Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir da Aisha Bappa

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotannin namu na wannan rana.

    Muna fatan sake haduwa da ku a gobe, Buhari Muhammad Fagge ke cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Yan ciranin Asiya na cikin rashin tabbas bayan harin da aka kai Moscow

    a

    Rahotanni na cewa ana ci gaba da duka da lalata kayan 'yanciranin ƙasashen tsakiyar Nahiyar Asiya a Rasha tun bayan harin da aka kai gidan raye-raye da ke Moscow a ranar Juma'ar da ta wuce.

    An zargi wasu 'yan kasar Tajikistan hudu da kashe mutum 139 a harin, wanda IS suka yi iƙirarin kai wa.

    An kama mutane da dama bisa zargin hannu a rikicin, dukkansu 'yan ƙasashen Nahiyar Asiya.

    A ƙarshen makon da ya gabata ne ofishin jakadancin Tajikistan a Rasha ya gargadin 'yan ƙasarsa da ka da wanda ya bar gidansa.

    Da yawa na fuskantar cin zarafi da kyama.

  3. Gwamnatin Kaduna za ta dasa bishiyoyi 20,000 a bana

    KSG

    Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce za ta dasa bishiyoyi 20,000 a 2024 a fadin jihar.

    Kwamishinan muhalli da albarkatun ƙasa na jihar Abubakar Buba ne ya bayyana hakan yayin wani taron kwana ɗaya kan manufofin sauyin yanayi a jihar, taren da haɗin gwiwar kungiyar Save the Children.

    Ya ce shirin wani yunkurin ne na rage tasirin sauyin yanayi da ake fama da shi a jihar da ma ƙasa baki daya.

    Da take nasa jawabin babbar sakatariyar ma'aikatar Linda Yakubu wadda ta wakilci kwamishinan ta ce matuƙar ana son ɗorewar jihar Kaduna do dole a yi wani abu game da lamarin sauyin yanayi.

    "Sauyin yanayi gaskiya ne kuma mun fara ganin tasirinsa a jiharmu. Za a gabatar da sabbin manufofi da za a rage tasirinsa a jihar."

  4. Mutum biyar sun mutu wa wani hatsarin mota a Jamus

    ..

    Akalla mutum biyar ne suka mutu wasu 20 suka jikkata a wani haɗarin mota da ya rutsa da su a kusa da birnin Leipzig da ke gabashin Jamus.

    Wata motar bas ta kamfanin Flix ne ta saki hanya ta afkawa wata bas ƙirar A9 suna cikin gudu.

    Kamfanin bas ɗin ya tabbatar da cewa motar ta bar Berlin ne ɗauke da direbobi biyu da fasinjoji 53 inda suka ɗauki hanyar zuwa Nuremberg daga Zurich.

    Jami'am jihar Saxony sun ce suna miƙa sakon ta'aziyyarsu iyalan wanda abin ya rutsa da su.

    Motocin kamfanin Flixbus da aka samar a Munich a 2011, suna aikin tafiye-tafiye ne masu dogon zango daga Turai zuwa Amurka zuwa Asiya.

  5. Tinubu ya bai wa iyalan sojojin da aka kashe gidaje da tallafin karatu

    A

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin kyautar gidaje da kuma tallafin karatu ga iyalan sojojin da aka kashe a jihar Delta a ranar 14 ga watan Maris.

    Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a yayin jana;izar sojojin, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta kyale iyalan waɗannan mutane su walaƙanta ba.

    "Mutane ne da suka sadaukar da rayuwarsu a wajen kare ƙasarsu, domin haka ba za mu bari su walaƙanta ba.

    "Gwamnati ta bai wa iyalansu gidajen zama da kuma tallafin karatu ga ya'yansu da suk mutu suka bari.

    "Za mu tabbatar sun amfana da duk wani tallafi da iyalan waɗanda suka rasa rayuwarsu suke samu a hukumance," in ji Tinubu.

    Tinubu ya umarci ma'aikatar fanso ta ƙasar da ta kammala biyan hakkin iyalan mamatan nan da kwana 90.

    An bai wa iyalan mamatan lambar girma da kuma shaida a yayin taron jana'izar tasu.

  6. Ana jana'izar sojojin Najeriya 17 da aka kashe a Delta

    A

    An fara jana'izar sojojin Najeriya 17 da aka kashe a jihar Delta a ranar 14 ga watan Maris 2024 a maƙabar sojoji ta ƙasa da ke Abuja.

    A ranar Laraba ne aka tsara binne mamatan, kuma an kai gawarsu makabartar da misalin ƙarfe biyu na ranar.

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da shugabannin Majalisun ƙasar biyu duka sun halarci jana'izar.

    'Yan uwa da iyalan mamatan duka sun halarci jana'izar domin shaida yadda za a binne 'yan uwansu.

    Lamarin mutuwar sojojin ya faru ne a lokacin da aka kira su, sukai ɗaiki kan wani rikicin ƙabilanci tsakanin Okuoma da Okoloba a jihar ta Delta.

    A
  7. Afirka ta Kudu za ta rufe manyan makarantun da ba sa aiki sosai

    ..

    An umarci a rufe makarantun masu zaman kansu guda huɗu da aka fasalta a matsayin "marasa aiki yadda ya kamata" a Afrika ta kudu inda aka bar dubban ɗalibai cikin jiran tsammani.

    A cewar ministan ilimin makarantun gaba da sakandare Blade Nzimande makarantun na ƙirƙirar sakamakon karatu na bogi da kuma sauran batutuwa.

    Hukumar ilimin ta ce makarantun sun gaza gabatar da bayanan harkokin kudinsu tun 2020.

    Makarantun sun kasance mallakar Educor wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu samar da ilimin makarantu masu zaman kansu a Afrika ta kudu.

    BBC ta tuntubi Educor kan tuhumce-tuhumcen da ake musu amma ba su ce komai ba har ya zuwa yanzu.

    Suna gudanar da makarantun da ke samar da ilimi sama da 60 a Afrika ta kudu da kuma waje.

  8. An yanke wa mutum hudu hukuncin kisa a Tunisia saboda kisan dan siyasa

    ..Mace dauke da dan siyasar da aka kashe

    Wata kotu a Tunisiya ta yanke wa wasu mutane huɗu hukuncin kisa sannan wasu biyu kuma ɗaurin rai da rai bayan kama su da laifin hannu a kisan sanannen jagoran siyasar kasar Chokri Belaid, a 2013.

    An dai samu Chokri Belaid, a motarsa bayan an harbe shi wanda hakan ya tayar da hankulan jama'a.

    Ɗan siyasar ya kasance mai sukar jam'iyyar Ennahda ta musulmai da ke mulkar ƙasar.

    Chokri Belaid,ya yi ikirarin cewa gwamati ta yi biris da batun cin zarafin da masu tsattsauran ra'ayin addini ke yi wa masu rajin raba gwamnati da addini.

    Duk da cewa ƙasar ta Tunisiya kan yanke hukuncin kisa kan laifuka masu girma, amma kuma ba a taɓa aiwatar da hukuncin ba tun shekarar 1990.

    Maimakon hakan a kan yankewa masu laifin daurin rai da rai.

    Ana dai tuhumar mutane 23 da ake zargi na da alaƙa da kisan Belaid.

    A cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP, an sanar da hukuncin ne kai tsaye a gidan talbijin na ƙasar.

    Masu ikirarin jihadi sun dauki alhakin kisan Belaid tare da Mohamed Brahmi, wanda shi ma ya kasance babban mai adawa da gwamnati.

    A yanzu Tunisiya na karkashin mulkin shugaba Kais Saied, wanda ake wa kallon mai tsattsauran ra'ayi bayan abubuwa da dama da ya aikata ciki har da ruguza hukumar dokoki ta ƙasar da korar firaiminista da kuma tsaida majalisar dokoki na wani lokaci.

  9. China na zawarcin kamfanonin kasashen waje

    Xi Jinping

    Shugaban kasar China Xi Jinping ya gana da Manyan 'yan kasuwa na Amurka a birnin Beijing, a wani mataki na zawarcin kamfanonin kasashen waje don bunkasa tattalin arzikin kasar. Mista Xi ya bukaci a kara karfafa dankon mu'amala da hadin gwiwa tsakanin Amurka da China.

    Rahotanni sun ce mayar da hankali kan harkokin tsaro da Beijing ta yi ya sa kamfanoni da yawa suna dar dar kar su wuce gona da iri.

    Amma a wani bidiyo da kafafen yada labaran kasar suka fitar, Mr Xi ya bukaci Amurka da China su nemi matsaya guda ko da kuwa suna samun sabanin ra'ayoyi.

    Mu’amala tsakanin kasashen biyu masu karfin fada-a-ji na ci gaba da farfadowa bayan da dangantaka ta yi tsami a cikin shekarun baya, sakamakon sabani da suke samu kan manufofin kasuwanci, da kuma makomar yankin Taiwan.

  10. Hezbollah ta kai hare-haren rokoki zuwa Isra'ila

    ..

    Kungiyar Hezbollah ta kai hare-haren rokoki zuwa arewacin Isra'ila, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya a wani martani kan hare-haren da Isra'ila ta kai kan wani kauyen kasar Lebanon.

    Bayanai na cewa mutum bakwai ne suka mutu a harin da Isra'ilar ta kai da daddare a Habbariyeh, hari mafi muni a baya-bayan nan.

    Isra'ila ta ce an kashe masu tayar da kayar baya da suka hada da wadanda suka kai wa Isra'ilar hari.

    To sai dai kungiyar ta 'yan kasar Lebanon da aka hara sun ce wadanda aka hara din masu aikin ceto ne.

    Hare-haren dai sun faru ne a daidai lokacin da Isra'ila da mayakan Hezbollah ke musayar yawu a kan iyakokinsu, al'amarin da ya fara tun bayan da Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan oktoban 2023.

  11. NAHCON ta rubuta wa Saudiyya wasika kan hana 'yan kasar biza

    Hukumar alhazai ta Najeriya NAHCON, ta ce ta rubutawa Saudiyya a hukumance, inda ta sanar da ita halin da ake ciki game da ƙarancin biza ga ‘yan ƙasar da suke son zuwa umrah.

    NAHCON ɗin ta ce ta yi wa hukumomin Saudiyyar bayanin illar rashin bai wa kamfanonin shirya tafiye-tafiyen bizar a yanayin da ake ciki.

    Cikin wata sanarwa da hukumar NAHCON ta fitar ta bayyana irin kalubalen da ‘yan Najeriya ke fama wajen samun bizar shiga saudiyya don gudanar da ibadar umrah a wanann wata na Ramadan a matsayin abin takaici.

    Dumbin maniyyata wadanda suka shirya tafiya umrah tuntuni tsakaninsu da kamfanonin shirya tafiye-tafiye, suna ci gaba da bayyana takaicinsu da rashin samun biza daga hukumomin Saudiyya.Adadin masu zuwa Umrah a lokacin watan Ramadan galibi ya kan fi na sauran lokuta saboda kwadayin dacewa da tarin ladan da ke tattare da yin ibadar a cikin watan na azumi, inda miliyoyin musulmi daga kasashe da dama na duniya ke zuwa yin umarah.

  12. Sojoji sun lalata haramtattun wuraren tace mai a jihar Ribas

    ..

    Sojojin saman Najeriya da ke aiki ƙarƙashin rundunar 'Operation Delta Safe' sun kai wani samame kan wuraren tace mai ba bisa ƙa'ida ba da jiragen ruwan dakon kaya maƙare da ɗanyen mai da aka sace a yankin Neja Delta.

    Wata sanarwar daraktan yaɗa labarai na rundunar sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, an gano cibiyoyin da jiragen ruwan dakon kayan tsakanin 25 da 26 ga watan Maris a wasu yankunan jihar Rivers.

    An gano wani jirgin dakon kaya a yankin Bille cike da albarkatun mai da aka tace ba bisa ƙa'ida ba. Kazalika, sojojin a yankin Dariama da Tumakiri, wuraren da suka yi suna kan tace mai ba bisa ƙa'ida ba, sojojin sun gano tukwanen girki abin da ke nuna akwai mutane a wajen. Sun kuma yi musayar wuta tsakaninsu inda kuma suka lalata wuraren da ake tace man ba bisa doka ba.

    A cewar sanarwar, sojoji sun ƙona wasu wuraren da aka gano ana tace ɗanyen mai ba bisa ƙa'ida ba inda kuma aka cinna masu wuta.

    A baya, sojoji sun lalata wuraren da aka gano a Bille da Dariama. Rundunar sojin saman da wasu hukumomin tsaro, a cewar sanarwar za su ci gaba da ƙara ƙaimi wajen gano ayyukan masu satar ɗanyen ma da ke gudanar da ayyukansu a yankin.

  13. Gwamnan Kano zai cika wa maniyyatan jihar naira dubu 500

    ..

    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da amincewa da tallafin naira dubu 500 ga maniyyata hajjin bana da suka fito daga jihar, a wani yunƙuri na rage masu raɗaɗin ƙarin kuɗin kujerar hajji da hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta yi.

    A baya-bayan nan ne hukumar alhazan ta najeriya ta sanar da ƙara kuɗin kujerar hajjin da kusan naira miliyan biyu sai dai ta bayyana cewa ƙarin bai shafi maniyyatan da ke ƙarƙashin tsarin adashin gata ba.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na X . A yanzu duk maniyyaci daga jihar Kano wanda ba ya tsarin adashin gata, zai yi ƙarin naira miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu a maimakon sama da naira miliyan ɗaya da dubu ɗari tara.

    Ya ce "duk maniyyacin da ya yi rajista kuma ya biya kafin alƙalamin naira miliyan 4.7 da naira miliyan 4.5 a hukumar alhazai ta jiha a yanzu zai biya naira miliyan 1.4 a maimakon naira miliyan 1.9."

    To sai dai sanarwar gwamnan ba ta fayyace ko tallafin zai kasance ga dukkannin maniyyatan jihar ba ne ko kuma wadanda ba za su iya yin cikon ba.

    View more on twitter
  14. NFIU ya gano maboyar 'yan IPOB a Burtaniya da Amurka

    ..

    Sashen da ke tattara bayanan sirri da suka jibanci hada-hadar kudade wato NFIU, ya ce ya gano wasu wurare 27 da 'yan kungiyar aware na Biafra, IPOB ke aiki a kasashe 22 a fadin duniya da suka hada da Amurka da Burtaniya da Northern Ireland.

    Sashen na NFIU kamar yadda jaridar Punch ya ce Amurka da Burtaniya ne suka kasance wurin da 'yan tayar da kayar bayar suka fi yin dandazo.

    Wadannan nan bayanan dai na dauke ne a cikin wata takarda da ke dauke da bayanan kungiyoyin barayin daji da 'yan kungiyar aware ta IPOB da sauran kungiyoyin ta'addanci. a cikin gida da wajen Najeriya da ke tattara kudade daga wurare da dama.

    A shekarar 2017 ne dai gwamnatin tarayya ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ta'addanci inda kuma a yanzu haka ake tsare tuhumar shi bisa laifukan ta'addanci.

  15. An gano rumbun bayanan jirgin da ya rusa gadar Baltimore

    ..

    Ƙwararrun masunta da ke gudanar da bincike sun gano rumbun bayanan jirgin nan da ya yi karo da babbar gadar Baltimore, kamar yadda masu bincike suka shaida wa kafar yaɗa labarai ta CBS.

    Hukumar kula da harkokin sufuri ta Amurka, ta tabbatar da gano rumbun bayanan daga jirgin na Dali.

  16. An ɗaure ɗan tsohon shugaban Guinea Bissau a Amurka saboda safarar ƙwaya

    ..
    Image caption: Mahaifin Bacai Sanha Jr ke nan da ya jagoranci Guinea Bissau daga 2009 zuwa 2012

    Wata kotu a Amurka ta yanke wa ɗan tsohon shugaban ƙasar Guinea Bissau shekara shida a gidan gyaran hali bayan kama shi da laifin jagorantar tawagar masu safarar ƙwayar "heroin".

    Mahukunta sun ce malam Bacai Sanha ƙarami mai shekara 52 ya shirya amfani da kuɗaɗen da ya samu daga harkar ƙwayar domin cimma ƙudirinsa na zama shugaban ƙasar ta hanyar yin juyin mulki.

    Ɗa ne ga malam Bacai Sanha wanda ya shugabanci ƙasar daga 2009 har zuwa lokacin mutuwarsa a 2012.

    Ana alaƙanta Sanha ƙarami da hannu a yunƙurin juyin mulkin Fabarairun 2022.

    An miƙashi shi ga mahukuntan Amurka a watan Agustan 2022 bayan kamashi a Tanzaniya a ƴan makonnin da suka gabata.

    Ba a ɗau lokaci ba da miƙashi aka fara sauraron shari'ar sannan a Satumbar shekarar da ta gabata ya amsa laifin hannu a shigar da ƙwayoyi ba bisa ƙa'ida ba.

    A cewar jami'in FBI Douglas Williams a ranar Talata, "Malam Bacai Samha ƙarami ba irin ƴan safarar miyagun ƙwayoyin da aka sani ba ne..."

    "Shi ɗa ne ga tsohon shugaban ƙasar Guinea Bissau kuma yana da takamaiman dalili na yin safarar ƙwayoyi domin ɗaukar nauyin juyin mulki da zai kai shi ga zama shugaban ƙasar tasa inda ya shirya kafa daular hada-hadar miyagun ƙwayoyi".

    Mahukuntan Amurka sun ce akwai yiwuwar mayar da shi gida bayan hakuncin zaman gidan yarin tun da shi ba ɗan asalin ƙasar ba ne.

    Sanha ƙarami wanda ake kira da "Bacaizinho" a Guinea Bissau ya riƙe muƙaman gwamnati da dama ciki har da muƙamin bai wa mahaifinsa shawara kan tattalin arziki.

    An ruwaito cewa da kansa ya amsa laifin hannu a yunƙurin juyin mulkin ɓarar da gwamnatin Umaro Sissoco Embalo a shekarar 2022.

  17. An umarci ma'aikatan gwamnati su rinƙa motsa jiki duk mako a Uganda

    Ana motsa jiki

    Gwamnatin Uganda ta umarci dukkan ma'aikatanta da su rinƙa ware sa'a biyu a duk mako suna motsa jiki domin su kasance cikin ƙoshin lafiya.

    Gwamnatin ta ce an bayar da umarnin ne domin ceton rayukan ma'aikatan da kuma rage musu kamuwa da wasu cutuka da suka jiɓanci rashin motsa jiki.

    Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, gwamnatin ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin a canja yanayin tsarin rayuwar ma'aikata da kuma rage haɗarin kamuwa da cutuka a ƙasar.

    Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne bayan wani bincike da hukumar lafiya ta ƙasar ta gudanar wanda ya nuna an samu ƙaruwar masu ƙiba sosai a ƙasar da ya kai daga kashi 17 cikin 100 zuwa 26 cikin 100.

    Ba wannan ne karon farko da gwamnatin ta Uganda ta fara bayar da irin wannan umarni ba,ko a 2018 ma an yi wasu abubuwa makamantan haka.

  18. Anjima a yau za a yi jana'izar sojin Najeriya 17 da aka kashe a Delta

    ..

    Rundunar sojin Najeriya ta sanar da yau 27 ga watan Maris a matsayin ranar da za a yi jana'izar sojoji 17 da aka kashe a garin Okuama da ke jihar Delta.

    Rundunar ta ce za a yi jana'izar ne a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ƙarfe 3 na yamma agogon Najeriya.

    Hakan yazo ne ƴan makonni bayan wasu ɓatagari sun kashe wasu daga cikin sojojin da ke aiki ƙarƙashin runduna ta 181 da aka turo domin kwantar da tarzomar da ke tsakanin al'ummar garin Okuama da Okoloba na jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.

    Shugaban ƙasa Bola Tinibu da ƴan Najeriya da dama sun yi allahwadai da kisan sojojin.

    Shugaban ƙasar ya umarci rundunar da ta tabbatar cewa waɗanda suka aikata kisan sun fuskanci hukunci.

    Su wane ne sojojin da aka kashe?

    ..

    A hoton da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X, sojojin da aka kashe sun haɗa da :

    • Lt Col AH Ali, kwamandan runduna ta 181
    • Manjo SD Shafa
    • Manjo DE Obi
    • Kyaftin U Zakari
    • Staff Sajant Yahaya Saidu
    • Koporal Yahaya Danbaba
    • Koporal Kabiru Bashir
    • Lance Koporal Bulus Haruna
    • Lance Koporal Sole Opeyemi
    • Lance Koporal Bello Anas
    • Lance Koporal Hamman Peter
    • Lance Koporal Ibrahim Abdullahi
    • Private Alhaji Isah
    • Private Clement Francis
    • Private Abubakar Ali
    • Private Ibrahim Adamu
    • Private Adamu Ibrahim