Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba, Usman Minjibir, A'isha Babangida, Umar Mikail da Ahmad Tijjani Bawage

time_stated_uk

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Ƴan bindiga sun tayar da garuruwa a Sokoto

    Ƴan bindiga sun kai hari tare da tayar da garuruwa da dama a yankin Isa da Sabon Birni a jihar Sokoto.

    Ƴan bindigar sun kashe mutane tare da ƙona gidaje da kuma yin awon gaba da wasu da ba a san adadinsu ba.

    Hon Muhammad Sa’idu Bargaja, ɗan majalisar tarayya ne da ke wakiltar Isa da Sabon Birni, ya ce hare-hare-hare sun tilastawa ɗaruruwan mutane tserewa zuwa garuruwa makwabta bayan tayar da garuruwa sama da 40.

    Latsa ƙasa don sauraron ƙarin bayani da ya yi wa Awwal Ahmad Janyau.

    Video content

    Video caption: Ƴan bindiga sun tayar da garuruwa da dama a Sokoto
  3. Ana fargabar bakuwar cuta ta kashe mutum 45 a Kano

    Cuta

    Ana fargabar cewa mutum 45 ne suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar wata cuta da ba a kai ga tantance ta ba a kauyen Gundutse da ke karamar hukumar Kura ta jihar Kano.

    Waɗanda lamarin ya shafa akasari mata ne da kananan yara da kuma tsafaffi inda suka riƙa yin amai da gudawa.

    Sai dai gwamnatin jihar ta ce ba wata bakuwar cuta ba ce, illa tasirin sauyin yanayi ne ya haifar da zazzaɓi mai tsanani.

    Bayanan dawakilinmu Zahraddeen Lawan ya tattaro daga garin na Gundutse da ke cikin karamar hukumar Kura a jihar Kano, na cewa mazauna yankin sun shiga firgici ne tun makonni biyu da suka gabata, bayan da suka lura da cewa yara kanana akasari mata suna yawan kwantawa rashin lafiya mai kama da zazzaɓi da kuma amai da gudawa.

    Al'amarin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

    Wannan magidanci yace yarsa me shekara goma ce ta fara kwantawa rashin lafiya daga nan kuma sai kaninta shima ya kamu.

    Ya ƙara da cewa wasu jami’an ma’aikatar lafiya sun je garin inda suka deɓi ruwan wata tuka-tuka, don yin gwaje-gwaje, amma a cewarsa ga alama ba a gano wani abu ba.

    Shi ma wani mutumi ya tabbatar da cewa ‘ya’yansa biyu ne suka rasu, bayan da zazzaɓi mai zafi ya lulluɓe su na ɗan wani lokaci.

    Kwamishinan ma’aiktar lafiya na jihar Kano, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya shaida wa wakilin namu cewa sun tura jami’ansu zuwa garin inda suka gudanar da bincike don gano cutar.

    Sai dai Dr Abubakar ya ce har yanzu bincikensu bai tabbatar da rahotanni da ke cewa mutum 45 sun rasu ba, amma ya ce hakan zai iya kasancewa.

    Ya ƙara da cewa sun zuba maganin kashe cutuka a ɗaukacin rijiyoyin yankin, inda ya ya shawarci jama’a su riƙa kwana a cikin gidan sauro a wuri kuma da iska ke kewayawa.

  4. Mutum 18 sun jikkata a harin da Lebanon ta kai Isra'ila

    Kafofin yaɗa labaran Isra'ila sun ruwaito cewa mutum 18 sun jikkata a wani hari da Lebanon ta kai arewacin Isra'ila.

    Jaridar Haaretz ta ruwaito cewa wasu dakarun ko-ta kwana na Isra'ila guda shida ne aka jikkata.

    Wasu majiyoyi sun ce ɗaya daga cikin dakarun yana cikin mawuyacin hali.

  5. Ministan harkokin wajen Turkiyya ya zargi Netanyahu da ƙoƙarin jefa yankin cikin yaƙi

    Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya zargi Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ƙoƙarin "ci gaba da zama a kan mulki" ta hanyar janyo fargaba a yankin.

    "Ta nuna ƙarara cewa Netanyahu na ƙokarin jefa yankin Gabas Ta Tsakiya cikin yaƙi don ya ci gaba da zama a kan mulki," kamar yadda ministan ya faɗa a wani taron manema labarai a Doha, babban birnin Qatar.

    Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da shugaban ofishin siyasa na Hamas, Ismail Haniyeh, ke shirin kai ziyara ƙasar a matsayin babban bako ga shugaba Recep Tayyip Erdogan a makon nan.

    Mista Erdogan ya soki shugabannin Isra'ila tun fara yaƙi a Gaza.

  6. Sojojin Najeriya sun tarwatsa yankunan ƴan Boko Haram da ISWAP a Borno

    Sojoji

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun tartwatsa wani yanki da mayaƙan Boko Haram da kuma ƴan ƙungiyar ISWAP a yammacin Afrika ke da karfi a jihar Borno.

    Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X, ta ce dakarunta na Desert Sanity III sun tarwatsa wuraren ne da ke kauyukan Ngumne, Kawaran da kuma sassan Mangu da ke dajin Sambisa.

    Duk da irin barazana da sojojin suka fuskanta a kan hanya na abubuwan fashewa da aka binne, sun ci karfin 'yan ta'addan, inda suka yi musu lugudan wuta tare da tarwatsa wuraren nasu.

    Sojojin sun samu nasarar kwato muhimman makamai da wasu kayan aiki, da suka haɗa da motoci guda biyu ɗauke da bindigogi, wasu abubuwan fashewa guda biyu, da kuma wani bututun gurneti na roka da ya kone.

    "Wannan gagarumin farmakin na nuni da yadda sojojin Najeriya ke da niyyar kawar da ta'addanci da kuma tabbatar da tsaro a yankin. Kwato manyan bindigogi na nuna koma baya ga 'yan ta'addar," in ji sanarwar.

    View more on twitter
  7. Kotun Kano ta ɗage zaman tuhumar Ganduje

    Abdullahi Ganduje

    Wata babbar kotu da ke Kano ta ɗage sauraron tuhumar da gwamnatin jihar ke yi wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje kan cin hanci da rashawa.

    Bayanai sun nuna cewa kotun ta ɗauki matakin ne saboda rashin sanar da waɗanda ake ƙara batun shari’ar.

    Mai Shari’a Usman Na’abba ne ya ba da umarnin ɗage ƙarar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu bayan da lauyan mai gabatar da ƙara Y. A. Adamu ya sanar da kotun cewar dukkan yunƙurin da suka yi na sanar da waɗanda ake ƙara ya ci tura.

    Sai dai lauyan Ganduje, Barista Musa Lawan ya ce tun da fari rashin sanar da su ƙarar da aka shigar ne ya sa suka ƙaurace wa zaman, amma yanzu suna jiran a sanar da su.

    Gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje da matarsa da ɗansa da kuma wani abokinsa da aikata laifuka takwas, waɗanda suka danganci cin hanci da rashawa.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari ƙarin bayanin da lauyan Ganduje, Musa Lawan ya yi wa Khalifa Shehu Dokaji:

    Video content

    Video caption: Latsa hoton sama ku saurari hira da lauyan Ganduje Barista Musa Lawan
  8. Kotu ta hana EFCC kama tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello

    Yahaya Bello

    Wata babbar kotun jihar Kogi ta hana hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya kama tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello.

    Mai Shari'a I.A Jamil ne ya bayar da umarnin yayin zaman da kotun ta yi a yau Laraba, inda ta ba da umarnin hana tsarewa da kuma tuhumar tsohon gwamnan.

    Alƙalin ya ce yunƙurin tauye wa Yahaya Bello haƙƙi "haramtacce ne" har sai kotun ta ba da umarnin yin hakan, kamar yadda kafofin yaɗa labarai a Najeriya suka ruwaito.

    Sai dai jami'an hukumar na can sun yi wa gidan tsohon gwamnan ƙawanya a unguwar Zone 4 da ke Abuja babban birnin ƙasar domin kama shi.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan Kogi na yanzu, Usman Ododo, ya ziyarci Yahaya Bello a gidan kuma akwai yiwuwar shi ne ya fitar da shi daga gidan a motarsa.

  9. Isra'ila za ta ɗauki matakin da ta ga ya dace kan Iran - Netanyahu

    Cameron

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya faɗa wa Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya David Cameron cewa ƙasarsa "za ta ɗauki mataki da kanta" kan harin da Iran ta kai mata.

    Ya ce gwamnatinsa za ta yi "duk mai yiwuwa wajen kare kan ta" yayin ganawar da gwamnatin Birtaniya ke fatan za sa Isra'ila ta sassauta kan batun harin.

    Mista Netanyahu ya jaddada cewa za su rama harin makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da Iran ta kai mata ranar Asabar.

    Mista Cameron ya faɗa masa cewa duk martanin da za su mayar ya kamata ya zama "cikin nutsuwa" kuma maras girma.

  10. Tsarin kula da lafiyar mata ya fuskanci koma-baya – MDD

    Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa koma bayan da aka samu a tsarin kiwon lafiyar mata yayin haihuwa ya jefa kokarin da aka yi tsawon shekaru 30 na dakile matsalar cikin hadari.

    Asusun kula da yawan al'umma na Majalisar Dinkin Duniya, ya gano cewa mata 800 na mutuwa a yayin haihuwa a rana guda a fadin duniya, abin da ya nuna irin adadin da ake samu ke nan tsawon shekaru 8 da suka wuce.

    Rahoton ya ce akwai bukatar a samo hanyoyin inganta lafiyar mata da yammata domin magance matsalolin da ake fuskanta a yayin goyon ciki da ma haihuwa.

    Kazalika rahoton ya ce ya bayyana cewa akwai bambamce bambancen da ake samu a sassan duniya.

    Ya ce ana samun mata masu juna biyu kamar 130 da ke fa da matsaloli a yayin goyon ciki a Afika wadanda kuma ke cikin barazanar rasa ransu yayin haihuwa fiye da yadda ake samu a kasashen nahiyar turai da kuma Arewacin Amurka.

  11. Tinubu ya ce a faɗa wa gwamnatin Kano ni ne shugaban APC - Ganduje

    ...

    Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa wanda mazaɓarsa ta ce ta dakatar da shi, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin Jihar Kano ba ta isa ta ƙwace kujerarsa ba, yana mai cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu da kansa ne ya tabbatar masa cewa "kujerarsa na nan daram-dam.

    Ganduje ya bayyana haka ne a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke nuna shi yana jawabi ga dandazon magoya bayansa da suka kai masa ziyara a gidansa na Abuja domin nuna goyon baya.

    Ya ce "jiya na ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu kuma na yi masa bayanin komai kuma ya gode muku abin da kuka yi." in ji Ganduje yayin da yake magana ga magoya bayansa.

    "Sannan shugaban ya ce ku yi hakuri, wannan kujerar da suke hari, kujerar tana nan ta zauna daram-dam." in ji Ganduje.

    Tsohon gwamnan ya kuma ce Tinubu ya tabbatar masa da cewa kujerar shugabancin jam'iyyar APC ta Najeriya tasa ce kamar yadda ya faɗa "kujerar shugabancin APC ta Najeriya tana kan Abdullahi Umar Ganduje."

    An nuna magoya bayansa a cikin bidiyon suna ta murna da shewa da tafi yayin da tsohon gwamnan ke gabatar da kalamansa.

    A yau Laraba ne dai wata babbar kotu a jihar Kano ta dakatar da Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan wasu shugabannin APC tara a mazaɓar ta Ganduje suka shigar da ƙara kan a dakatar da shi bayan wata takardar koke da wani ɗan jam'iyyar Ja'afaru Adamu ya shigar.

    A takardar koken, Adamu ya yi magana kan tuhume-tuhumen rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan inda ya buƙaci jagororin mazaɓar su gudanar da bincike kan batun domin farfaɗo da ƙimar jam'iyyar da kuma tasirin da batun zai yi a fafutukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yaƙi da rashawa.

  12. Kwamitin gudanarwar PDP ya kaɗa ƙuri'ar ƙauna ga Umar Damagum

    ..

    Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar PDP a Najeriya ya bayyana goyon bayansa ga shugaban jam'iyyar na ƙasa na riƙon ƙwarya, Umar Damagum.

    Sakataren harkokin watsa labarai najam'iyyar, Debo Ologunada, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

    Ya ce kwamitin gudanarwar ya nuna goyon bayan ne ga shugaban na riƙon ƙwarya a taronsa na 54 da ya gudanar ranar Talata.

    Ologunagba ya ce kwamaitin ya nuna goyon bayan ne bisa la'akari da irin ƙoƙarinsa wajen sake wa jam'iyyar ta PDP fasali domin ta amsa sunanta na babbar jam'iyyar adawa a Najeriya.

    A ranar Alhamis ɗin nan ne dai jam'iyyar za ta gudanar da babban taronta inda a nan ne za a tabbatar da ci gaba da shugabancin Umar Damagum a matsayin shugaban jam'iyyar ko kuma a tsige shi.

    A 2023 ne dai aka naɗa Umar Damagum a matsayin shugaban jam'iyyar ta PDP bayan dakatar da tsohon shugaban jam'iyyar, Cif Iyorchia Ayu.

  13. An kashe mutum 13 a rikicin arewacin Darfur

    ...

    Fararen hula 13 ne aka kashe a arangamar da aka yi tsakanin sojoji -da ke samun goyon bayan tsaffin kungiyoyin 'yan tawaye da kuma RSF a jihar Darfur ta Arewa da ake fafatawa tsakanin sojojin Sudan da rundunar RSF.

    Shafin intanet mai zaman kansa na Darfur 24 ya ruwaito a jiya cewa sojojin sun kai hare-hare ta sama a kan wuraren RSF a Kutum, kimanin kilomita 136 daga arewacin El Fashir babban birnin jihar, wanda yake a ƙarƙashin hannun sojojin.

    Ta kuma ƙara da cewa an yi taho-mu-gama a yankunan arewaci da gabashin birnin, da kuma sansanin 'yan gudun hijira da ke wajen El-Fashir.

    Dakarun RSF sun kai hare-hare akai-akai kan sansanonin soji da ke El Fashir a yunkurinsu na kwace babban birnin jihar da kuma karfafa yankin Darfur da yaƙi ya ɗaidaita.

    Wasu manyan tsaffin ‘yan tawaye guda biyu da ke da sansani a yankin sun shiga fafatawar a watan da ya gabata, inda suka yi alkawarin yin yaƙi tare da sojoji domin kare fararen hula.

    Hemedti ya ce a shirye ya ke ya ayyana tsagaita buɗɗe wuta a wani sakon bidiyo da ya fitar a ranar 15 ga watan Afrilu a daidai lokacin da Sudan ke bikin cika shekara na yaƙin da ake yi tsakanin dakarunsa da sojojin kasar.

    Shugaban Sudan, Burhan bai mayar da martani ba amma ya sake nanata a cikin saƙon farko na bikin Eid al-Fitr kokarinsa na samun nasara a kan RSF.

  14. Harin Rasha da makami mai linzami ya kashe fararen hula a arewacin Kyiv

    ...

    Harin makami mai linzami da sojojin Rasha suka kai a Chernihiv da ke arewacin Ukraine ya yi sanadin mutuwar fararen hula da jikkata mutane da dama a cewar shugaban yankin Vyacheslav Chaus.

    Chaus ya bayar da rahoton cewa, makami mai linzami guda uku ne aka harbo kusa da tsakiyar birnin, kuma jami'an agajin gaggawa na wurin a lokacin.

    Mukaddashin magajin garin Oleksandr Lomako ya tabbatar da mutuwar mutane akalla biyar a harin.

    Harin dai ya zo ne jim kaɗan bayan rahotannin harin da sojojin Ukraine suka kai a filin jirgin saman sojin Rasha da ke yankin Crimea.

    Har yanzu ba a tabbatar da cikakkun bayanai ba, ko da yake kafofin sada zumunta na cikin gida sun yada bidiyon wata gobara da ta tashi a filin jirgin sama a Dzhankoy da ke arewacin Crimea.

    A Chernihiv kuma, magajin garin, Oleksandr Lomako ya ce makamai masu linzami na Rasha sun kai hari kan wani gini mai hawa takwas wanda ya bayyana a matsayin ababen more rayuwa a wani yanki mai dimbin jama'a.

    Bidiyon da ke wurin ya nuna yadda mutane ke neman kariya da tsira a wata tashar bas a cikin birnin. Jami’ai sun yi kira ga jama’a da su fito domin bada jini.

  15. Mun kasa samun mazan aure - Matan boko haram da suka tuba

    ..

    A yayin da mayaƙan Boko Haram da suka tuba kuma suka miƙa wuya ga gwamnati tare da ajiye makamansu da kuma yin watsi da ayyukan ta’addanci ke ci gaba da samun karɓuwa a hannun al'ummomi, akwai matukar damuwa da matan cikinsu suka ce suna fuskanta ta wahalar samun mazajen aure.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa wani bincike da aka yi ya nuna cewa, ko da yake ‘yan ta’addar da suka tuba suna zaune a cikin al’ummominsu daban-daban, matan da ke cikinsu sun koka da cewa tun dawowarsu, babu wani na miji da ya fito neman aurensu, kasancewar mazajen suna guje musu kamar annoba.

    Bayanai daga hukumomi sun nuna cewa adadin ƴan boko haram ɗin da suka miƙa wuya da iyalansu ya kai 162,000, amma babu irin wadannan bayanan da suka nuna adadin waɗanda suka sake aure, ko kuma zawarawa a cikinsu.

    Wasu daga cikin shugabannin al’ummomin sun koka da yadda mazajensu ke fargabar shiga kowace irin salon soyayya da ƴan matan boko haram din duk da cewa sun miƙa wuya da kuma yadda wasu daga cikin matan ke bayyana sha’awarsu ta neman aure.

  16. Jami'an tsaro sun kashe ƴan tawaye 29 a Indiya gabanin babban zaɓe

    ..

    Jami'an tsaro sun ce sun kashe ƴan tawayen Maoist 29 a jihar tsakiyar Indiya ta Chhattisgarh kwanaki kaɗan gabanin fara zaɓe a ƙasar.

    Lamarin ya faru ne a yankin Kanker da ke kusa da Baster inda ya kasance cibiya ta ƴan tawayen.

    Ƴan sandan jihar sun ce wannan ne hasara mafi girma da ƴan tawayen suka fuskanta a arangamarsu da jami'an tsaro a shekarun baya bayan nan.

    Chhattisgarh na fuskantar rashin tsaro na tsawon lokaci daga ƴan tawayen Maoist waɗanda ke ikirarin suna yaƙi domin kwato ƴancin talakawa.

    Yayin da mutanen Bastar ke shirin kaɗa ƙuri'u a ranar Juma'a wadda ta kasance rana ta farko ta babban zaɓe daga bisani kuma mutanen Kanker za su kaɗa ta su a ranar 26 ga watan Afrilu.

    Jami'an tsaron sun ce rikicin ranar Talata ya samo asali ne bayan sun samu labarin bayyanar jagororin ƙungiyar ƴan tawayen ta Maoist a Kankar.

    Shugaban hukumar ƴan sanda na Bastar ya shaidawa ƴan jarida a ranar Laraba cewa sun yi musayar wuta da ƴan tawayen wanda daga bisani aka samu gawawwakin ƴan tawaye 29 da kuma makamai da dama.

    Jami'an tsaron kare iyakokin Indiya sun ce ana tunanin akwai manyan ƴan tawaye biyu cikin 29 da aka kashe.

    Ministan harkokin cikin gida, Amit Shah ya taya jami'an tsaron murna kan nasarar da suka samu kan ƴan tawayen.

    Mr Shah ya ziyarci Chhatisgarh a farkon makon nan don yin kamfe din zaɓe. A ranar Laraba ne ya shaida cewa gwamnatinsa "a shirye take don ƙwato ƙasar daga hannun ƴan tawayen".

    Ta'addancin ƙungiyar ya fara ne a jihar Bengal ta Kudu a ƙarshen shekarar 1960 sannan tun lokacin ya bazu zuwa sama da kashi uku na ƙananen hukumomi 600 na Indiya.

    Ƴan ta'adda sun mamaye manyan yankuna na jihohi da dama da suka haɗa da jihohin dake arewa maso gabas da wanda ke yankin tsakiyar Indiya.

    A ƴan shekarun bayan nan ne jami'an tsaro su ka tura ƴan ta'addan zuwa cibiyoyinsu dake daji sannan aka samu raguwar tashe tashen hankula.

    Amma an cigaba da samun rikici tsakanin jami'an tsaro da kuma ƴan tawayen yayin da aka rasa rayuka da dama a duk shekara.

  17. Kotu ta tabbatar da dakatar da Ganduje daga shugabancin APC

    ..

    Wata babbar kotu a jihar Kano ta tabbatar da dakatar da Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ga shugabancin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

    Mai shari'a Usman Malam Na'abba ne ya yanke hukuncin bayan ƙarar da Dakta Ibrahim Sa'ad ya shigar a madadin jagororin jam'iyyar biyu a mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Kano.

    Mambobin jam'iyyar da aka shigar da ƙarar a madadinsu su ne - mataimakin sakatare, Laminu Sani da mai bai wa APC shawara kan harkokin shari'a, Haladu Gwanjo waɗanda suke cikin ƴan jam'iyyar tara da suka dakatar da Ganduje kwanaki biyu da suka gabata.

    Kotun ta kuma nemi Ganduje da ya daina ayyana kansa a matsayin mamba a jam'iyyar ta APC.

    Mai shari'a Na'abba ya dakatar da kwamitin gudanarwar jam'iyyar APC a Kano da ya guji yin katsalandan kan matakin shugabannin jam'iyyar a mazaɓar Ganduje da kashi biyu bisa uku na galibin shugabannin jam'iyyar suka sa hannu a kai kamar yadda kundin tsarin jam'iyyar ya tanada.

    A baya-bayan nan ne wasu shugabannin APC tara a mazaɓar ta Ganduje suka ce sun ɗauki matakin dakatar da Ganduje bayan wata takardar koke da wani ɗan jam'iyyar Ja'afaru Adamu ya shigar.

    A takardar koken, Adamu ya yi magana kan tuhume-tuhumen rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan inda ya buƙaci jagororin mazaɓar su gudanar da bincike kan batun domin farfaɗo da ƙimar jam'iyyar da kuma tasirin da batun zai yi a fafutukar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yaƙi da rashawa.

  18. Dangote ya karya farashin dizel a Najeriya

    ..

    Matatar mai ta Dangote ta sanar da ƙara rage farashin dizel daga N1,200 zuwa N1,000 duk lita ɗaya.

    Ƴan makonnin da suka gabata, lokacin da matatar ta soma aiki, kamfanin yana sayar da farashin dizel a kan naira 1,200 duk lita guda.

    Hakan na nufin an yi ragin fiye da kashi 30 cikin 100 daga farashin da ake sayar da dizel ɗin a baya kimanin N1,600 kowace lita.

    Matatar ta ce muhimmin ragin da aka yi kan farashin na dizel zai yi tasiri sosai a ɓangaren tattalin arziki tare da rage hauhawar farashin da ake fuskanta a Najeriya.

    Matatar Dangote ta soma gudanar da harkokinta ne da sayar da man jirgi da kuma na dizel.