Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Aisha Bappa da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Bankwana

    Nan muka kawo ƙarshen labaran namu na yau sai kuma gobe.

  2. An ayyana ranakun Juma'a da Litinin a matsayin hutu a Najeriya

    ...

    Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Juma’a, 29 ga Maris da Litinin 1 ga Afrilun 2024 a matsayin hutu don bikin Easter.

    Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnati, ya buƙaci mabiya addinin kirista da ma daukacin al’ummar Najeriya baki daya da su yi koyi da sadaukarwa da kauna da Yesu Kiristi ya nuna wajen mutuwa.

    A cewar Ministan, bikin Easter yana inganta dabi'un soyayya da gafara da jin ƙai wadanda suke da muhimmanci ga hadin kai da zamantakewa.

    Ya yi kira ga Kiristoci da su yi koyi da wadannan kyawawan halaye domin suna iya yin tasiri mai kyau ga ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a Najeriya ta hanyar samar da hadin kai da rage rikice-rikice da karfafa hadin gwiwa tsakanin 'yan Najeriya.

    Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su nuna ayyukan jin kai da karamci don taimakawa wajen rage wa marasa galihu daga cikin su matsin rayuwa.

    Yayin da yake yiwa kiristoci na gida da waje barka da bukukuwan Easter, ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai da gwamnatin shugaba Tinubu a kokarinta na kawo cigaba mai dorewa a ƙasar.

  3. Mozambik ta amince da yarjejeniyar mayar da masu laifi da Rwanda

    Majalisar dokokin Mozambique ta amince da yarjejeniyar mayar da masu laifi da Rwanda duk da fargabar da ake da ita kan masu sukar shugaban Rwanda Paul Kagame.

    'Yan majalisar 'yan adawar Mozambique dai sun kada kuri'ar ƙin amincewa da yarjejeniyar suna masu cewa za ta iya ba da damar cin zarafin siyasa.

    Ƙungiyar lauyoyin Mozambique ta bayyana damuwa game da matakin.

    Ana zargin hukumomin Rwanda da kai wa masu suka hari a ƙasashe da dama na Afirka ciki har da Mozambique amma Rwanda ta musanta hakan.

    Ƙasashen biyu dai na da alaka ta kut-da-kut, inda aka girke sojojin Rwanda a arewacin Mozambik domin su taimaka wajen yaƙar masu iƙirarin jihadi.

    'Yan Rwanda da dama da suka tsere daga kisan ƙare dangi na 1994 suna zaman ƴan gudun hijira a Mozambique.

  4. Gwamnatin Kaduna ta miƙa ɗaliban Kuriga hannun iyayensu

    K

    Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce da miƙa ɗaliban makarantar Kuriga da aka sace ga iyayensu.

    Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun gwamnan jihar Sanata Uba Sani ya ce sai da aka tabbatar da lafiyar kwakwalwar yaran da kuma lafiyar jikinsu gabanin a miƙa su ga iyayensu sannan su koma makaranta.

    Gwamna Uba Sani ya ce yaran da suka saba da shi suke ɗaukarsa tamkar mahaifi a gare su, sun yi alƙawarin amfani da wannan jarrabawa da suka fuskanta wajen mayar da hanakali da jajurcewa kan karatunsu da sun koma makaranta.

    "Gidauniyar Uba Sani za ta ci gaba da kula da karatunsu daga nan har matakin gaba da sakandire," in ji sanarwar.

    A

    Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin Jihar Kaduna za ta biya iyalan malamin makarantar Malam Abubakar diyyar naira miliyan 10 wanda ya mutu a lokacin da ake tsare da su sakamakon rashin lafiya.

    Gwamnan ya kuma yi alƙawarin sake gida makarantar Kuriga daga bangaren firaimare har sakandire tare da zagayeta da katanga, da kuma samar mata da cikakken tsaro domin yaran su koma su ci gaba da karatu.

    A

    A ranar shida ga watan Maris ne aka fara satar farko a watan nan, kuma an yi ne a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    Wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram sun sace a kalla ƴangudun hijira 200, yawancinsu mata da ƙananan yara a lokacin da suka shiga daji yin ice.

    Duk da ƙaddamar da nemansu da sojoji suka yi, amma hakan ta gagara, babu wanda aka yi nasarar kuɓutarwa.

    Washegari watau ranar bakwai ga watan dai na Maris, ƴanbindiga suka tasa ƙeyar ɗalibai kusan 300 daga makarantar firamare da sakandare a jihar Kaduna.

    A

    Daga bisani gwamnatin jihar ta sanar cewa ɗalibai 28 daga cikin waɗanda 'yan bindigar suka sace sun tsere daga hannunsu.

    A ranar tara ga watan Maris, ƴanbindiga sun sace ɗalibai ƴan makarantar allo 17 a wata makaranta da ke jihar Sakkwato a arewa maso yammacin Najeriya.

    Amma an sako su a ranar 22 ga watan Maris.

    A
  5. An sami katsewar wutar lantarki a sassan Ethiopia

    Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Habasha ya ce yawancin sassan kasar sun fuskanci katsewar wutar lantarki saboda matsalolin da ke cikin tsarinsu.

    Ita dai kamfanin samar da wutar lantarkin ba ta bayyana hakikanin abin da wadannan matsalolin suke ba, amma a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce tana gudanar da bincike kan abin da ya jawo katsewar.

    Dukkanin sassan kasar, in ban da birnin Bahir Dar da ke arewa maso yammacin kasar, da kewaye, sun fuskanci matsalar wutar lantarki da ta fara da misalin karfe 3:40 na agogon kasar.

    A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce ya fara maido da wutar lantarki a babban birnin kasar, Addis Ababa, da kuma wasu sassan kasar sa'o'i bayan da matsalar ta afku.

  6. An hana tsohon shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma shiga zaɓe

    ...

    Hukumar zaɓen ƙasar Afirka ta Kudu ta ce an hana tsohon shugaban kasar Jacob Zuma tsayawa takara a babban zaɓen kasar da za a yi a watan Mayu.

    Ana dai kallon goyon bayan da Zuma ke nuna wa sabuwar jam'iyyar uMkhonto weSizwe (MK) a matsayin wata barazana ga jam'iyyar ANC mai mulkin ƙasar.

    Jam'iyyar ANC dai ta dakatar da tsohon shugaban wanda ya yi mulki daga shekarar 2009 zuwa 2018.

    Sunansa ne na farko a jerin ‘yan takarar jam'iyyar MK, amma hukumar IEC ta samu rashin amincewarsa da yiwuwar zama dan majalisar tarayya.

    Zuma dai ya samu hukuncin daurin watanni 15 a shekara ta 2021 bisa laifin wulakanta kotu kuma kundin tsarin mulkin kasar ya ce duk wanda aka yanke masa hukuncin daurin fiye da watanni 12 ba zai cancanci tsayawa takara ba.

    A karon farko tun bayan fara mulkin dimokuradiyya a shekarar 1994, yawan kuri'un jam'iyyar ANC na iya faduwa ƙasa da kashi 50 cikin dari, kamar yadda kuri'un jin ra'ayoyin jama'a da dama suka nuna.

    Ana ganin jam'iyyar MK tana da farin jini a yankin KwaZulu-Natal inda aka haifi Zuma.

  7. Google ya dakatar da asusu kimanin miliyan 13

    A

    Kamfanin Google ya ce ya toshe tallace-tallace sama da biliyan biyar tare da dakatar da wasu asusu kimanin miliyan 13 saboda saɓawa dokarsa da manufofinsa.

    Katafaren kamfanin ya kuma bayyana a wata sanarwa a ranar Laraba cewa, ya cire tallace-tallace daga shafukan sama da biliyan biyu da miliyan 100.

    “Biliyoyin mutane a duk duniya suna dogara da kamfanin Google don samar da bayanai masu dacewa da aminci, gami da tallace-tallace."

    "Shi ya sa muke da dubban mutane da ke aiki ba dare ba rana don kiyaye yanayin talla a intanet."

    "A yau, mun fitar da rahoton tsaro na talla na shekara-shekara don sanar da ci gaban da muka samu wajen aiwatar da manufofin masu tallace-tallace da masu wallafawa da kuma ɗaukar alhakin aikinmu na kiyaye bayanan masu amfani da intanet, ”in ji kamfanin.

    A cikin shekarar 2023, Google ya ce aikin damfara da zamba ya ƙaru.

  8. An yanke wa Sam Bankman-Fried Sarkin 'yan crypto hukuncin shekaru 25 a gidan yari

    A

    Wata kotu ta yanke wa Sam Bankman-Fried Sarkin 'yan crypto zaman gidan yari na shekaru 25.

    Bankman-Fried fitaccen ɗan kasuwa ne da babu irinsu da yawa - ya yi shahara mai ƙarfi a kafafen sada sumunta, abin da ya sa ƙanana da matsagaitan masu hada-hadar crypto ke bin shafinsa.

    Manyan masu zuba jari sun amince da shi, saboda yadda kasuwanci ke haskakawa kuma ya samu karbuwa a duniya, dalilin da ya sanya suka sanya miliyoyin suƙinsu kenan a kamfaninsa.

    Yana yawan nuna kansa a matsayin kwararre kuma ɗan baiwa a lissafi wanda bai damu da tara duniya ba.

    Biloniyan ya taɓa tuka wata motar iyalai da ta rakwakkwaɓe kuma ya sha kwana kan buhun waje a ofishinsa. Yana da burin taimakawa ƙungiyoyin baimakawa al'umma.

    Kamfaninsa na musayar kuɗi na crypto ya bunƙasa ya sama na biyu mafi girma a duniya inda suke hada-hadar dalar Amurka biliyan 10 zuwa 15 a rana.

    Kamfanin Samuel Hapak ya wakilci masu zuba jari 200 a zaan kotun waɗanda suka yi asarar kuɗi da suka kai dala miliyan 35 lokacin da kamfanin FTX ya bayyana yana daf da durkushewa.

    Shugaban kamfanin samar da manhajar kwamfuyuta na Wincent ya shaida wa BBC cewa ɗaurin da aka yi wa Sam na shekara 25 ya yi daidai.

    Kamfanin Wincent ya yi asarar rabin jarinsa kimanin dala miliyan 70 - kashi 25 na hannun jarinsa, Hapak ya shaida wa BBC.

  9. An kama gandaye 12 da ke cin abinci a bainar jama'a yayin azumi a Zanzibar

    Jami’an ‘yan sanda a tsibirin Unguja da ke tsibirin Zanzibar sun kama wasu gandaye 12 da ake zargi da cin abincin rana a bainar jama’a a yayin azumin watan Ramadan.

    A cewar mukaddashin kwamandan ‘yan sandan yankin Yamma, Abubakr Ally, matakin ya biyo bayan wani faifan bidiyo ya nuna yadda wasu ke cin abinci a bainar jama’a da rana.

    Kwamandan ya ce bayan binciken sun yi nasarar kama gandayen ne daga sassa daban-daban na birnin.

    Jami’in ya ƙara da cewa ‘yan sandan na ci gaba da kammala bincike domin a gurfanar da wadanda ake zargi da ƙin yin azumi da gangan a gaban kotu.

    Yanzu haka dai mutanen suna tsare a ofishin 'yan sanda na Madema

  10. 'Yan majalisar dokokin Jihar Enugu sun sauya sheka daga LP zuwa PDP

    A

    'Yan majalisar dokokin jihar Enugu shida sun sauya sheƙa daga jam'iyyar LP zuwa PDP, shekara guda bayan zaɓe.

    Kakakin majalisar jihar Chief Uche Ugwu ne ya sanar da ficewar tasu a wata wasika da ya karanta yayin wani zama da aka yi a ranar Alhamis

    Waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da shugaban masu rinjaye Mr Johnson Ani daga Enugu ta arewa, da mai tsawatarwar majalisar Mr Ejike Eze da ke wakiltar Igbo-Eze, sai mataimakiyar mai tsawatarwar Ms Princess Ugwu daga Enugu ta Kudu.

    Sauran sun haɗa da Mr Pius Ezugwu da da Mista Williams Amuka da kuma Mista Osita Eze.

    Wasikar ta ce mutanen sun sauya sheƙar ne dalilin rikice-rikice da rabuwar kai da suka ƙi-ci suka ƙi-cinyewa a matakin jam'iyyar na ƙasa da sauran rassanta na jihohi.

    Sun ce wannan rikici da har ya kai wasu ga ɗaukar mataki na shari'a babu abin da za su haifar sai koma baya ga jam'iyyar. Waɗanda aka zaɓa kuma ba za su iya yin abin da mutane suka zaɓe su domin shi ba.

  11. An tsawaita dokar taɓaci kan masu iƙirarin jihadi a Burkina Faso

    a

    Shugabannin sojin da ke mulki a Burkina Faso sun tsawaita matakan da suka ɗauka na sanya dokar ta ɓaci da shekara guda, a yaƙin da suke yi na ganin sun murƙushe masu iƙirarin jihadi a ƙasar.

    Dokar sojin ta ce duk wanda ya haura shekara 18 kuma ba shi da wata tawaye a halittarsa zai iya shiga aikin soji.

    Ta kuma ce duk da sanin 'yanci da hakkin 'yan ƙasa amma za a iya sanya su cikin aikin domin tabbatar da tsaron ƙasa.

    Masu aiko da rahotanni sun ce an rika samun bayanan yadda ake tilasatawa masu adawa da gwamnatin sojin Burkina Faso shiga aikin soji don yaƙi da masu iƙirarin jihadi. Wasu kuma aka riƙa sace su.

    Mutum sama da miliyan biyu ne suka tsere daga muhallansu sakamakon rikicin masu iƙirarin jihari a ƙasar, tun shekarar 2015.

  12. NNPC ya ƙaryata raɗe-raɗin rage farashin mai

    ..

    Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa na rage farashin mai daga naira 568 zuwa 560 duk lita ɗaya.

    NNPCL ya ƙaryata rahotannin cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun kakakin sa Femi Soneye.

    Sanarwar ta bayyana cewa NNPCL a shirye yake ya ci gaba da samar da albarkatun man da zai wadata ƙasar a dukkan gidajen mansa da ke faɗin ƙasar.

    A ranar 9 ga watan Fabarairu ne NNPCL ya ce ba za a ƙara kuɗin mai ba a ƙasar.

  13. 'Yan sandan Kano sun kama ƴan daba 22 da suka addabi Ɗorayi

    ..

    Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta tabbatar da kama mutum 22 da ake zargi riƙaƙƙun ƴan daba ne a unguwar Ɗorayi da ke jihar.

    Matakin ya zo ne sakamakon ɓarkewar faɗa tsakanin ƴan daba a unguwar ranar Laraba.Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta ya nuna yadda aka ji wa wasu matasa raunuka a arangamar da aka yi.

    Cikin wani bidiyo da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ƴan sanda sun bayyana sunan wasu mutum 30 da ake zargi ƴan daba ne da suka addabi Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale.

    A cewar kakakin rundunar, kwamishinan ƴan sanda na jihar Muhammad Usaini Gumel zai buɗe sabon ofishin yaƙi da ayyukan daba a unguwar ta Ɗorayi.

    Rundunar ta ƙaddamar da shirin tuba da gyara halin wasu 'yan daba a Kano, har ma ta ɗauki wasu kusan 50 aiki bayan sun tuba.

    Kazalika, rundunar ta sha shirya wasanni tsakanin tubabbun 'yan dabar da kuma ma'aikatanta a matsayin wani sabon salon yaƙi da halayayyar ta daba.

    Video content

    Video caption: Tubabbun 'yan daban da suka koma 'yan sandan sa-kai

    Kiyawa ya wallafa a shafinsa cewa "wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sada zumunta kan wannan lamari, ba su san shi ba, kuma bidiyon ba a Kano ya faru ba."

  14. Kamfanin Xiaomi na China zai ya fara kera mota mai amfani da lantarki

    Mota

    Wani katafaren kamfanin fasaha a China,da aka fi sani da kera wayoyin salula, ya fara karbar odar motarsa ​​ta farko mai amfani da wutar lantarki.

    Xiaomi na fatan fasahar da ke bada damar hada motar da wayoyin salula za ta jawo hankalin abokan ciniki.

    Rahotanni sun ce motar kamfanin mai amfani da lantarki ta farko mai suna Speed ultra seven, za ta kai farashin dala dubu saba’in kuma ana kwatantata da motoci kirar kamfanin porsche irinsu Taycan da Panamera.

    Kamfanoni masu kera motocin da ke aiki da lantarki na ta kara yawa a China, kuma hukumomi a Amurka da Turai sun zargi gwamnatin China da rashin adalci wajen bai wa masana’antar tallafi don taimaka mata wajen samun kaso mai tsoka a kasuwar.

  15. Mutum huɗu sun mutu sakamakon harin wuƙa a Amurka

    ..

    An kashe mutum huɗu yayin da biyar suka jikkata bayan wani mutum ya kai wa mutane hari da wuƙa a jihar Illinois da ke Amurka.

    Ƴan sandan Rockford sun ce hare-haren sun faru ne bayan sumame da aka kai wani gida da tsakar ranar Laraba. Ɗaya daga cikin waɗanda aka raunata na cikin mawuyacin hali.

    Waɗanda harin ya ritsa da su sun haɗa da yarinya ƴar shekara 15, da wata mata ƴar shekara 63 da maza biyu - ɗan shekaru 49 da 22.

    Ƴan sanda sun kama wani mutum mai shekara 22 sannan suna masa tambayoyi.

    Ƴan sandan sun ce har yanzu ba a gano dalilin kai harin ba.

    An kai sumamen ne a gidan da ke kan layin Florence sai dai hare-haren sun faru a wurare daban-daban a cewar ƴan sandan.

    Babban jami'in ɗan sandan a yankin Winnebago, Gary Caruana ya ce wata matashiya ta samu raunuka a hannayenta da fuskarta bayan an ganta tana guduwa daga maharin.

    Matashiyar tana asibiti a yanzu tana jinya.

    Ya ƙara da cewa wani matashi ya samu raunuka a ƙoƙarin taimaka wa matar lokacin da ake sararta.

    Shugabar ƴan sanda na Rockford, Carla Redd ta ce ba duka waɗanda harin ya ritsa da su ne suka samu raunuka ba haka kuma babu wanda ya ji rauni daga harbin bindiga.

    Ta kuma ce ƴan sanda ba su yarda akwai wasu waɗanda ake zargi da suka tsere ba.

  16. Masu shigar da ƙara na son a ɗaure Rubiales saboda sumbatar ƴar wasan Sifaniya

    ..

    Masu gabatar da ƙara a Sifaniya na neman a aika tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar gidan yari domin ya yi zaman shekara biyu da rabi bayan sumbatar wata ƴar ƙwallo ba tare da izininta ba a bikin da aka yi bayan Sifaniya ta lashe Kofin Duniya.

    Luis Rubiales na fuskantar tuhume-tuhumen cin zarafi mai nasaba da lalata da kuma tilasta mata bayan da ya cafko Jenni Hermoso, inda ya sumbace ta a baki cikin Agustan bara.

    Ms Hermoso da sauran ƴan ƙungiyar sun ce ƙasƙantarwa ne kuma bai kamata tsohon shugaban hukumar ya yi abin da ya yi ba.

    An tilasta wa Mista Rubiales ya ajiye aiki, sai dai ya musanta aikata ba daidai ba.

    A cewar wata takardar kotu da Reuters ta gani, mai gabatar da ƙara Marta Durantez ta tuhumi Mista Rubiales da laifin cin zarafi mai alaƙa da lalata da kuma ɗaya tuhumar ta tilasta mata saboda abin da ya yi bayan sumbatar ta.

    Tuhume-tuhumen na ɗauke da hukuncin shekara ɗaya da wata 18.

    Ms Durantez ta zargi tsohon kocin na ƙungiyar ƙwallon ƙafar mata ta ƙasar, Jorge Vilda da daraktan wasanni na ƙungiyar Albert Luque da shugaban harkokin kasuwanci na hukumar, Ruben Rivera da tilasta wa Ms Hermoso ta bayyana cewa da izininta aka sumbace ta.

    Dukkansu uku sun musanta yin ba daidai ba lokacin da suka bayyana gaban kotu. Suna kuma iya fuskantar wata 18 a gidan yari idan aka same shi da laifi.

  17. Majalisar dokokin Faransa ta yi allah-wadai da kisan kiyashin ƴan Aljeriya a 1961

    ..

    Majalisar dokokin Faransa ta amince da ƙudirin yin allah-wadai da kisan kiyashin da aka yi wa ƴan Aljeriya shekaru fiye da sittin da suka gabata.

    Masana tarihi sun ce kusan masu zanga-zanga 300 ne aka kashe lokacin da ƴan sanda suka tarwatsa masu gangamin nuna goyon baya ga samun ƴancin kan Aljeriya.

    An yi wa wasu dukan kawo wuƙa da ya janyo mutuwarsu yayin da sauran kuma suka nutse a kogin Seine.

    Ƙudirin ya nemi a tsayar da ranar tunawa da kisan kiyashin na 1961.

    Daga bisani an samu babbar jami'ar ƴan sanda, Maurice Papon da laifin cin zarafin bil adama saboda haɗa kai da ƴan Nazi.