Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Mukhtari Adamu Bawa da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    Ma'abota BBC Hausa nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Umar Mikail ne ke fatan kun sha ruwa lafiya tare da fatan za ku yi sahur lafiya.

    Mu kwana lafiya.

  2. Ƙasashen da suka gabatar da kuma amincewa da ƙudirin tsagaita wuta a Gaza

    Gaza
    Image caption: Jakadan Falasɗinawa a Majalisar Ɗinkin Duniya Riyad Mansour kenan lokacin da yake jawabi yayin kaɗa ƙuri'ar

    Ƙasashe 10 ne suka gabatar da ƙudiri a zauren Kwamatin Tsaro na MDD don neman tsagaita wuta nan take a yaƙin da Isra'ila ke yi da Hamas a Zirin Gaza.

    Ƙasashen su ne:

    • Algeria
    • Sierra Leone
    • Mozambique
    • Republic of Korea
    • Japan
    • Slovenia
    • Guyana
    • Ecuador
    • Malta
    • Switzerland

    Bayan kaɗa ƙuri'a, ƙasashe 14 cikin 15 ne na kwamatin suka amince da ƙudirin, yayin da Amurka ta ƙaurace.

    Akwai ƙasashe biyar da ke da kujerar dindindin wadda ke ba su damar hana kowane irin ƙudiri wucewa a kwamatin. Su ne Rasha, da China, da Amurka, da Birtaniya, da Faransa. Sai kuma ƙasashe 10 marasa kujerar dindindin da ake zaɓa duk shekara biyu a babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

  3. Matakin da muka ɗauka kan tsagaita wuta ba sauya shawara ba ce - Amurka

    John Kirby

    Mai magana da yawun fadar tsaro ta Amurka John Kirby ya ce matakin da ƙasar ta ɗauka na ƙaurace wa ƙudirin neman tsagaita wuta a Gaza "ba ya nufin ta sauya manufa kan yaƙin" da Isra'ila ke yi a zirin na Falasɗinawa.

    Da yake magana da manema labarai a Fadar White House, ya ce sun daɗe suna neman a sako mutanen da Hamas ke garkuwa da su da kuma taimaka wa Isra'ila.

    "Mun daɗe muna bayyanawa ƙarara irin yadda muke neman a tsagaita wuta don samun nasarar ceto mutanen da ake garkuwa da su. A haka ake ƙulla yarjejeniyar sakin fursunoni, kuma ƙudirin ya bayyana hakan a kiran da ya yi," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa sun ƙaurace wa ƙuri'ar ce saboda babu inda ƙudirin ya yi tir da Hamas a kalamansa, amma ya ce "hakan ba zai hana mu fahimtar cewa tsagaita wuta da kuma tattaunawar sakin mutanen za su iya tafiya tare ba".

    Ya ce ganawar da aka tsara tsakanin ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant da kuma mai ba da shawara kan tsaro na Amurka Jake Sullivan za ta gudana kamar yadda aka shirya.

    "Za mu tabbatar wa da ministan tsaro cewa Amurka na ci gaba da mara wa Isra'ila baya a wannan yaƙi da suke yi da Hamas."

  4. Ɗaliban Kuriga: Yara 137 suna lafiya amma malamainsu ya rasu – Uba Sani

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku kalli bidiyo

    Gwamnan Kaduna Uba Sani ya tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin mutum 138 da 'yan bindiga suka sace a makarantar firamare ta Kuriga da ke jihar.

    Yayin da yake ganawa da ɗaliban 137 ranar Litinin, gwamnan ya ce malamin makarantar da aka sace tare da ɗaliban ya rasu, abin da ya sa suka zama 137.

    Sai dai bai yi ƙarin bayani ba game da rasuwar tasa.

  5. Shugaban Senegal ya taya ɗantakarar adawa murnar lashe zaɓe

    Shugaban ƙasar Senegal mai barin gado Macky Sall
    Image caption: Shugaban ƙasar Senegal mai barin gado Macky Sall

    Shugaban ƙasar Senegal mai barin gado, Macky Sall ya taya ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye murnar nasarar da ya samu a zaɓen shugaban ƙasar.

    Hakan na zuwa ne duk da cewa ana ci gaba da jiran hukumar zaɓe ta ƙasar ta sanar da ɗantakarar da ya yi nasara.

    A cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Macky Sall ya ce: "Na jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa na ranar 24 ga watan Maris ba tare da wata tangarɗa ba kuma ina taya wanda ya samu nasara, Mista Bassirou Diomaye Faye murna, wanda bayanan da ke fitowa su ka nuna cewa shi ne ya yi nasara."

    Macky Sall ya kammala saƙon nasa da cewa: "Wannan nasara ce ga mulkin demokuraɗiyyar Senegal."

    Dama dai tuni ɗan takara na jam'iyya mai mulki Amadou Ba ya miƙa saƙon taya murnarsa ga Mista Bassirou, wanda alƙaluman da jam'iyyu suka tattara ke nuna cewa ya samu nasara kai-tsaye a zaɓen na ranar Lahadi.

    Haka nan ma sauran ƴan takarar shugaban ƙasa duk sun isar da saƙonsu na taya murna ga Mista Bassirou Faye.

    Duk da haka har yanzu ba a bayyana Bassirou a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar ba a hukumance.

    Ana sa ran hukumar zaɓe ta ƙasar ta kammala tattara alƙaluma kafin sanar da ɗan takarar da ya yi nasara cikin kwana uku.

    Faye shi ne ɗan takarar da madugun ƴan adawa Ousman Sonko ke mara wa baya.

    A ranar 14 ga wannan wata na Mayu ne aka saki Bassirou Faye da Ousman Sonko daga gidan yari bayan afuwar da shugaban ƙasar ya yi musu.

    View more on twitter
  6. Labarai da dumi-dumiIsra'ila ta soke ziyarar da jami'anta za su kai Amurka

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya soke ziyarar da wakilan ƙasar suka tsara kaiwa Fadar White House ta Amurka a makon nan.

    Cikin wata sanarwa da kafar yaɗa labaran ƙasar ta Kann ta wallafa, ofishin Netanyahu ya ce an ɗauki matakin ne "saboda sauya alƙibla da Amurka ta yi" bayan ta ƙi daƙile ƙudirin Kwamatin Tsaro na MDD da ya yi kira a tsagaita wuta a Gaza nan take.

    A baya Netanyahu ya yi barazanar soke ziyarar - wadda za a yi kafin hari ta ƙasa da ake sa ran Isra'ila za ta kai a yankin Rafah na Zirin Gaza - wadda kuma gwamnatin Joe Biden ta nuna adawa da shi.

  7. Dole ne a aiwatar da umarnin tsagaita wuta a Gaza - Antonio Guterres

    Antonio Guterres

    Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a aiwatar da ƙudirin neman tsagaita wuta a Zirin Gaza nan take da Kwamatin Tsaro ya yi a yau Litinin.

    "Dole ne a aiwatar da wannan matsaya," in ji Mista Guterres a shafinsa na X. Ya ƙara da cewa "idan ba a yi hakan ba ba za mu yafe ba".

    A yau ne ƙasashe 14 cikin 15 mambobin kwamatin tsaron suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da ƙudirin, yayin da Amurka ta ƙi yin amfani da damarta ta hawa kujerar na-ƙi bayan ta ƙaurace wa ƙuri'ar.

    Sai dai a baya ta sha sha ƙin amincewa da kiran tsagaita wuta tana mai cewa yin hakan zai kawo wa tattaunawar da ake yi cikas game da sakin mutanen da ake garkuwa da su.

    View more on twitter
  8. Labarai da dumi-dumiKwamatin Tsaro na MDD ya yi kira a tsagaita wuta a Gaza

    Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD)

    Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya amince da ƙudiriin neman tsagaita wuta a Zirin Gaza "nan take".

    An samu nasarar amincewa da ƙudirin ne bayan Amurka ta ƙaurace wa kaɗa ƙuri'a a zaman kwamatin na yau Litinin, saɓanin yadda ta saba yi a baya.

    Kazalika, daftarin ya buƙaci a saki dukkan 'yan Isra'ila da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.

    Kwamatin ya sha fama da rikita-rikita bayan ɓarkewar yaƙin tun daga watan Oktoba, inda ya kasa yin kiran a tsagaita wuta.

    Matakin ya nuna irin lalacewar alaƙa tsakanin Isra'ila da babbar ƙawarta Amurka game da yaƙin da take yi a Gaza.

    A baya dai Amurka ta sha ƙin amincewa da kiran tsagaita wuta tana mai cewa yin hakan zai kawo wa tattaunawar da ake yi cikas game da sakin mutanen da ake garkuwa da su.

    Amurka ta soki Isra'ila game da ƙaruwar Falasɗinawan da take kashewa a Gaza, inda mutum fiye da 32,000 suka mutu - akasarinsu mata da ƙananan yara - saboda hare-haren Isra'ila, a cerwar ma'aikatar lafiya ta Gaza.

  9. Ɗantakarar shugaban Senegal na jam'iyya mai mulki ya taya na adawa murna

    Bassirou Diomaye Faye
    Image caption: Bassirou Diomaye Faye

    Yayin da al'ummar ƙasar Senegal ke jiran hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar Lahadi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki Amadou Ba ya taya ɗan takara na haɗakar ƴan adawa Bassirou Diomaye Faye murnar samun nasara.

    Alƙaluman da jam'iyyun siyasar ƙasar ke tattarawa bayan rufe rumfunan zaɓe a jiya Lahadi sun nuna cewa Bassirou Faye na jam'iyyar adawa shi ne ke kan gaba a yawan ƙuri'un da za su iya ba shi nasara kai-tsaye.

    Har yanzu dai babu wani sakamako da ya fito daga hukumar zaɓen ƙasar, wadda ke ci gaba da tattara sakamakon, kuma ba za ta bayyana ƙuri'un da kowane ɗantakara ya samu ba sai ta kammala haɗa alƙaluma.

    Taya Faye murna da Amadou ya yi ya zo wa al'umma da mamaki, ganin irin hamayya mai ƙarfi da ke tsakanin ɓangarorin biyu.

    A cikin sanarwar da ya fitar, Amadou Ba ya ce: "Ganin irin bayanan da ke fitowa game da zaɓen shugaban ƙasa, yayin da muke ci gaba da jiran sakamako a hukumance, ina taya shugaba Bassirou Diomaye Faye murna kan nasarar da ya samu tun a zagayen farko,

    "Ina roƙon Allah ya ba shi ƙarfin ikon tafiyar da harkokin wannan ƙasa tamu. Ina roƙar masa nasara da kuma nasarar dukkanin al'ummar Senegal."

    Bassirou Diomaye dai shi ne ɗantakarar da madugun adawa Ousmane Sonko ya mara wa baya, bayan haramta masa tsayawa takara.

    Dama dai tuni ƴan takarar shugaban ƙasar 17 suka taya Bassirou Faye murna, bayan da sakamako ya fara fitowa daga sassan ƙasar.

    A lokacin yaƙin neman zaɓe Faye ya bayyana kansa a matsayin wanda zai kawo sauyi a ƙasar ta yammacin Afirka mai yawan mutane miliyan 18.

    Cikin alƙawurran da ya yi har da rage biyayyar da Senegal ɗin ke yi wa uwargijiyarta Faransa da kuma daina amfani da takardar kuɗi ta CFA.

  10. Najeriya ta shiga neman jami'in Binance da ya tsere

    Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa ya tabbatar da cewa jami'in Binance, kasuwar hada-hadar kudin kirifto ta intanet da ake tsare da shi a Najeriya, Nadeem Anjarwalla ya kuɓuce daga hannun hukuma a ranar Juma'a.

    Wata sanarwa da jami'in harkar yaɗa labarai a ofishin, Zakari U. Mijinyawa ya fitar ta ce bayan samun wannan rahoto, hukumomi sun ɗauki matakai cikin gaggawa don ganin sun sake kama mutumin da ake zargi.

    Ya ce binciken farko-farko ya nuna cewa Nadeem Anjarwalla ya tsere daga Najeriya ne ta hanyar amfani da wani fasfo da aka yi fasa-ƙwaurinsa.

    Haka kuma an kama jami'an da ke da alhakin tsare wanda ake zargi, kuma yanzu haka ana gudanar da cikakken bincike don tantance abin da takamaimai ya faru.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, Najeriya kamar sauran gwamnatocin ƙasashe a faɗin duniya na gudanar da bincike a kan harkokin samar da kuɗi don ayyukan ta'addanci da halasta kuɗin haram waɗanda ake zargin kamfanin hada-hadar kuɗi na Binance na aikatawa.

  11. Kotu ta sanya wa Murja Kunya takunkumin amfani da soshiyal midiya

    ...

    Wata babbar kotu da ke Kano ta ba da belin fitacciyar jarumar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya a kan kuɗi naira dubu 500 da kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya mata.

    Baba Jibo Ibrahim, mai magana da yawun kotunan Kano ya tabbatar wa BBC wannan labarin, inda ya ce kotun ta ba da belin Murja ne bayan zaman kotun da aka yi a yau Litinin.

    Alƙalin ya ce dole ne ɗaya daga cikin masu tsaya mata ya zama ɗan'uwanta na jini, sannan ɗayan kuma dole ne ya zama yana da shaidar mallakar fili a Kano.

    Alƙali Nasiru Saminu ya kuma ce ya bayar da belinta ne bisa hujjar cewa matashiyar 'yar Tiktok din ta wuce kwana 30 a garƙame.

    Sai dai alƙalin ya haramta wa jarumar tiktok ɗin amfani da shafukan sada zumunta har zuwa lokacin kammala shari'ar.

    Alƙalin ya kuma ce kwamishinan ƴansanda na da ikon sake kama Murja matuƙar ta ƙi mutunta umarnin haramta mata amfani da shafukan sada zumuntar tare da gabatar da ita gaban kotu.

    Mai shari'ar ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 16 ga watan Mayu don ci gaba da zama.

    Hukumar Hisba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami'an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi yada baɗala a shafukan sada zumunta.

    Daga bisani kuma wata kotu a Kano ta tura ƴar tiktok ɗin zuwa asibitin kula da lafiyar masu taɓin hankali domin duba lafiyar ƙaƙwalwarta.

  12. Rasha na tuhumar waɗanda suka buɗe wuta a gidan rawa da ta'addanci

    ..
    Image caption: Dalerdzhon Mirzoyev (hagu) da Saidakrami Murodali Rachabalizoda

    Rasha na tuhumar mutum huɗu da ta ce sun kai hari kan wani gidan rawa har mutum aƙalla 137 suka mutu.

    Mutanen huɗu sun bayyana a kotu fuskarsu a kumbure- alamar sun sha duka, ɗaya kuma an kai shi kotun a keken guragu. Dukkansu ana tuhumarsu da aikata ta'addanci.

    Ƙungiyar IS ta ɗauki nauyin kai harin na ranar Juma'a tare da wallafa hoton bidiyo don tabbatar da iƙirarin.

    Jami'an Rasha sun ce, babu tantama akwai hannun Ukraine a harin. Kyiv ta musanta iƙirarin.

    Bidiyon wanda IS ta ski ya nuna maharan suna harbin kan mai uwa da wabi cikin gidan rawar kuma BBC ta tabbatar da sahihancin bidiyon.

    Sai dai babu wani jami'in Rasha da ya tabbatar da iƙirarin kuma kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov a wani taron manema labarai a ranar Litinin, ya ce bai dace ya yi magana a kai ba har sai an kammala bincike.

  13. Ma'aikacin Binance ya tsere daga Najeriya

    ..

    Kamfanin Binance ya tabbatar wa BBC cewa ɗaya daga cikin jami'ansa da hukumomin Najeriya suka tsare, a yanzu ba ya hannu daidai lokacin da ake yaɗa rahotannin cewa ya tsere daga Najeriya.

    Nadeem Anjarwalla, wanda ke da fasfon ƙasashen Birtaniya da Kenya, an kama shi ne a cikin watan jiya tare da abokin aikinsa, Tigran Gambaryan, a wani ɓangare na binciken kaucewa biyan haraji da gwamnatin Najeriya ke yi wa kamfanin na kudin kirifto.

    Kakakin Binance ya ce "mun samu labarin cewa Nadeem ba ya hannun Najeriya. Babban abin da muka mayar da hankali a kai shi ne tsaron ma'aikatanmu kuma muna aiki tare da hukumomin Najeriya domin warware batun ba tare da ɓata lokaci ba."

    Har yanzu dai hukumomin Najeriyar ba su ce komai ba a game da haka.

    Tuni dai gwamnatin Najeriya ta maka kamfanin a gaban kotu inda ta shigar da tuhume-tuhume guda huɗu a kansa da suka shafi ƙin biyan haraji.

    Babban bankin ƙasar ya yi zargin cewa fiye da dala miliyan 26 ne ake hada-hadar su a kasuwar hada-hadar kudin kirifto ta Binance.

    Ya kuma zargi shafin da saka wa dala farashi abin da ke ƙara janyo karyewar darajar naira.

  14. Ƴansanda sun tabbatar da mutuwar ƙarin mutum uku a turmutsitsin Bauchi

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar ƙarin mutum uku sakamakon turmutsitsin da aka yi a jihar Bauchi lokacin raba zakkar kuɗi.

    Tun da farko hukumomi sun tabbatar da mutuwar mata huɗu.

    Sai dai wani ɗanjarida a jihar ta Bauchi Hassan Mohammed wanda ke bibiyar lamarin, ya ce yana tunanin mutanen da suka mutu za su kai kusan 17.

    Ƴansanda sun ce sun ƙaddamar da bincike game da turmutsitsin da ya janyo mutuwar mutanen.

    Najeriya dai ta shafe watanni tana fama da matsin tattalin arziki har da tashin farashin kayayyaki.

    A ranar Juma'a, an samu ɗaliban jami'ar jihar Nasarawa da suka mutu a irin wannan turmutsitsin na raba abinci.

  15. An ayyana dokar ta ɓaci kan matsalar fari a Malawi

    ..

    Gwamnatin Malawi ta ayyana dokar ta ɓaci sakamakon matsanancin fari a akasarin gundumomin ƙasar.

    Ita ce ƙasa ta biyu a kudancin Afirka da ta yi haka ckin ƙasa da wata ɗaya.

    Shugaba Lazarus Chakwera ya buƙaci fiye da dala miliyan 200 na jin ƙai. A cewar hukumar samar da abinci ta duniya, ƙasashe da dama a kudancin Afirka na gab da faɗawa ƙangin yunwa saboda tasirin yanayin zafi na El Nino.

    Malawai ce ƙasa ta baya-bayan nan da ta tabbatar da cewa ƙoƙarinta na samar da kayan abinci ya fuskanci tangarɗa sakamakon matsanancin yanayi na fari.

    Ya zo ne ƙasa da wata ɗaya bayan da Zambiya ta ayyana dokar ta ɓaci kan haka.

    Zimbabwe da ke maƙwabtaka ita ma ta fuskanci koma-baya wajen samar da amfanin gona.

    Shugaban Malawi Lazarus Chakwera ya ce kusan gidaje miliyan biyu ne da ke ƙasar na cikin haɗarin fuskantar yunwa bayan da farin ya shafi gunduma 23 cikin 28 da ke ƙasar, abin da ya shafi kusan kashi 45 cikin 100 na amfanin gonar da ake samarwa a ƙasar.

    Ya nemi agajin ton dubu 600 na masara wanda shi ne abincin da aka fi amfani da shi a ƙasar.

  16. Mutum uku sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Nairobi

    Ambaliyar ruwa

    Ana fargabar cewa akalla mutum uku sun rasa ransu a wata ambaliyar ruwa da ta afku a Nairobi, babban birnin Kenya.

    Daga cikin waɗanda suka rasu har da wani jami'in ɗansanda da yake ƙoƙarin ceton wasu iyalai da suka maƙale a yankin Kamakunji.

    Wasu hotuna da bidiyo da aka sanya a kafafen sada zumunta sun nuna yadda mutane a cikin ababen hawa ke tsaye cirko-cirko saboda motocinsu sun maƙale sakamakon ruwan da ya mamaye tituna a birnin.

    Rahotanni sun ce wani ɓangare na babbar hanyar Nairobin ma ta shafe da ruwa.

    Masu hasashen yanayi dai sun ce za a ci gaba da samun mamakon ruwan sama nan da wasu kwanaki masu zuwa a birnin na Nairobi.

    Tuni dai mahukunta suka shawarci mazauna wuraren da ke da haɗarin fuskantar ambaliyar ruwan da su bar wajen.

  17. Zaben Senegal: Dan adawa Bassirou Diomaye Faye na kan gaba a zaben kasar da aka yi

    Fastar Mr Faye

    Jagoran 'yan adawa a Senegal Bassirou Faye, ne ke kan gaba a zaben shugaban kasar Senegal da aka yi, bayan abokan takararsa da dama sun amsa cewa sun sha kayi.

    Miliyoyin al'ummar kasar ne suka kada kuri'a a zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Lahadi, bayan shafe shekaru ana ta fadi tashin siyasa da kuma zanga-zangar 'yan adawa a kan shugaba Macky Sall.

    Masu zabe dai na da damar zaben dan takarar da suke so a cikin mutum 17 da suka tsaya.

    To sai dai kuma dan takarar gamayyar jam'iyyu masu mulki, Amadou Ba, ya yi watsi da rahotannin shan kayi, inda ya ce ya na jiran sake takara a zagaye na biyu na zaben da za a yi wanda a shi ne za a ayyana wanda ya lashe zaben.

    Mr Faye, mai kimanin shekaru 44, babban jigo ne a jam'iyyar da Ousmane Sonko ke jagoranta, ya kasance a tsare a gidan yari kwanaki kafin zaben, yayin da shi kuma Ousmane Sonko aka haramta masa tsayawa takara.

    Sakamakon farko da aka sanar a gidan talbijin din kasar ya nuna cewa Mr Faye ya samu mafi rinjayen kuri'u, abin da ya janyo aka rinka murna a kan titunan babban birnin kasar Dakar.

    Magoya baya sun rinka daga tutar kasar a wani bangare na nuna farin cikin a game da sakamakon da aka bayyana.

    Sakamakon da aka bayyana ya sa biyar daga cikin 'yan takarar sun amsa shan kayi.

    Anta Babacar Ngom, mace daya tilo a cikin 'yan takarar shugaban kasar, cikin wata sanarwa ta ta ya Mr Faye murna.

    Kawo yanzu dai ba a san adadin kuri'un da aka kirga a, to amma ana kyautata tsammanin sanar da sakamakon karshe a gobe Talata.

  18. Aljeriya ta aika ton 150 na kayan jin ƙai zuwa Gaza

    ..
    Image caption: Ma'aikatar tsaro ta Aljeriya ta ce agajin ya nuna cewa ƙasar tana bayan Falasɗinawa

    Aljeriya za ta tura ton 150 na kayan jin ƙai ga Falasɗinawa a Gaza daidai lokacin da ake gargaɗin yiyuwar fuskantar yunwa a can.

    Kayayyakin sun haɗa da abinci da madarar jarirai.

    "Wannan tallafin ya nuna irin goyon bayan da Aljeriya ke da shi ga Falasɗinawa," in ji ma'aikatar tsaron ƙasar.

    Jirgin sojoji ne zai yi jigilar kayan jin ƙan a ranar Litinin daga filin jirgin saman soji na Boufarik da ke kusa da Algiers, babban birnin ƙasar zuwa filin jirgin sama na El-Arish na Masar da ke kusa da zirin Gaza.

    A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, an yi ƙiyasin rabin al'ummar Gaza na fama da yunwa sakamakon watannin da aka shafe ana gwabza yaƙi da Isra'ila.

    MDD ta yi hasashen mutane za su fuskanci yunwa a arewacin Gaza tsakanin Maris da Mayu sannan al'ummar Falasɗinu za su faɗa cikin yunwa nan da watan Yuli.

  19. Gwamnati ta maka kamfanin Binance a kotu kan zargin ƙin biyan haraji

    ..

    Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙara kan kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

    Hukumar tara haraji ta Najeriya, FIRS ce ta sanar da matakin, kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya ruwaito.

    Gwamnatin dai na tuhumar kamfanin na Binance da aikata laifuka huɗu da ke da alaƙa da ƙin biyan haraji.

    Cikin waɗanda ake ƙarar akwai Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, dukkansu manyan shugabannin Binance da yanzu haka ke tsare a hannun hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa.

    Tuhume-tuhumen da ake yi wa Binance sun haɗa da zargin ƙin biyan harajin VAT kan kayayyakin more rayuwa da harajin da kamfanoni ke biya na kuɗin shigar da suke samu da ƙin biyan kuɗaɗen harajin da suka karɓa da kuma haɗa baki da abokanan hulɗarsu wajen kaucewa biyan haraji ta shafinta.

    A cewar gidan Talabijin na Channels, gwamnatin Najeriya tana zargin Binance da ƙin yin rajista da hukumar FIRS saboda dalilai na haraji da kuma saɓawa dokokin biyan haraji a ƙasar.

    Ɗaya daga cikin tuhumar da ake yi ta shafi gazawar Binance na karɓa da kuma biyan nau'ikan haraji ga gwamnati kamar yadda yake a sashe na 40 na dokar FIRS ta 2007 da aka yi wa gyaran fuska.

    Gwamnatin Najeriya ta ce tana kan ƙudurinta na tabbatar da cewa kamfanonin kirifto suna mutunta dokokinta na haraji tare da magance almundahana a tsakanin irin kamfanonin.