar kudi ta wayar salula su aiwatar da wani sabon harajin tsaro ta intanet saboda hana aikata laifuka ta intanet.

  19. Benin ta buƙaci gwamnatin Nijar ta sake duba dangantakar da ke tsakaninsu

    ...

    Shugaban kasar Benin, Patrice Talon, ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar dangantaka da makwabciyar ƙasarsa Nijar inda Nijar ke ci gaba da rufe iyakar ƙasashen biyu a cewar rahoton da RFI ta fitar.

    A ranar 6 ga watan Mayu, kasar Benin ta hana fitar da mai daga Nijar ta hanyar bututun mai da ke hade rijiyoyin mai a Nijar da tashar ruwan Cotonou a Benin saboda ci gaba da rufe iyakokin.

    A cikin wata sanarwa da RFI ta ruwaito, shugaban ya bayar da hujjar yanke hukuncin, ya kuma kara da cewa yana da sha'awar sake bude iyakokin kasar da daidaita alakar kasashen biyu.

    “Na ji bakin ciki da tabarbarewar dangantakar da ke tsakanin Nijar da Benin, kasashe biyu abokan juna da juna,” in ji shi."

    "Daukar Benin a matsayin kasa makiya da yaɗa jita-jitar cewa ta tara sojojin kasashen waje a kan iyakokinta don kai wa Nijar hari, abin dariya ne."

    "Idan Yamai ta amince a ba da hadin kai a gobe, jiragen ruwa za su iya jigilar man fetur daga Nijar."