Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Mukhtari Adamu Bawa da Umar Mikail

time_stated_uk

  1. Sai da safenku

    Ƙarshen rahotonnin ke nan a wannan shafi.

    Mu zama lafiya.

  2. Isra'ila ta tsinci kanta cikin kaɗaici - Shugaban Hamas Haniyeh

    Ismail Haniyeh

    Shugaban ƙungiyar Hamas ya ce ƙuri'ar neman tsagaita wuta da Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa ta nuna irin "kaɗaicin da" Isra'ila ta tsinci kanta a ciki a yaƙin da take yi da ƙungiyar a Zirin Gaza.

    Da yake magana yayin taron manema labarai, kamar yadda kamfanin labarai na Iran IRNA ya ruwaito, Ismail Haniyeh ya ƙara da cewa "kaɗaicin" da Isra'ilar ke fama da shi na ƙara bayyana cewa "Amurka ta gaza wajen kallafa wa sauran duniya ra'ayinta ba" - yana mai nuni da Amurkar a matsayin babbar ƙawar Isra'ila.

    Haniyeh ya ci gaba da cewa halin da Isra'ila ta tsinci kanta "manuniya ce ga irin jajircewar Hamas da kuma al'ummar Falasɗinu".

    Da yake magana kan abin da ƙudirin na MDD ya ƙunsa - wanda ya nemi a tsagaita wuta a yaƙin nan take saboda azumin watan Ramadan da kuma sakin mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza - Haniyeh ya ce ƙudirin bai cika ba.

    Isra'ila ta zargi Hamas da gabatar da buƙatun "da ba za su yiwu ba" a tattaunawar tsagaita wuta.

  3. Falasɗinawan da aka kashe a Gaza sun zarce 32,000 - Ma'aikatar lafiyar Gaza

    ..

    Ma'aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza ta ce adadin mutanen da suka mutu a Gaza sun ƙaru zuwa 32,424.

    An kashe mutum 81 cikin kwana ɗayan da ya gabata yayin da wasu 93 suka ji rauni, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana cikin wata sanarwa.

    Ana ci gaba da gwabza yaƙi a Gaza yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hari a yankin duk da amincewa da ƙudirin neman tsagaita wuta da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ranar Litinin.

  4. Mutum shida sun ɓata bayan karyewar babbar gadar Baltimore

    Gadar Baltimore

    Hukumomi a Baltimore da ke Maryland a Amurka sun ce har yanzu ba a ga mutum shida ba bayan da babbar gadar yankin ta karye.

    A rahoton da aka sanar a baya, an sanar da ɓacewar mutum bakwai.

    An gano mutum biyu - ɗaya an kai shi asibiti, ɗayan kuma bai samu rauni ba.

    Sakataren harkokin sufuri a jihar ta ce ana tunanin mutanen shida suna cikin masu aiki kan gadar a lokacin da ta karye.

    Ya ƙara da cewa jami'ai ba sa tunanin akwai wani da ya ɓata wanda yake cikin wata mota lokacin da lamarin ya faru.

  5. Hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta ce ta damƙa kuɗin mamata ga danginsu a Bauchi

    Accident scene

    Hukumar kiyaye aukuwar haɗurra ta jihar Bauchi ta ce ta damƙa wa dangin wasu mutane da hatsari ya ritsa da su a kan hanyar Bauchi zuwa Toro, kuɗi naira 1, 680,700, mallakar 'yan uwan nasu.

    Rilwanu Sulaiman Birnin Kebbi, jami'in wayar da kai na hukumar ya ce kuɗin mallakar mutum uku ne, a cikinsu har da wanda yake da naira 1, 648, 500.

    Ya ce hukumarsu ta damƙa kuɗin ne ga dangin waɗanda suka mutu a ofishinta da ke yankin Toro, bayan kammala bincike a ranar Litinin.

    Hatsarin dai ya yi muni, wanda Rilwanu Sulaimanu ya ce ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu, yayin da uku suka jikkata kuma suna kwance suna jinya a asibiti.

    Cash belonging to an accident victim

    Hatsarin mota kusan ruwan dare ne a Najeriya, inda ɗumbin mutane suke mutuwa a kan tituna sanadin karon ababen hawa da sauran dalilai.

  6. Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa sau biyu a wata ɗaya

    ..

    Babban Bankin Najeriya ya yi ƙarin kuɗin ruwa da kashi 2% karo na biyu kenan cikin wata ɗaya, inda yanzu ya kai kashi 24.75, a cewar gwamnan bankin Olayemi Cardoso.

    Shi ne karo na biyu da CBN ya yi ƙarin a cikin wata daya, bayan ƙara kashi 4% a watan Fabrairu.

    Shawarar babban bankin wanda shi ne ƙari mafi yawa a cikin kusan shekara biyu, na da nufin taƙaita samun kuɗaɗen jari da rage hauhawar farashi.

    Hauhawar farashi a Najeriya yanzu ta kai kashi 31.7%, sanadin tsadar farashin abinci da na makamashi, tashin kuɗin sufuri da kuma taɓarɓarewar tsaro a yankunan da ake samar da abinci.

    Kayan abincin sun haɗar da burodi da shinkafa da nama da nono da kayan marmari duka sun ninka farashinsu.

    Najeriya mafi girman tattalin arziƙi a Afirka na fuskantar tsattsauran yanayin tattalin arziƙi, lamarin da ya ingiza mutane da dama cikin talauci.

  7. Ƙarin kuɗin kujerar hajji bai shafi masu adashin gata ba – Nahcon

    ..

    Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta bayyana cewa ƙarin kuɗin kujerar hajj da ta yi a baya-bayan nan ba zai shafi maniyyatan da suka biya ta tsarin adashin gata ba.

    Hukumar ta Nahcon ta bayyana haka ne ƴan kwanaki bayan fitar da sabon farashin kujerar hajjin ga maniyyatan bana.

    Nahcon ta ce ita ce za ta ɗauki nauyin biyan cikon kuɗaɗen maniyyatan da suka biya ta tsarin adashin gata abin da ke nufin maniyyatan ba za su biya ƙarin ko sisi ba.

    A ranar Lahadi ne hukumar ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin suka koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya tare da bai wa maniyyatan wa'adin kwana huɗu su cika kuɗin.

    Ta jingina matakin nata ga yadda farashin dala ke ci gaba da hauhawa wadda da ita ce ake yin ƙiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke buƙata.

    Tun bayan sanar da ƙarin kuɗin ne al'umma suke ta bayyana ra'ayoyinsu inda wasu ke ganin matakin ya zo a ƙurarren lokaci ganin yadda ake fama da tsadar rayuwa a ƙasar.

    Adashin gata tsari ne da Nahcon ya ɓullo da shi shekarun da suka gabata domin saukakawa maniyyata wajen tara kudin gwargwadon halin da mutum yake da shi.

    Hukumar alhazai ta dauko wannan tsari na adashin gata daga kasashe kamar Malaysia da Indonesia, inda 'yan kasar ke irin wannan tarin kudi don sauke faralli.

    View more on twitter
  8. An yi sammacin Sheikh Gumi saboda kalamansa kan ƴan bindiga

    ..

    Hukumomin tsaro sun gayyaci fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi saboda kalamansa da kuma kiran da ya yi na a yi wa ƴan bindiga afuwa, kamar yadda rahotanni daga kafofin yaɗa labaran ƙasar suka nuna.

    Sheikh Ahmad Gumi, wani tsohon jami'in soja ne da ke Kaduna a arewacin Najeriya kuma ya sha tayin shiga tsakanin hukumomi da kuma ƴan bindiga masu garkuwa da satar mutane don neman kuɗin fansa a ƙasar.

    A baya-bayan nan ne aka ba da rahoton cewa malamin ya yi tayin tattaunawa da ƴan bindigar a kan sakin gomman ɗaliban da aka sace a farkon watan nan daga wata makaranta da ke Kuriga a jihar Kaduna.

    Sai dai gwamnan Kaduna Uba Sani ya ce babu hannun Sheikh Gumi a sakin ɗaliban.

    Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris a ranar Litinin ya ce jami'an tsaro sun gayyaci Sheikh Gumi domin yi masa tambayoyi inda ya ce malamin bai fi ƙarfin doka ba.

    "Idan ka furta kalamai, musamman waɗanda suka shafi tsaron ƙasa, ya zama dole jami'an tsaro su ƙara tunani, kuma abin da suke yi ke nan," kamar yadda aka ruwaito ministan na cewa.

    A baya dai Sheikh Gumi ya yi iƙirarin ganawa da jagororin ƴan fashin daji domin neman su tuba daga sace-sacen mutane.

  9. An fara miƙa wa dangi gawawwakin 'masu azumin mutuwa' a Kenya

    ..

    Hukumomi a Kenya sun fara sakin gawawwakin mutanen da suka mutu a al'amarin ƙungiyar asiri, wanda ake zargin cewa an ƙarfafa musu gwiwar yin azumi ne har sai sun riga mu gidan gaskiya.

    An shaida gawa 34 a cikin 429 da aka haƙo a Daji Shakahola mai nisa da ke kusa da garin gaɓar ruwa na Malindi da taimakon samfuran DNA na danginsu.

    A ranar Talata ne aka miƙa gawa bakwai ga danginsu. Limamin Kiristan da ya naɗa kansa PaulNthenge Mackenzie ya riƙa yin wa'azin cewa lokacin tashin alƙiyama ya kusa.

    An zarge shi da ingiza ɗaruruwan mabiyansa su yi "azumi" don su ga Yesu cikin sauƙi, amma dai ya musanta da hakan. Malamin makaranta Francis Wanje ya karɓi gawa huɗu, a ciki har da ta 'yarsa da surukinsa da kuma jikansa.

    Ya rasa mutum takwas a cikin danginsa, waɗanda ɓatansu ne kuma ya taimaka wa masu bincike suka gano manyan kaburbura a makeken dajin Shakahola.

  10. 'An kashe Falasɗinawan da suka ɗaiɗaita a harin Rafah'

    ..

    Kafofin yaɗa labarai a Falasɗinu sun ruwaito cewa aƙalla mutum 18 ciki har da yara tara da mata da dama aka kashe a wani hari cikin dare da Isra'ila ta kai kan wani gini a wajen Rafah da ke kudancin Gaza.

    Cibiyar yaɗa labarai da ke da alaƙa da Hamas da kamfanin dillancin labarai na Safa ya ce ginin da ke Musabah mallakin iyalin Abu Naqira ne kuma gomman mutanen da aka ɗaiɗaita na samun mafaka a can.

    Da safiyar ranar Talata ne, ɗan jarida Huseein Eslayeh ya wallafa bidiyo a shafin X inda ya nuna abin da ya yi saura daga ginin da harin ya shafa.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa hotuna daga wurin da ginin ya rushe.

    Wani bidiyo da Eslayeh ya naɗa a wajen asibitin al-Najjah da ke Rfah ya nuna mutane tsaye cikin jimami yayin da ake binne mutanen da aka kashe.

  11. Hotunan babbar gadar Baltimore da ta karye a Amurka

    ..
    ..
    ..
  12. An gano fiye da dala miliyan 10 da aka cire sanadin tangarɗar na'ura – Bankin Ethiopiya

    ..

    Babban bankin kasuwanci na Ethiopiya ya ce ya gano fiye da kashi uku bisa huɗu na kuɗin da ta rasa sakamakon tangardar da aka samu wadda ta bai wa abokanan hulɗarsa damar cirar fiye da kuɗin da suke da shi a asusunsu.

    Cikin wata sanarwa, shugaban bankin, Abe Sano ya ce an cire fiye da dala miliyan 14 daga na'urar cirar kuɗi ko kuma aka tura zuwa wasu asusun a lokacin da aka samu matsalar kwanaki 10 da suka gabata.

    An maido da fiye da dala miliyan 10, in ji Mista Abe.

    Rahoton farko daga jaridun ƙasar ya nuna kuɗin da aka yi hada-hadarsu a lokacin da aka samu matsalar na iya kai wa dala miliyan 40.

    Ɗalibai ne suka fi cirar kuɗi a lokacin da aka fuskanci tangarɗar.

    A cewar shugaban bankin, dubban abokanan hulɗar sun mayar da kuɗin bisa raɗin kansu inda ya ƙara da cewa waɗanda suka ƙi mayar da kuɗin da suka cira na iya fuskantar tuhumar aikata babban laifi.

  13. An ayyana dokar ta ɓaci bayan karyewar gada a Baltimore

    Gwamnan Maryland, Wes Moore ya ayyana dokar ta ɓaci a Maryland sakamakon karyewar gadar Francis Scott da ke Baltimore.

    Moore ya ce "muna aiki tare da tawagar hukumomi domin tura kayan agaji daga gwamnatin Biden."

    Ya yaba wa jarumai maza da mata da suke aiki tuƙuru domin kuɓutar da waɗanda lamarin ya ritsa da su".

    Ya ƙara da cewa zai ci gaba da bibiyar hukumomin tarayya na jiha da kuma ƙananan hukumomi da ke gudanar da ayyukan agaji yayin da suke ci gaba da nazari da kai ɗauki".

  14. Bidiyon yadda gadar sama ta dare a Baltimore

    Wani katafaren jirgin ruwa ya yi taho mu gama da wata gada da ke Baltimore a Amurka lamarin da ya janyo gadar ta dare tare da ruftawa cikin ruwa.

    Lamarin ya faru ne da ƙarfe 1:30 agogon ƙasar.

    Mahukunta sun ce kimanin mutum 20 ne suka faɗa ruwan bayan da lamarin ya faru.

    A cewar babban jami'in ɗansanda a Baltimore, an tsamo mutum biyu daga ruwan.

    Zuwa yanzu dai ma'aikatan ceto na ci gaba da ƙoƙarin nemo waɗanda suka nutse.

    Video content

    Video caption: Latsa hoton don kallon bidiyon yadda gadar ta dare bayan da jirgin ruwa ya buge ta
  15. An yanke wa ɗan Chinan da ya kashe Ummita hukuncin kisa

    ..

    Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke wa ɗanƙasar China Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe budurwarsa, Ummukhulsum Sani Buhari.

    Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Haruna Dederi ne ya tabbatar wa BBC hukuncin kotun bayan zaman shari'ar da aka yi ranar Talata.

    Ya ce "alƙali ya yi hukunci inda ya sami Frank da laifin kisan kai wanda hukuncinsa kisa ne kuma ya zartar da hukunci a kan haka." in ji kwamishinan.

    Ya ƙara da cewa "ita shari'a tana da farko tana da ƙarshe, kuma abubuwan da aka iya bi sawu aka gano yayin tuhumar wanda ake tuhuma sune ake kafa hujja da su a kai ga hukunci,"

    "Abubuwan da suka gabata sune suka wajabta wa kotu ta ɗauki irin wannan matsayi." kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

    A ranar 16 ga Satumban 2022 ne ɗanChinan ya daɓa wa marigayiyar wuƙa a gidansu da ke unguwar Janbulo a Kano.

  16. Muna sane da tsare ɗanƙasarmu ma'aikacin Binance a Najeriya – Amurka

    Binance

    Amurka ta ce tana da masaniya a kan rahotannin tsare ɗanƙasarta a Abuja, babban birnin Najeriya.

    A watan da ya gabata ne aka kama shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan tare da abokin aikinsa, Nadeem Anjarwalla, wanda ke da fasfon Birtaniya da Kenya a wani ɓangare na binciken kaucewa biyan haraji da gwamnatin Najeriya ke yi wa kamfanin na kuɗin kirifto.

    Mai magana da yawun ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, "A duk lokacin da aka samu wata matsala ta tsare ɗanƙasarsu a wata ƙasa, to ofishin jakadancin da ke ƙasar na yin duk mai yiwuwa wajen bayar da taimakon da ya dace."

    Ofishin jakadancin ya ƙi bayar da cikakken bayanai game da tsare ɗanƙasar, yana mai cewa saboda dalilai na sirri.

    Yanzu haka Nadeem Anjarwalla, ba ya hannun Najeriya bayan da mahukuntan ƙasar suka tabbatar da cewa ya tsere, to amma wata majiya daga makusantansa ta ce ya bar Najeriya ne ta hanyar da ta dace.

    Mahukuntan Najeriya dai sun ce suna aiki da jami'an tsaro don samar da takardar sammaci ga Mr Anjarwalla.

    A ɓangare guda kuma, mahukuntan Najeriya sun maka kamfanin a gaban kotu inda suka shigar da tuhume-tuhume da suka shafi ƙin biyan haraji.

  17. Afirka ta Kudu ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Rikicin Gaza

    Afirka ta Kudu ta yi maraba da batun tsagaita wuta da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta a Gaza.

    Cikin wata kuri'a da aka kada a ranar Litinin, kwamitin ya bukaci a tsagaita wuta har zuwa karshen watan Ramadan, wanda zai kare nan da makonni biyu.

    Cikin wata sanarwa da ministar harkokin wajen Afirka ta Kudu Naledi Pandorin, ta fitar,ta ce kasarta ta ji dadin yarjejeniya, to amma ta yi kira da a samu tsagaita wuta ta dindindin.

    Ta ce," Yanzu alhakin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin duniyar ne ya tabbatar da cewa ba a samu wata matsala a wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta ba."

    Yarjejeniyar tsagaita wutar wadda a cikinta aka yi kiran da a saki mutanen da aka tsare da su, ta samu cikas a lokuta da dama.

    Wannan ne dai karon farko da kwamitin ya yi wannan kiran tun bayan fara yakin.

    Amurka dai ta kauracewa kada kuri'ar, yayin da sauran kasashe 14 na kwamitin kuma suka kada kuri'ar amincewarsu da batun tsagaita wutar.

  18. Zan yi shugabanci cikin ƙas-ƙas da kai – Zaɓaɓɓen shugaban Senegal

    ..

    Zaɓaɓɓen shugaban Senegal Bassiorou Diomaye ya yi alƙawarin yin mulki tare da ƙas-ƙas da kai da kuma nuna gaskiya.

    Ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka yi ranar Lahadi.

    Babban abokin hamayyar Mista Faye daga jam'iyya mai mulki Amadou Ba tuni ya amince da shan kaye abin da ya sa Faye mai shekara 44 ya zama shugaban ƙasa mafi ƙanƙantar shekaru a tarihin ƙasar.

    "Zaɓe na da aka yi ya nuna al'ummar Senegal sun amince su tsame kansu daga abubuwan da suka faru a baya," kamar yadda ya faɗa wa ƴan jarida a ranar Litinin.

    "Na yi alƙawarin yin shugabanci tare da ƙas-ƙas da kai da kuma gaskiya."

    Ɗaya daga cikin manyan ƙudurorinsa a matsayin shugaban ƙasa shi ne "haɗa kan ƴan kasa" sakamakon yadda aka shafe shekara uku ana tashin hankali da kuma rikicin siyasa a ƙasar, kamar yadda Mista Faye ya bayyana.

    Ya kuma yi alƙawarin "yaƙar cin hanci a kowane mataki" da sake gina hukumomi tare da magance matsalar tsadar rayuwa.

    Mista Faye ya kuma gode wa shugaba Macky Sall mai barin gado ganin yadda ya taimaka aka gudanar da zaɓe cikin cikin nasara.

    Sakamakon zaɓen wanda ba na hukuma ba ya nuna Mista Faye ne ke kan gaba da kusan kashi 53.7 cikin 100 yayin da Mista Ba yake da kashi 36.2 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

    Nasararsa na zuwa ne ƙasa da mako biyu bayan da aka sake shi daga gidan yari.

  19. Ina Kwana!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi na Kai Tsaye, barka da warhaka.

    Da fatan mun wayi gari lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu kawo maku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a duniya, musamman Najeriya da ƙasashe maƙwabta.

    Sai ku kasance tare da mu, kuna kuma iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin karanta ƙarin labarai da kallon bidiyo.